Sanata Uba na Neman Jefa Kansa a Gagarumar Matsala kan Badakalar Naira Miliyan 400

Sanata Uba na Neman Jefa Kansa a Gagarumar Matsala kan Badakalar Naira Miliyan 400

  • Rundunar Yan Sanda ta bukaci Babbar Kotun Tarayya mai zama a Abuja ta ba da umarnin kamo Sanata Andy Uba
  • Kotu ta bukaci tsohon sanatan ya gurfana a gabanta ranar 28 ga watan Oktoba, 2025 ko kuma ta bayar da umarnin kama shi
  • Alkalin kotun ya dauki wannan mataki ne a shari'ar da ake tuhumar Andy Uba da wani mutumi da zambar Naira miliyan 400

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, a ranar Laraba ta umurci tsohon sanata, Andy Uba da ya bayyana a gabanta ranar 28 ga Oktoba, 2025.

Kotun Tarayya ta gargadi Sanata Andy Uba ya gurfana a gabanta kan shari’ar zamba ta Naira miliyan 400, ko kuma ta bayar da umarnin kamo shi.

Sanata Emmanuel Andy Ubah.
Hoton tsohon sanata daga Anambra, Andy Ubah Hoto: Senator Emmanuel Andy Ubah
Source: Facebook

Mai shari’a Mohammed Umar ne ya yi wannan gargaɗi bayan lauyan rundunar yan sanda, Aminu Abdullahi, ya shigar da buƙatar hakan, cewar Premium Times.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kama malamim addinin musulunci a jihar Bauchi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tun lokacin da aka fara shari’ar a 2024, Andy Uba bai taba halarta ba, sai dai wanda ake tuhumarsu tare, Benjamin Etu, ne yake zuwa zaman kotu a kowane lokaci.

Dalilin maka Sanata Uba a gaban kotu

Tun farko rundunar yan sandan Najeriya ta shigar da ƙarar a watan Oktoba 2024, bayan wani ɗan kasuwa, George Uboh ya kai ƙorafi cewa Uba da abokinsa sun yaudare shi, sun karbar masa kudi.

Dan kasuwar ya ce Sanata Uba da abokinsa sun karbi Naira Miliyan 400 da sunan taimaka masa wajen samun mukamin Manajan Darakta na Hukumar Raya Yankin Neja Delta (NDDC).

A shekarar 2007, Andy Uba ya yi gwamna Anambra na tsawon kwanaki 16 kacal, kafin kotun koli ta soke nasararsa.

Daga baya a 2011 ya lashe kujerar Sanata mai wakiltar Anambra ta Kudu a Majalisar Dattawa, inda ya yi wa’adi biyu a ofis.

An nemi kotu ta bada umarnin kamo Uba

Kara karanta wannan

Sarki Sanusi II ya hadu da ministocin Tinubu a majalisar dinkin duniya

A zaman ranar Laraba, mai gabatar da ƙara, Abdullahi, ya nemi kotu ta bayar da umarnin kama shi bisa sashe na 394 na dokar ACJA, 2015, saboda kin bayyana a gaban kotu akai-akai.

Sai dai lauyan Sanata Uba, C.F. Odiniru, ya yi fatali da wannan buƙata, yana mai cewa wanda yake karewa yana kwance yana jinya ne a asibiti da ke Amurka, don haka ba zai iya zuwa ba.

Abdullahi ya amsa da cewa da wannan hujjar ya yi amfani a zaman da ya gabata a watan Yuli, yana mai cewa rashin halartar Uba tun daga 2024 har zuwa yanzu raina kotu ne kuma ƙoƙari ne na jinkirta shari’a.

Gudumar kotu da ankwar yan sanda.
Hoton gudumar kotu da ankwar da ake daure hannun masu laifi Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Kotu ta aika sako ga Sanata Andy Uba

Mai shari’a Umar ya nuna rashin gamsuwa da bayanan bangaren wanda ake tuhuma, inda ya tambaya da alamar takaici:

"To me kuke nufi, za mu ci gaba da zama haka har tsawon shekaru goma?”

Daga nan sai ya yi gargaɗi cewa dole Uba ya bayyana a ranar 28 ga Oktoba, in ba haka ba za a bayar da umarnin kama shi, in ji rahoton jaridar Guardian.

Kara karanta wannan

Zargin N3bn: Alkali ya fara fusata, an shekara 10 ana shari'ar tsohon gwamna da EFCC

Kotu ta nuna damuwa kan shari'ar Suswam

A wani labarin, kun ji cewa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta nuna takaici kan yadda shari’ar zargin almundahanar tsohon gwamna ta ki ci ta ki cinyewa.

Mai Shari’a Peter Lifu ya ce ko ma mene ne ya faru, bai kamata a ce an shafe shekaru 10 ana jan kafa a shari'ar da EFCC ta shigar kan tsohon gwamnan Binuwai ba.

Hukumar EFCC ta dauki tsawon shekaru tana shari'a da tsohon gwamnan Binuwai, Gabriel Suswam kan zargin almundahanar Naira biliyan 3.1.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262