Ana Bankwana da Damina, za a Sheka Ruwa da Iska a Taraba, Kaduna da Wasu Jihohi

Ana Bankwana da Damina, za a Sheka Ruwa da Iska a Taraba, Kaduna da Wasu Jihohi

  • Hukumar kula da hasashen yanayi ta NiMet ta ce ruwan sama mai yawa, hade da iska da tsawa zai sauka a sassan Najeriya a yau
  • Ana sa ran samun ruwan sama da tsawa a jihohin Arewa, kamar Kano, Kaduna, Borno, Yobe, Benuwai, Filato da dai sauransu
  • An shawarci masu ababen hawa da su yi taka-tsan-tsan yayin tuki, sannan mazauna bakin teku su dauki matakan kariya daga ambaliya

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar kula da hasashen yanayi ta Najeriya (NiMet) ta fitar da hasashen yanayi na ranar Alhamis, 25 ga Satumba, 2025.

Hasashen ya nuna cewa za a samu ruwan sama da iska daga safiya har zuwa dare a wasu jihohin Arewa da Kudancin kasar nan.

Hukumar NiMet ta yi hasashen cewa za a samu ruwan sama a jihohi da dama a ranar Alhamis.
Ruwan sama da iska mai karfi, hade da tsawa na sauka a wasu sassan Najeriya. Hoto: Sani Hamza/Staff
Source: Original

Kano, Kaduna, Borno, Hukumar NiMet ta fitar da hasashen yanayin ne a daren ranar Laraba, 24 ga Satumba, 2025, a sanarwar da ta wallafa a shafinta na X.

Kara karanta wannan

'Kowa ya shirya,' Amabliyar ruwa za ta shafi yankuna 69 a Kano, Borno da jihohi 13

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hasashen ruwan sama a jihohin Arewa

Da safiya:

Za a fara safiyar Alhamis da yanayi mai hadari da kuma fitowar rana na ɗan wani lokaci. Amma daga bisani ruwan sama da tsawa za su iya sauka a sassan jihohin Taraba, Zamfara, Kaduna, Kano, Bauchi, Gombe, da Adamawa.

Hakazalika, NiMet ta yi hasashen cewa ruwan sama, iska mai karfi, hade da tsawa za su iya sauka a sassan jihohin Neja, Kwara, Nasarawa, da kuma Babban Birnin Tarayya (Abuja).

Da rana zuwa dare:

NiMet ta yi hasashen cewa za a samu ruwan sama da tsawa mai matsakaicin ƙarfi a sassan jihohin Jigawa, Borno, Yobe, Kaduna, Kano, Bauchi, Adamawa, da Taraba.

Sannan ana sa ran samun ruwan sama da tsawa mai matsakaicin ƙarfi za su sauka a sassan jihohin Benuwai, Filato, Neja, Kwara, da Kogi.

Hasashen ruwan sama a jihohin Kudu

Da Safiya:

Hukumar NiMet ta rahoto cewa:

Kara karanta wannan

Ewugu: Tsohon mataimakin gwamnan da 'yan bindiga suka sace kafin ya rasu

"Za a iya fuskantar yanayi na hadari, tare da yiwuwar samun ruwan sama mai karfi a sassan jihar Cross River."

Da rana zuwa dare:

Amma da rana zuwa dare kuma, hukumar ta ce ana sa ran samun ruwan sama da tsawa mai matsakaicin ƙarfi a yawancin sassan yankin Kudancin Najeriya.

Hukumar NiMet ta ce ruwan sama mai yawa zai iya jawo ambaliya a wasu sassan kasar nan.
Mutane na tsallaka titi da ruwa ya shanye, bayan saukar ruwan sama a Legas. Hoto: Getty Images
Source: UGC

Shawarwarin NiMet ga jama'a

Hukumar ta NiMet ta yi gargadi tare da ba da shawarwari game da hasashen da fitar, inda ta ce:

  • Akwai yiwuwar ruwan sama, iska mai karfi, tare da tsawa za su su haifar da dakatarwar ayyukan waje na ɗan lokaci.
  • Za a iya samun hadurra a titunan kasar nan saboda ruwan sama mai karfi na dusashe ganin masu tuki, kuma tituna suna tsantsi
  • Za a iya fuskantar ambaliyar ruwa a yankunan da suka saba fuskantarsa, da wadanda ke zaune a bakin koguna.

Hukumar NiMet ta gargadi mutane da hukumomi, su dauki matakan gaggawa don kare rayuka da dukiyoyi yayin da ruwan sama mai yawa zai sauka a yau.

Za a samu ambaliya a jihohi 15

Kara karanta wannan

Ranar Laraba: Mamakon ruwan sama da iska mai karfi zai jawo ambaliya a jihohi 3

A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta ce za a samu ruwan sama mai yawa a tsakanin 24 zuwa 28 ga watan Satumba, 2025.

A cewar ma'aikatar muhalli ta tarayya, ruwan zai jawo ambaliya a yankuna 69 da ke jihohi 15, ciki har da Adamawa, Delta, Kano, da sauransu.

Rahoton hukumar NEMA ya nuna cewa mutane 232 sun mutu, sama da 121,000 sun rasa muhallansu sakamakon ambaliyar ruwa ya zuwa Satumba .

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com