An Kama Dilolin Makamai a Nijar, an Fara Binciken 'Yan Siyasar Najeriya

An Kama Dilolin Makamai a Nijar, an Fara Binciken 'Yan Siyasar Najeriya

  • Hukumomin leken asiri na Burkina Faso, Mali da Nijar sun fara bincike kan manyan shugabannin ‘yan bindiga daga Najeriya
  • Binciken ya nuna ana amfani da kuɗin yarjejeniyar zaman lafiya a Najeriya wajen sayen manyan makamai a iyakokin Nijar
  • An cafke wasu dillalan makamai da ke aiki da shugabannin ‘yan bindigan yayin da ake ci gaba da tattara bayanai kan wasu 'yan siyasa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Hukumomin leken asiri na Burkina Faso, Mali da Nijar, sun kaddamar da bincike mai zurfi kan manyan shugabannin ‘yan bindiga daga Arewa maso Yammacin Najeriya.

Binciken na nufin gano yadda suke samun makamai da alburusai daga iyakokin ƙasashen Sahel a Afrika ta Yamma.

Shugabannin Niger, Mali da Burkina Faso. Hoto: @AfricanHub
Shugabannin Niger, Mali da Burkina Faso. Hoto: @AfricanHub
Source: Twitter

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa cewa an kuma tsawaita binciken zuwa wasu ‘yan siyasar Najeriya da ake zargin suna da alaka shugabannin ‘yan bindigan.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gwabza kazamin fada da 'yan bindiga, an samu asarar rayuka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiyoyi masu tushe sun bayyana cewa wannan mataki na daga cikin tsare-tsaren kasashen AES na yaki da hanyar samar da kudi wa 'yan ta’adda da kuma safarar makamai.

Dalilin kaddamar da binciken tsaron

Binciken ya samo asali ne daga bayanan sirri da suka nuna alaƙar dillalan makamai da ‘yan ta’adda da kuma wasu kungiyoyi masu zaman kansu a yankin Sahel.

Ana zargin ‘yan bindigan da suka jima suna addabar Najeriya da farmaki ga jami’an tsaro, garkuwa da mutane suna samun makamai ta hannun wakilai a kan iyakar Najeriya da Nijar.

Hukumomi sun bayyana cewa ana biyan waɗannan dillalan makamai ne da kuɗin ƙasashen waje.

Tuni dai an cafke wasu daga cikin dillalan makaman kwanan nan, kuma yanzu haka suna tsare don amsa tambayoyi.

A ina ‘yan bindiga ke samun kudi?

Rahotannin leken asiri sun nuna cewa shugabannin ‘yan bindigan suna samu kuɗi masu yawa ta hanyar yarjejeniyar zaman lafiya.

Kara karanta wannan

Tsohon dan bindiga mai shekara 70 da ya ajiye makamai ya yi jawabi a Katsina

Hakan na cikin abin da hukumomin AES za su yi bincike a kai domin tabbatar da ko jami’an gwamnati suna shiga hulɗa kai tsaye da ‘yan ta’addan a matsayin sulhu.

Majiyar tsaro ta tabbatar da cewa an cafke wasu dillalan makamai da suka fito daga Nijar zuwa Najeriya tare da alaƙa da waɗannan manyan shugabannin ‘yan bindigan.

Rahotanni sun bayyana cewa girman cinikayyar makaman da ake yi da 'yan ta'addan ta tayar da hankali matuka.

Dan bindiga yayin zaman sulhu a Najeriya
Dan bindiga yayin zaman sulhu a Najeriya. Hoto: Zagazola Makama
Source: Facebook

Rashin tsaro: Za a binciki 'yan siyasa

Binciken da ake yi ya biyo bayan samun wasu bayanan sirri na sadarwa daga hannun ‘yan ta’addan da ake zargi da garkuwa da mutane da dama a Arewacin Najeriya.

An gano cewa wasu kungiyoyi masu zaman kansu na da alaƙa da safarar makamai kuma ana amfani da kuɗin da suka samu ta hanyar yarjejeniyar siyasa wajen kera musu makamai.

Duk da cewa ba a bayyana sunayen 'yan siyasar da ake zargi ba, hukumomin AES na ci gaba da tattara hujjoji.

An kashe malamin Musulunci a Kwara

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan bindiga masu garkuwa da mutane sun kai hari wasu kauyuka na jihar Kwara.

Kara karanta wannan

Katsina: Kananan hukumomi 2 sun zauna da ƴan ta'adda ɗauke da mugayen makamai

A yayin da suka kai harin, 'yan ta'addan sun kashe wani malamin addinin Musulunci da ya ke zuwa wa'azi yankin.

Bayan kashe malamin, an harbi wata mata mai ciki kuma likitoci sun tabbatar da mutuwar ta baya mika ta asibi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng