"An Biya Su:" Gwamnan Kano, Abba Ya Rage Bashin Fanshon Zamanin Ganduje
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya fara cika alkawuran da ya dauka ga 'yan fansho a Kano na tabbatar da an biya su dukkanin hakkokinsu
- A ranar Laraba, Gwamna Abba ya biya wasu daga cikin 'yan fansho hakkinsu da ya gada daga gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje
- Daga cikin N48bn da 'yan fansho ke bin gwamnati, Abba ya sauke Naira biliyan 27 ga tsofaffin ma'aika da iyalan wadanda su ka rasu
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bayyana cewa gwamnatinsa na da niyyar biyan dukkanin kudin fansho da hakkokin ma'aikatan da su ka rasu a jihar.
Ya bayyana cewa zai biya hakkinsu da ya gada daga gwamnatin baya da yawansa ya Naira biliyan 48 kafin karshen mulkinsa a shekarar 2027.

Source: Facebook
A sakon da ya wallafa a shafinsa na X, Gwamnan ya bayyana haka ne a fadar gwamnatin Kano ranar Laraba yayin da yake kaddamar da biyan wasu daga cikin 'yan fanshon.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Abba ya biya 'yan fansho a Kano
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana cewa wannan karon, an biya hakkin 'yan fansho da hakkin mamata da yawan kudin ya kai N5bn.
A cewar gwamnan, wannan adadi ya kai jimillar kudin da gwamnatin ta fitar zuwa Naira biliyan 27 cikin bashin Naira biliyan 48 da suka gada.

Source: Facebook
Gwamnan ya ce:
"Wannan mataki alama ce ta jajircewarmu wajen dawo da martaba da adalci ga tsofaffin ma’aikatanmu da suka sadaukar da rayuwarsu wajen hidimtawa jihar nan."
Ya kara da cewa biyan wadannan kudi ya taimaka gaya wajen karfafa kwarin gwiwar ma’aikata da kuma kara amincewar jama’a da kokarin gwamnati wajen kula da walwalarsu.
Sarakuna, 'yan fansho sun yabi gwamnatin Kano

Kara karanta wannan
Abba Gida-Gida zai rage bashin Ganduje, za a biya karin N5bn ga 'yan fansho a Kano
A wajen taron, an raba takardun karbar kudin fansho da kuma mika wasu ga iyalan mamata da wadanda ba su da lafiya.
Sannan wasu daga cikin tsofaffin ma'aikatan sun samu 'alat' da ke tabbatar da cewa kudinsu sun nuna a asusun bankinsu.
Sarkin Rano, Dr. Muhammad Isa Umaru, wanda ya wakilci shugaban majalisar sarakunan Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yaba da kokarin Gwamna Yusuf.
Ya ce an rika bukatar tsofaffin ma'aikata su biya cin hanci kafin su samu hakkokinsu a baya, amma yanzu gwamnati na yin komai cikin gaskiya da adalci.
Gwamna Abba ya waiwayi ƴan fansho
A baya, mun wallafa cewa gwamnatin Jihar Kano karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta sanar da cewa za ta fara biyan bashin fansho karo na uku.
A cikin wata sanarwa da Darakta Janar na Yada Labarai na gwamnati, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya ce wannan na daga cikin ƙoƙarin gwamnati na taimakon ma'aikata.
A baya, gwamnati ta riga ta biya wasu ɓangare na bashin fansho, inda aka cika biyan Naira biliyan 11 daga cikin Naira biliyan 48 da ake bin jihar a gwamnatin baya.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
