Gwamnatin Tinubu Ta Ware Makarantun da za a rika Karatu Kyauta a Najeriya
- Gwamnati ta sanar da cewa ɗaliban kwalejojin fasaha (FTC) za su ci gaba da karatu kyauta ba tare da biyan kudin makaranta ba
- Rahotanni sun bayyana cewa shirin ya haɗa da ɗaukar nauyin kayan makaranta, littattafai da wasu muhimman abubuwa
- Ministan Ilimi, Dr Tunji Alausa, ya gargadi shugabannin makarantu da kada su karɓi kudin da ba a ba su izini ba daga wajen iyaye
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Gwamnatin Tarayya ta sanar da sabon tsari na ilimi kyauta a dukkan kwalejojin fasaha na FTC da ke fadin kasar nan.
Wannan ya haɗa da ɗaukar nauyin kuɗin makaranta da wasu abubuwa na musamman domin sauƙaƙa wa iyaye da kuma bai wa yara damar samun ilimi ba tare da tangarda ba.

Source: Twitter
Ma'aikatar yada labarai ta wallafa cewa sanarwa kan shirin ta fito ne daga ma’aikatar ilimi ta tarayya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gargaɗi ga shugabannin makarantu
Dr Alausa ya bayyana a cikin sanarwar cewa babu wani shugaban makaranta ko jami’i da aka amince masa ya karɓi kudin da ba su cikin tsarin gwamnati daga iyaye ko masu kula da ɗalibai.
Ya ce duk wani ƙorafi da ya shafi hakan, a aika shi kai tsaye ga ma’aikatar ta hanyar lambar waya: 08036576733, 08036373796 ko imel: tse@education.gov.ng.
Alausa ya ƙara da cewa an aika da takardun gargadi zuwa dukkan kwalejojin fasaha da iyaye don tabbatar da cewa tsarin yana aiki yadda ya kamata.
Yadda za a yi karatu kyauta a FTC
Baya ga kuɗin makaranta da kudin hayan daki, gwamnati ta ce za ta ɗauki nauyin abubuwan da suka haɗa da kuɗin ƙungiyoyin makaranta, lafiya da kayan sana’a.
Baya ga samar da tsaro, za a dauki nauyin kudin wutar lantarki da ruwa, darussa na musamman, inshora da kuma kuɗin shiga yanar gizo.
Sai dai an bayyana cewa ɗalibai masu zama a makarantu su ne za su rike nauyin kayayyakin karan kansu irin su kayan sawa ranar Juma'a da Lahadi don zuwa ibada.

Source: Facebook
Haka zalika daliban ne za su tadani takalman shiga bandaki, bargo, zanin gado, tawul da sauran kayan da suka shafe su kai tsaye.
Jaridar the Guardian ta wallafa cewa ministan ya sanar da cewa za a bukaci dukkan ɗaliban makarantun su kawo takardar A4.
Manufar shirin ilimi kyauta a Najeriya
Ma’aikatar ilimi ta bayyana cewa wannan shiri yana da nufin tabbatar da cewa babu ɗan Najeriya da zai rasa ilimin fasaha saboda rashin iya biyan kudi.
Ministan ya ce wannan wani muhimmin mataki ne na gina ƙasa da za ta dogaro da kanta ta hanyar samar da ƙwararru a fannoni daban-daban.
Ya ce:
“Matakin ya nuna yadda gwamnatin Tinubu ke daraja ilimin fasaha da sana’o’i a matsayin hanyar bunkasa matasa, samar musu da kwarewar da za su iya amfani da ita wajen ci gaban ƙasa.
Za a dauki nauyin karatun 'yan Kano
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Kano karkashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta dauki nayin karatun wasu dalibai.
Rahotanni sun bayyana cewa kimanin dalibai 240 'yan asalin jihar ne za su shiga shirin tallafin karatun.
Sai dai sanarwar da Legit Hausa ta samu ta nuna cewa daliban za su yi karatu a jami'o'in Najeriya ne ba kasar waje ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


