Sheikh Bala Lau Ya Hade 'Yan Izala da Darika, Ya Masu Nasiha Mai Ratsa Zuciya kan Tinubu

Sheikh Bala Lau Ya Hade 'Yan Izala da Darika, Ya Masu Nasiha Mai Ratsa Zuciya kan Tinubu

  • Shugaban Izala na Afirka, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya yiwa yan Najeriya nasiha kan abin da ya fi dacewa su yi wa shugabanninsu
  • Babban malamin ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu na bukatar addu'o'in 'yan Najeriya domin cimma nasara a gwamnatinsa
  • Ya jaddada cewa babu abin da zai tafi daidai matukar babu zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al'ummar Najeriya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Ibadan, jihar Oyo - Shugaban Kungiyar Izala na kasa, Dr. Abdullahi Bala Lau ya yo kira ga yan Najeriya su ci gaba da yiwa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu addu'a.

Sheikh Bala Lau ya ce Shugaba Tinubu na bukatar addu'a daga musulmi da wadanda ba musulmi ba domin cimma nasarar aiwatar da ayyukan da ya dauko.

Sheikh Abdullahi Bala Lau.
Hoton Shugaban Izala na Afirka, Sheikh Abdullahi Bala Lau a wurin taron FOSON a Ibadan Hoto: Jibwis Jigeria
Source: Facebook

Fitaccen malamin ya yi wannan kira ne a wurin taron gagarumin kwanaki uku da kungiyar Ahlus-Sunnah ta Najeriya (FOSON) ta shirya a Ibadan, Tribune Nigeria ta rahoto.

Kara karanta wannan

Zargin taba annabi: Sheikh Bala Lau ya magantu kan rawar hukumar DSS a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar FOSON ta shirya shirin ne domin tabbatar da hadin kai tsakanin Musulmi a fadin kasar nan.

Da yake jawabi, Sheikh Bala Lau, wanda shi ne shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah na Yammacin Afirka, ya jaddada cewa babu wani ci gaba da za a iya samu idan babu zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Nasihar da Bala Lau ya yiwa yan Najeriya

Babban malamin Sunnah kuma shugaban Izala ya roki daukacin yan Najeriya da su dage da yi wa Shugaba Tinubu addu'a domin ya yi nasara.

“Ya kamata mu tambayi kanmu: Mece ce makomar mu? Mu za mu shirya makomar mu tun daga yau. Mu shirya matasanmu, mu karfafa musu gwiwa kuma mu tallafa wa al’ummar Musulmi baki daya.
"Daga karshe kuma, mu yi addu’a ga kasar mu. Ba za a iya samun ci gaba ba tare da zaman lafiya, kwanciyar hankali da hadin kai ba.

Kara karanta wannan

Sarki ya kinkimo bukatar kirkiro jiha 1, ya fadawa Tinubu gaba da gaba a Ibadan

“Mu a matsayinmu na kungiya, muna da babban rawar da muke takawa a kasar nan. Saboda haka, dole mu yi addu’a sosai ga shugabanmu, Bola Ahmed Tinubu, domin ya samu nasara, ya zama shugaba adali.
"Akwai abubuwa da dama da yake son gwamnatinsa ta cimma, amma ba tare da addu’a ba, ba zai yiwu ba.”

- Sheikh Bala Lau.

Dalilin shirya gagarumin taron Ahlus-Sunnah

Shi ma Shugaban FASON, Sheikh Tajudeen Abdul Kareem, ya ce an shirya taron ne domin inganta zaman lafiya da hadin kai tsakanin yan kasar.

A ruwayar The Nation, Sheikh Tajudeen ya ce:

“Abin da muke kokarin yi shi ne tabbatar da zaman lafiya a cikin kasa. Mu taimaka wa shugabanninmu su zama masu adalci wajen tafiyar da harkokin kasa ta yadda za a samu hadin kai da kwanciyar hankali.
"Mu kungiya ce da ke yada zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin kasa. Najeriya kasa daya ce, babu bambanci tsakanin Yarbawa, Hausawa da Igbo, dukanmu daya ne."
Shugaba Tinubu da Bala Lau.
Hoton Shugaba Tinubu a masallaci da Sheikh Bala Lau Hoto: Jibwis Nigeria
Source: Facebook

Legit ta samu jin ta bakin wani dan Izala, Bello Hassan, wanda ya ce maganar Malam tana kan gaskiya a mahangar addini amma dai yana ganin lokaci ya yi da malamai za su ja bakinsu su yi shiru.

Kara karanta wannan

"Za ku iya rasa kimarku": Tinubu ya aika da gagarumin saƙo ga Majalisar Ɗinkin Duniya

Bello ya ce ba wai yana sukar malamai su shiga siyasa ba ne amma yadda mutane suka canza, wasu jahilci ya masu katutu, ya kamata malamai su kama bakinsu.

"Yi wa shugahanni addu'a ba maganar Bala Lau bace, Manzon Allah SAW ne ya ce mu masu addu'a. Amma ya kamata malamai su dan tsame kansu a wasu abubuwan da suka shafi siyasa, saboda jahilai sun yi yawa," in ji shi.

Tinubu ya ba Izala Naira miliyan 10

A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bai wa kungiyar Izala reshen jihar Gombe tallafin Naira miliyan 10.

Shugaban ya yabawa kungiyar Izala mai hedkwata a Jos, jihar Filato bisa goyon baya da gudummuwar da suka bai wa gwamnatinsa.

A madadin shugaban JIBWIS, Sheikh Nasiru Abdulmuhyi ya gode wa Tinubu da ministan, tare da tunatar da Musulmi su kiyaye koyarwar addini.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262