Bayan Kwankwaso, Ganduje Ya Ragargaji Abba, ya Fadi Kuskuren Gwamnan Kano

Bayan Kwankwaso, Ganduje Ya Ragargaji Abba, ya Fadi Kuskuren Gwamnan Kano

  • Abdullahi Ganduje ya ce binciken da gwamnan Kano ke yi ba su da tushe kuma suna nuna rashin fahimtar aiki
  • Ya bayyana cewa gwamnati na gadan matsaloli da basussuka, don haka binciken ba shi da manufar gina jihar
  • Tsohon shugaban APC na ƙasa ya ce ana kashe kuɗi ba tare da ingantattun ayyuka ba, don haka ya kamata a gyara

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano — Tsohon gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya yi tir da yadda Gwamnan Jihar, Abba Kabir Yusuf, ke gudanar da bincike da kuma tafiyar da mulki.

Ganduje ya bayyana cewa yawanci sababbin shugabanni ba su fahimtar hakikanin yadda ake gudanar da gwamnati.

Ganduje da gwamna Abba Kabir Yusuf
Ganduje da gwamna Abba Kabir Yusuf. Hoto: Salihu Tanko Yakasai|Sanusi Bature D-Tofa
Source: Twitter

BBC Hausa ta wallafa cewa Ganduje ya yi wannan jawabi ne yayin da ya ke mayar da martani ga binciken da gwamnatin Kano ke jagoranta.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta ware makarantun da za a rika karatu kyauta a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abdullahi Ganduje ya soki binciken da ake yi

Ganduje ya ce babu shakka idan gwamnati ta shuɗe a kan bincike ta, amma su sababbin shugabannin ba su fahimci yadda aikin gwamnati ya ke ba.

Tsohon gwaman ya yi nuni da cewa ya kamata a faɗi adadin kuɗin da aka samu Kano da kuma yadda aka kashe su.

Ganduje ya ce kudin da Abba Kabir ya samu a wata shida da suka wuce bai same su a shekara takwas da ya yi.

Ya ce cigaban mai haƙar rijiya Abba ke yi saboda irin facaka da suke yi da kuɗin da ake kashewa kan ayyukan da suke cewa suna yi.

Dr. Ganduje ya ce Abba zai bar bashi

Ganduje ya ce gwamnati da ya gada ta bar masa wasu kalubale ciki har da bashin kuɗin 'yan fansho da sauran al'amura da suka jima kafin zuwansa.

Ya ƙara da cewa wasu daga cikin matsalolin da ake gani a yanzu sun dade a jihar, inda shugabanni suke barin ayyuka da basussuka.

Kara karanta wannan

Trump ya ce an masa makarkashiya bayan ya samu matsaloli 3 a taron UN

A karshe Ganduje ya bayyana cewa yana da tabbas cewa shi ma Abba Kabir Yusuf zai bar bashi a lokacin da ya gama mulki.

Rabiu Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf
Rabiu Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Twitter

Ganduje ya ce Abba na kame-kame

A lokacin da aka tambaye shi ko bai ga nasarorin gwamnatin Abba Kabir Yusuf ba, Ganduje ya amsa da cewa gwamnati tana da nasarori da rashin nasarori.

Sai dai ya kara da cewa wasu abubuwan da ake kira cigaba ba su bayyana a zahiri ba saboda yadda ake kashe kuɗi.

Abdullahi Ganduje ya ce har yanzu Abba Kabir Yusuf kame kame ya ke, kuma ba shi da ko ludayi ma balle a ga kamun ludayinsa a fagen mulki.

Ganduje ya yi maraba da Kwankwaso

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje ya ce ya samu labarin Rabiu Kwankwaso zai sauya sheka.

Sai dai duk da jin labarin, Ganduje ya ce bai dauke shi da muhimmanci ba saboda wasu abubuwan da suka faru a baya.

Duk da abin da ya faru, tsohon shugaban jam'iyyar ya ce zai yi maraba da Rabiu Kwankwaso idan har ya sauya sheka zuwa APC.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng