Taba Annabi a Kano: Abba Ya Dauki Matakin Farko bayan Korafi kan Sheikh Triumph

Taba Annabi a Kano: Abba Ya Dauki Matakin Farko bayan Korafi kan Sheikh Triumph

  • Gwamnatin Kano ta ce ta karɓi ƙorafe-ƙorafe da dama daga ƙungiyoyin addini kan kalaman Sheikh Lawan Triumph
  • Mai girma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin a miƙa batun ga Majalisar Shura domin ta yi nazari
  • An shawarci jama’a su kwantar da hankula tare da ci gaba da harkokinsu ba tare da tashin hankali ba a fadin jihar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Gwamnatin Kano ce ta karɓi ƙorafe-ƙorafe da kuma ƙorafe-ƙorafen mayar da martani daga ƙungiyoyin addinin Musulunci kan kalaman da Sheikh Lawan Triumph.

Kalaman sun jawo muhawara tsakanin kungiyoyin addini daban-daban, inda wasu ke ganin kalaman na da tasiri ga zaman lafiya, wasu kuma suka ɗauki akasin haka.

Abba Kabir Yusuf da Sheikh Triumph
Abba Kabir Yusuf da Sheikh Triumph. Hoto: Sheikh Abubakar Lawal Shuaibu Triumph
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan matakin da gwamnan ya dauka ne a wani sako da Sanusi Bature D-Tofa ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Nigeria @65: Za a fara shagulgulan ranar 'yancin kai ta 2025 a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƙungiyoyin da suka miƙa ƙorafe-ƙorafe

A cikin sanarwar da mai magana da yawun sakataren gwamnatin Kano, Musa Tanko, ya fitar, ya ce an karɓi ƙorafe-ƙorafen daga kungiyoyi takwas.

Cikin su akwai kungiyar Safiyatul Islam, Tijjaniya Youth Enlightenment Forum, da kuma Interfaith Parties for Peace and Development.

Haka kuma akwai Cibiyar Sairul Qalbi, Cibiyar Habbullah Mateen, da kuma limaman masallatan Juma’a karkashin Darikar Qadiriyya.

Bugu da ƙari, Kwamitin Malaman Sunnah na Kano da Multaqa Ahbab Alsufiyya suma sun gabatar da ra’ayoyinsu a rubuce zuwa ga gwamnati.

Matakin da gwamnatin Kano ta dauka

Sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, ya tabbatar da cewa gwamnatin ta mika dukkan ƙorafe-ƙorafen ga Majalisar Shura.

Ya ce wannan mataki zai baiwa majalisar damar yin nazari dalla-dalla tare da bayar da shawarwari kan yadda za a gudanar da lamarin cikin adalci da kwanciyar hankali.

Daily Nigerian ta wallafa cewa ya kara da cewa gwamnati ba za ta yi sakaci ba wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai tsakanin mutane a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Sanata Barau ya bi sahun Gwamna Abba, ya tura dalibai 1000 karatu a jami'ar Katsina

Wani zama da 'yan sanda suka taba yi da Sheikh Lawal Truimph
Wani zama da 'yan sanda suka taba yi da Sheikh Lawal Truimph. Hoto: Abdullahi Haruna Kiyawa
Source: Facebook

Kira kan a zauna lafiya a jihar Kano

Gwamnatin jihar ta yi kira ga al’ummar Kano da su kwantar da hankulansu, tare da guje wa duk wani abin da zai iya haddasa rikici.

“Muna roƙon jama’a su ci gaba da harkokinsu na yau da kullum, su kasance masu bin doka da oda,”

- In ji sakataren gwamnatin Kano a cikin sanarwar.

Har ila yau, gwamnatin ta jaddada cewa za ta ci gaba da sa ido wajen tabbatar da mutunta juna da zaman lafiya tsakanin dukkan ɓangarori.

Yanzu idanun jama’a a Kano da wasu jihohi sun karkata ne zuwa ga Majalisar Shura domin jin matakin da za ta ɗauka bayan kammala nazarin ƙorafe-ƙorafen.

An gayyaci Sheikh Triumph a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Kano ta gayyaci Sheikh Shuaibu Lawal Triumph domin amsa tambayoyi.

An gayyaci malamin ne bayan samun korafi kan wasu kalamai da ya yi a wani wa'azi da aka ce suna shirin tayar da tarzoma.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: An kai karar Akpabio majalisar dinkin duniya kan Natasha

Bayan tattaunawar da suka yi, 'yan sanda sun yi kira ga jama'a da su kwantar da hankalinsu domin za su tabbatar an yi bincike na adalci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng