'Kowa Ya Shirya,' Amabliyar Ruwa Za Ta Shafi Yankuna 69 a Kano, Borno da Jihohi 13
- Ma’aikatar muhalli ta tarayya ta ce za a samu ruwan sama mai yawan gaske a tsakanin 24 zuwa 28 ga watan Satumba, 2025
- A cewar ma'aikatar, ruwan zai jawo ambaliya a yankuna 69 da ke jihohi 15, ciki har da Adamawa, Delta, Kano, da sauransu
- An ruwaito cewa mutane 232 sun mutu, sama da 121,000 sun rasa muhallansu sakamakon ambaliyar ruwa ya zuwa Satumba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Ma'aikatar Muhalli ta Tarayya ta yi hasashen cewa ambaliyar ruwa za ta shafi yankuna 69 a jihohi 15 na Kudu da Arewacin Najeriya.
Ma'aikatar ta yi gargaɗin cewa ruwan sama mai yawa da zai sauka tsakanin 24 zuwa 28 ga Satumba, 2025, zai iya haifar da ambaliya a yankunan.

Source: Getty Images
Gwamnati ta gargadi jihohi 15 kan ambaliya
Cibiyar gargadi kan ambaliyar ruwa (FEW) da ke karkashin ma'aikatar ce ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar ranar Laraba, inji rahoton Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daraktan sashen kula da zaizayar kasa, ambaliya da kuma yankunan da ke a bakin Teku, Usman Abdullahi Bokani, ya sanyawa sanarwar hannu.
Wannan wani ɓangare ne na matakin farko na gargaɗin jama'a game da yiwuwar afkuwar ambaliya a yankunansu don hana asarar rayuka da dukiyoyi a lokacin da ake ruwan sama.
Ambaliyar ruwa ta kasance wani iftila'i da ya zama ruwan dare a Najeriya, inda take raba dubban mutane da muhallansu a kowace shekara, tana lalata ababen more rayuwa, da kuma kawo cikas ga samar da abinci.
Asarar da ambaliyar ruwa ta jawo a 2025
A cewar hukumar NEMA, mutane 232 sun rasa rayukansu, yayin da wasu 121,224 suka rasa muhallansu sakamakon ambaliyar ruwa da ta afku sassan kasar ya zuwa 20 ga Satumba, 2025, inji rahoton BusinessDay.
Bugu da kari, bayanan sun nuna cewa mutane akalla 339,658 ambaliyar ta shafa zuwa yanzu, yayin da 681 suka samu raunuka daban-daban.
Ita kuma hukumar NiMet ta yi gargadin cewa jihohi da dama na Najeriya, musamman wadanda ke da tekuna a Arewa, za su gamu da ambaliya, wanda ke nufin cewa za a iya sake fuskantar wata matsalar nan gaba.

Source: Getty Images
Jihohi da yankunan da ambaliya za ta shafa
Cibiyar FEW ta sanar da cewa:
"Mai yiyuwa ne ruwan sama mai yawa ya sauka a jihohi 15 a fadin kasar nan tsakanin 24 ga Satumba zuwa 28 ga Satumba, 2025. Wannan na iya haifar da ambaliyar ruwa a sassa daban daban na jihohin."
Ga jerin jihohi da yankunansu da ake fargabar ambaliyar za ta shafa:
- Adamawa: Farkumo, Jimeta, Mayo-Belwa, Wuro Bokki, Yola
- Anambra: Ogbakuba
- Bayelsa: Amassoma, Ikpidama, Kalama, Kolokuma/Opokuma, Odi, Odoni, Ogbia, Oloibiri, Oporoma, Otouke, Peremabiri, Sagbama, Yenagoa
- Borno: Damasak
- Delta: Abigborodo, Aboh, Abraka, Agbor, Asaba, Forcados, Koko, Okoloba, Okpo-Krika, Patani, Sapele, Ughelli, Warri, Umugboma, Umukwata, Umuchi-Utchi
- Edo: Benin City, Okada
- Imo: Egbema, Oguta
- Kano: Bebeji, Gezawa, Gwarzo, Kano, Karaye, Tudun-Wada, Wudil
- Katsina: Jibia
- Ondo: Akure, Ikare, Ita-Ogbolu
- Oyo: Iseyin, Oyo
- Rivers: Ahoada, Itu
- Sokoto: Isa, Shagari
- Taraba: Bandawa, Gembu, Ngaruwa, Serti
- Zamfara: Anka, Bungudu, Bukuyum, Gummi, Gusau, Kaura Namoda, Maradun, Shinkafi
Ma'aikatar ta yi kira ga masu ruwa da tsaki da su lura da wannan gargaɗi, su shirya yadda ya kamata, da kuma samar da matakan kariya.
Ambaliya za ta afku a jihohi 3
A wani labarin, mun ruwaito cewa, hukumar NiMet ta yi hasashen cewa ambaliyar ruwa za ta shafi jihohin Legas, Ogun da kuma Oyo.
Sanarwar hakan na kunshe ne a cikin rahoton hasashen yanayi na ranar Laraba da ta fitar, inda ta ce ruwan sama mai yawa zai sauka.
Hukumar ta yi hasashen ruwan sama da iska mai karfi zai sauka a jihohin Bauchi, Gombe, Jigawa, Kano, Katsina, Yobe da dai sauransu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng


