Hankalin Tinubu Ya Koma kan Kundin Tsarin Mulki, Yana So a Yi Masa Kwaskwarima

Hankalin Tinubu Ya Koma kan Kundin Tsarin Mulki, Yana So a Yi Masa Kwaskwarima

  • Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana goyon bayansa a kan canja tsarin mulkin kasa domin inganta gudanar da Najeriya
  • Shugaba Tinubu ya bayyana sauya tsarin mulki a matsayin wata dama ta musamman don tabbatar da shugabanci nagari da haɗin kan kasa
  • Da ya ke mayar da bayani, Shugaban Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen ya bukaci ƙirƙirar karin kujeru na musamman ga mata a majalisu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa na da cikakken goyon baya ga sauye-sauyen kundin tsarin mulki.

Ya bayyana cewa yin hakan zai taimaka sosai a wajen taimaka wa kasar domin tabbatar da kyakkyawan shugabanci da cigaban Najeriya.

Shugaban Kasa na son a yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima
Hoton Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu a wani taro a kasar waje Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Shugaban ya bayyana wannan ne ta bakin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume.

Kara karanta wannan

'Dan majalisa Gabdi ya ce gwamnoni ne matsalar kasar nan, ya ba talakawa shawara

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake kaddamar da bude taron jin ra’ayoyin jama’a kan sake duba kundin tsarin mulki na 1999 da aka gudanar a birnin Abuja.

Tinubu ya goyi bayan gyara kundin tsarin mulki

Daily Post ta wallafa cewa Tinubu ya bayyana wannan mataki a matsayin wata gwaggwabar dama da za a amfani da ita wajen kafa tubalin cigaba mai ɗorewa.

Shugaban Majalisar Wakilai, Hon. Abbas Tajudeen, ya jaddada cewa majalisar ta kuduri aniyar ganin an gudanar da sauye-sauye da suka shafi kowa.

Ya yabawa kwamitin da Benjamin Kalu ke jagoranta kan sauya kundin tsarin mulki, inda ya bayyana cewa aikin da suka yi yana nuni da cewa Najeriya tana kan turbar gina kasa mai adalci.

Tinubu ya ce gyara kundin tsarin mulkin zai taimaki Najeriya
Hoton Shugaban Kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onunuga
Source: Facebook

Ya ce:

"Gyaran kundin tsarin mulki ba zai tabbata ba sai an saurari jama’a. Dole ne a yi wannan sauyi domin sauƙaƙa rayuwar al’umma."

Majalisa na son a gyara kundin tsarin mulki

Kara karanta wannan

Yadda Tinubu da Atiku ke kokuwar kwace magoya bayan Buhari na Arewa

Shugaban Majalisa ya kara da cewa Najeriya ba za ta iya samun ci gaba ba matuƙar ana barin mata da sauran rukunin jama’a a baya.

Ya ce mata ba su da haura 5% na kujerun majalisa a yau, kuma hakan ba zai kai kasar nan gaba ba ganin yadda su ke taka muhimiyar rawa a wajen ci gaban kasa.

A jawabinsa, Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Hon. Benjamin Kalu, ya bayyana cewa dole ne a yarda da tsarin 'yan sanda na jihohidon kusantar da tsaro ga jama'a.

Kalu ya kara da cewa an samar da wadannan shawarwari ne bisa bukatun al'umma, ba wai umarnin 'yan majalisa ba.

Tinubu ya kira tsohon shugaban rikon Ribas

A wani labarin, kun ji cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gayyaci tsohon shugaban riko na Jihar Ribas, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas mai ritaya, zuwa fadar Aso Rock da ke Abuja.

Rahotanni sun bayyana cewa Ibas ya isa fadar shugaban ƙasa da ƙarfe 5.50 na yammacin ranar Laraba cikin kayan gargajiya masu launin ruwan kasa, inda ya gana da Shugaba Tinubu.

Kara karanta wannan

Majalisar Wakilai ta bude wa Bola Tinubu kofar rumtumo wa Najeriya bashin kudi

Tsohon shugaban rikon kwaryan na jihar Ribas ya shiga ganawar ne tare da Ministan Kuɗi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki na Kasa, Wale Edun, da Shugaban Hukumar EFCC, Ola Olukayede.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng