'Yan Bindiga Sun Bude Wuta a Masallaci Ranar Juma'a, Mutane da Dama Sun Mutu

'Yan Bindiga Sun Bude Wuta a Masallaci Ranar Juma'a, Mutane da Dama Sun Mutu

  • Yan bindiga sun kai hari masallaci ana tsakiyar Sallar Asuba a kauyen Yandoto da ke yankin karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara
  • Rahotanni daga mutanen kauyen sun nuna cewa yan ta'addan sun kashe akalla mutane biyar a masallacin, sun raunata wasu da dama
  • Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sandan jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar ya ce har yanzu bai samu rahoton harin ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Zamfara - Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da mugayen makamai sun kai hari kan mutanen da ke sallar Asuba a jihar Zamfara.

Rahotanni sun nuna cewa 'yan ta'addan sun kashe mutane yayin da ake tsakiyar sallar Asuba a masallacin kauyen Yandoto da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara.

Jihar Zamfara.
Taswirar jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Yan bindiga sun kashe mutane a masallaci

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun hallaka dan sanda, an yi awon gaba da jami'an tsaro

Jaridar Daily Trust ta tattaro akalla masallata biyar suka rasa rayukansu a harin da 'yan bindigar suka kai masallacin Yandoto da sanyin safiyar yau Juma'a.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan mummunan lamari ya girgiza al'ummar yankin gaba daya saboda yadda maharan suka nuna rashin imani ta hanyar kashe masu ibada.

Shaidu sun ce yan ta'addan sun kutsa cikin masallacin ana cikin Sallah, suka bude wa masu ibada wuta babu kakkautawa, inda suka kashe mutane biyar nan take.

Majiyoyi daga kauyen sun ce yan bindigar sun kuma jikkata wasu da dama daga cikin wadanda suka fita Sallar Asubah.

Yan bindiga yi garkuwa da masallata

Wani mazaunin garin, wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsaro, ya ce maharan sun kuma yi awon gaba da adadi da ba a tantance ba na masu ibada.

Da yake bayyana abin da ya faru, mutumin bayyana harin a matsayin “ta’addanci mai muni sa raahin imani da tausayi."

Mutumin ya ƙara da cewa tuni aka garzaya da wadanda suka aamu rauni zuwa asibiti, kuma samun kulawar likitoci yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe malamin musulunci da mace mai ciki a Kwara

A cewarsa, wasu daga cikin wadanda aka kwantar a asibiti sakamakon harin sun fara murmurewa.

Rundunar 'yan sanda ba ta samu labari ba

Da aka tuntubi jami'in hulda da jama'a na rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, DSP Yazid Abubakar, ya ce bai samu rahoto kan lamarin daga DPO na yankin ba tukuna.

Wannan harin ya zo ne kasa da mako guda bayan makamancinsada yan bindiga suka kai a kauyen Gidan Turbe, a cikin karamar hukumar Tsafe ne.

Gwamna Dauda Lawal na Zamfara.
Hoton gwamnan Zamfara, Dauda Lawal a gidan gwamnatinsa da ke Gusau Hoto: Dauda Lawal
Source: Facebook

A harin, yan ta'adda sun tattara mutanen da suka fito sallah da Asuba akalla, sun yi awon gaba da su zuwa cikin jeji, kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.

Yan bindiga sun sace mutane a Zamfara

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan bindigan sun kai harin kan jama'a a kauyen Bayan Dutsi da ke yankin Tofa, a karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara.

An ruwaito cewa 'yan bindigan sun kutsa kauyen ne suna harbe-harbe kan mai uwa da wabi, lamarin da ya jawo raunuka ga wasu mazauna harin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari a Zamfara, an yi awon gaba da mutane masu yawa

Majiyoyin sun bayyana cewa jami’an tsaro sun kara ninka kokarin da suke yi domin ceto mutanen da aka sace da kuma dawo da zaman lafiya a yankin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262