"Za Ku Iya Rasa Kimarku": Tinubu Ya Aika da Gagarumin Saƙo ga Majalisar Ɗinkin Duniya
- Shugaban Kasa, Bola Tinubu ya buƙaci a sama wa Najeriya ta kujerar a Majalisar Tsaro ta domin daidaita wakilcin kasashen a duniya
- A jawabain da ya gudanar ta bakin Mataimakinsa, Kashim Shettima, Tinubu ya nemi sauya tsarin kuɗin duniya da kafa sabuwar kotun kasa da kasa
- Shugaban Najeriya ya jaddada cewa matukar Majalisar Dinkin Duniya ba ta yi abin da ya dace wajen sauya-sauye ba, za ta iya rasa kimarta
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kasar Amurka – Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya shawarci Majalisar Ɗinkin Duniya da ta rungumi sauye-sauye cikin gaggawa don tsira da tasirinta.
Ya ce yin biris da wasu batutuwa da ke bukatar canji zai iya jawo wa ta rasa tasiri da kimar da ta ke da shi a idon duniya baki daya.

Source: Twitter
Premium Times ta wallafa cewa shawarar Shugaban na kunshe a cikin jawabin da Mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima, ya karanto yayin zaman Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tinubu ya shawarci Majalisar Dinkin Duniya
Daily Post ta wallafa cewa Tinubu ya bayyana cewa bambanci tsakanin maganganun Majalisar Dinkin Duniya da ayyukanta yana barazana ga yadda jama'a ke aminta da ita.
Ya ce ci gaba da watsi da sauye-sauye a harkokin Majalisar ya sa wasu kasashe sun fara ganin tsarin ba shi da amfani wanda ya jawo wasu ke tarukansu a wajen Majalisar.
Shugaban Ƙasa ya gabatar da muhimman buƙatu guda huɗu na sauyi, inda ya fara da bukatar Najeriya ta samu kujera ta dindindin a Majalisar Tsaron Majalisar Dinkin Duniya.
Ya ce:
“Majalisar Ɗinkin Duniya za ta dawo da tasirinta ne kawai idan ta fara wakiltar duniya kamar yadda take a yau, ba yadda take a da ba.”

Kara karanta wannan
Shettima ya kalli shugabannin duniya, ya fadi matsayar Najeriya kan kafa kasar Falasdinawa
Tinubu ya bayyana cewa Najeriya ta sauya daga kasancewa mallakar Turawan mulkin mallaka da mutane miliyan 20, ta koma ƙasa mai ikon kanta.

Source: Facebook
Kuma a yanzu, tana da yawan jama’a sama da miliyan 236, wacce ake hasashen za ta zama ta uku mafi yawan jama’a a duniya, saboda haka tana bukatar wakilci a Majalisar.
Tinubu ya bayyana damuwarsa ga Majalisa
Shugaban Najeriya ya kuma nuna damuwarsa kan yadda batutuwan muhimmanci kamar kawar da makaman nukiliya da gyaran tsarin kasuwanci ke tafiyar hawainiya.
Ya bayyana cewa:
“Wannan jinkirin, matsala ne ga ɗan Adam baki ɗaya.”
Shugaban Ƙasa ya nemi a kafa sabuwar kotu irin ta kasa da kasa don kula da bashi tsakanin ƙasashe masu tasowa da masu ci gaba.
Ya jaddada cewa Afrika, musamman Najeriya, na da dimbin albarkatu da za su ciyar da fasahar zamani gaba, amma ana ukatar jari domin sarrafa su.
Ya ce:
"Idan dai har za mu ci gaba da fitar da albarkatun ƙasa ba tare da sarrafa su a gida ba, za mu ci gaba da fama da rikice-rikice da rashin daidaito."
Tinubu ya aika sako ga Majalisar Dinkin Duniya
A baya, mun wallafa cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cikakken goyon bayan Najeriya ga ƙasashen da ke marawa kafa ƙasar Falasɗinu mai cin gashin kanta baya.
Shugaban da ya bi sahun kasashe irinsu Faransa mai jaddada cewa wannan mataki ne mai muhimmanci don tabbatar da adalci da zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya.
Tinubu ya bayyana wannan matsayi ne a jawabin da Mataimakinsa, Sanata Kashim Shettima, ya karanta a madadinsa yayin taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 80 a Amurka.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

