'Yan Bindiga Sun Hallaka Dan Sanda, an Yi Awon Gaba da Wasu Jami'an Tsaro
- An shiga jimami a jihar Kwara bayan 'yan bindiga sun yi sanadiyyar hallaka wani jami'in dan sanda
- Miyagun sun hallaka dan sandan ne bayan da suka kai hari a wani kamfanin hakar ma'adanai da ke karamar hukumar Patigi
- Kwamishinan 'yan sandan jihar Kwara ya musanta rahotannin da ke cewa har da jami'ansa aka sace a yayin harin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kwara - 'Yan bindiga dauke da makamai sun hallaka wani jami’in 'yan sanda a jihar Kwara.
'Yan bindigan sun hallaka dan sandan ne mai suna Salisu Shamaki a wani harin da suka kai a Egboro, karamar hukumar Patigi, ta jihar Kwara.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa lamarin ya faru ne a ranar Talata, 23 ga watan Satumban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan bindiga sun kashe dan sanda
Lamarin ya auku ne lokacin da maharan suka kutsa cikin wani kamfanin hakar ma’adanai na wani ɗan kasar China.
Majiyoyi bayyana cewa Salisu Shamaki, wanda aka ɗorawa alhakin tsaron ɗan kasar China a yankin, ya rasa ransa a yayin harin.
Hakazalika 'yan bindiga sun kuma yi awon gaba da wasu jami'an tsaro masu gadi a wurin hakar ma'adanan. Har zuwa daren Laraba, ba a san inda suke ba.
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa an kashe ɗan sandan ne a kauyen Gbuaji da ke yankin, inda yake gadin ɗan kasar China, duk da cewa maigidan nasa baya nan.
Ya ce an kawo gawar jami’in zuwa Patigi domin yi masa jana’iza.
Kwamishinan 'yan sanda ya yi bayani
Kwamishinan 'yan sanda na jihar Kwara, Adekimi Ojo, ya tabbatar da mutuwar jami’in, sai dai ya bayyana cewa lamarin ya faru ne a Patigi ba a Ifelodun ba.
Hakazalika kwamishinan ya bayyana cewa babu jami’in 'yan sanda da aka sace a yayin harin.

Source: Original
"Wani jami'in dan sanda ya rasa ransa a wani kamfanin 'yan kasar China da ke Egboro, karamar hukumar Patigi, kuma an sace jami'an tsaro biyu da ke gadin wurin. An kuma lalata wasu kayayyaki da ke cikin kamfanin.
"Ɗan kasar Chinan bai je wurin ba tsawon watanni uku da suka gabata."
"Abin takaici, ɗaya daga cikin jami’an 'yan sanda huɗu da ke wurin ya mutu a yayin harin. Amma akasin rahotannin da ake yadawa, jami’an da ake cewa an sace yanzu haka suna tare da ni suna bada rahoto kan abin da ya faru."
- Adekimi Ojo
'Dan majalisa ya kubuta daga hannun 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa dan majalisar dokokin jihar Plateau, Laven Denty Jacob, ya shaki iskr 'yanci bayan 'yan bindiga sun yi awon gaba da shi.
'Dan majalisar mai wakiltar Pankshin ta Kudu, ya kubuta daga hannun 'yan bindigan ne bayan ya shafe karamin lokaci yana tsare.
Shugaban kwamitin yada labarai na majalisar dokokin jihar Plateau ya bayyana cewa bai da masaniya kan ko an biya kudin fansa ko ba .a biya ba, kafin a sako Laven Denty Jacob.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

