'Abinci Ya Yi Araha,' BUA Ya Fadi Lokacin da Darajar Naira Za Ta Kai N1400/$1

'Abinci Ya Yi Araha,' BUA Ya Fadi Lokacin da Darajar Naira Za Ta Kai N1400/$1

  • Shugaban BUA, Abdul Samad Rabiu, ya yi hasashen cewa darajar Naira za ta kai tsakanin ₦1,300/$1 da ₦1,400/$1 kafin ƙarshen 2025
  • Ya danganta wannan da "gyare-gyaren tattalin arziki masu ƙarfi" na Shugaba Bola Tinubu waɗanda aka fara ganin sakamakonsu
  • Abdul Samad Rabiu ya roki 'yan Najeriya da su kara hakuri, yana mai cewa farashin kayayyakin abinci zai ragu fiye da na yanzu

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaban kamfanin BUA, Abdul Samad Rabiu, ya yi hasashen cewa Naira za ta ragargaza Dala zuwa tsakanin N1,300/$1 - N1,400/$1 kafin ƙarshen 2025.

Abdul Samad Rabiu ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan ganawarsa da Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa da ke Abuja a ranar Laraba.

Alhaji Abdul Samad Rabiu, BUA, ya ce darajar Naira za ta kara karfi zuwa karshen 2025.
Shugaban BUA, Abdul Samad Rabiu, yana jawabi a wani taro, da hoton kudin Naira ana kirgawa. Hoto: Bloomberg/contributor
Source: Getty Images

'Darajar Naira za ta kara karfi' - BUA

Kara karanta wannan

Atiku ko Peter Obi: Kungiya ta fadi wanda ya kamata ya hakura da takara a 2027

Shugaban BUA ya ce sauye-sauyen manufofin tattalin arziƙin Tinubu sun riga sun fara ba da sakamako mai kyau ga 'yan kasuwa da kuma darajar Naira, inji rahoton Punch.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alhaji Abdul Samad ya ce:

“Ina sa ran darajar musayar kuɗi za ta ƙara ƙarfi. Ina tsammanin Naira za ta koma N1,300 zuwa N1,400 kafin ƙarshen shekara. Kuma wannan wani abu ne da ya kamata mu yi murna da shi."

Da yake bayani game da tasirin gyare-gyaren tattalin arziki na kwanan nan, shugaban na BUA ya lura cewa kamfanoni sun daina dogara kacokan ga Babban Bankin Najeriya (CBN).

Ya ce:

"Yanzu kamfanonin sun daina shiga CBN karbar kuɗin waje (FX), domin yawancinsu suna amfani da katin kudi na yanar gizo da kuma tsarin banki na ƙasa da ƙasa.
“Don haka, dole ne mu yaba wa shugaban kasa da gwamnati, sauye-sauyensu suna samar da babban tubali na tsayuwar tattalin arziki, da kuma kyakkyawar makoma ga kamfanoni da 'yan Najeriya baki ɗaya.

Farashin kayayyaki zai kara sauka

Game da hauhawar farashin kayayyaki da tsadar abinci, Abdul Samad Rabiu ya ce farashin kayayyaki ya faɗi a yanzu idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata.

Kara karanta wannan

Da gaske Tinubu zai zauna a mulki har ya mutu? Fadar shugaban kasa ta magantu

Ya ƙarfafa jama’a da su kara haƙuri yayin da gwamnatin Tinubu ke ci gaba da aiwatar da gyare-gyare da za su kara saukar da farashin abinci, inji rahoton Vanguard.

"Idan ka duba farashin kayan abinci a bara da abin da muke da shi a yau, za ka ga cewa an samu ragi mai yawa a farashin dukkan kayayyaki.
"Don haka, ina ganin muna buƙatar mu ɗan ƙara haƙuri. A fili, abubuwa suna inganta, kuma dole ne mu ci gaba da goyon bayan gwamnati"

- Abdul Samad Rabiu, BUA.

Abdul Samad BUA ya jinjinawa manufofin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da suka jawo saukin abinci da karfin Naira.
Shugaban BUA, Abdul Samad tare da Shugaba Bola Tinubu a fadar shugaban kasa. Hoto: @BUAgroup
Source: Twitter

BUA ya jinjinawa manufofin Tinubu, CBN

Jim kaɗan bayan rantsar da shi a shekarar 2023, Shugaba Tinubu ya haɗa tare da buɗe kasuwar musayar kuɗin waje don sakar wa Naira mara, inda ya haɗa manyan hanyoyin musayar kuɗi zuwa tsari ɗaya.

Tun da farko a watan Yulin wannan shekara, Abdul Samad Rabiu ya ce sababbin manufofin CBN sun kawar da buƙatar kamfanoni su riƙa yin dogon layi don neman kuɗin waje (FX).

Ya soki tsarin canjin kudi na baya, inda darajar musayar na hukuma ya yi ƙasa da na kasuwar bayan fage, yana mai cewa hakan ya haifar da gurɓacewa da kuma iyakance damar samun kuɗin ga kamfanoni da yawa.

Kara karanta wannan

2027: Gangar siyasa ta fara kaɗawa, Sanata ya ƙaddamar da kungiyar zaɓen Tinubu

"Na yi magana makonnin da suka gabata cewa sau biyu kawai na hadu da gwamnan CBN na yanzu tun bayan naɗin sa, saboda babu buƙatar hakan.
"Amma kafin yanzu, nakan ziyarci CBN duk bayan sati biyu don neman kudin waje. Hakan kawai zan yi domin in tsira a wancan lokaci."

- Abdul Samad Rabiu, BUA.

'Farashin siminti zai karye a Najeriya' - BUA

A wani labarin, mun ruwaito cewa, shugaban kamfanin BUA, Alhaji Abdul Samad Rabiu ya ce farashin buhun siminti zai karye a Najeriya a 2025.

A yayin taron wani a Abuja, hamshakin dan kasuwar ya ce za a samu karyewar farashin siminti matuƙar Naira ta ci gaba da ƙara daraja a kasuwar musaya.

Alhaji Abdul Samad Rabiu ya ce farashin kayan samar da siminti ne ya jawo tsadarsa, yana mai cewa kayayyaki za su sauka nan ba da jimawa ba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com