Matakan da Ake Bi wajen Nada Shugaban Hukumar Zabe ta INEC a Najeriya
Yayin da wa'adin shugaban hukumar zaben Najeriya (INEC), Farfesa Mahmud Yakubu ya kusa karewa, an fara magana matakan da za a bi wajen maye gurbinsa.
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Wa'adin shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), Farfesa Mahmud Yakubu zai kare a watan Nuwamban 2025.
Jam'iyyun siyasa da suka hada da APC, PDP da ADC da ma sauran 'yan kasa sun fara magana kan sabon shugaban INEC da za a nada.

Source: Facebook
A wannan rahoton, mun tattaro muku hanyoyi ko matakan da ake bi wajen nada shugaban hukumar zabe a Najeriya.
1. Shugaban kasa zai sabi shugaban INEC
Shafin Law Global Hub ya wallafa cewa sashe na 153 na kundin tsarin mulkin Najeriya ya samar da matakan da ake bi wajen nada shugaban INEC.
Sashen ya ce akwai manyan kwamishinoni da majalisu na tarayya 14 da doka ta amince da su, ciki har da majalisar shari’a ta kasa, majalisar kasa da kuma INEC.
Sashe na 154 ya yi karin bayani kan cewa shugaban kasa ne zai zabi wanda ya ke so ya zamo shugaban INEC.

Source: Twitter
Ga abin da kundin tsarin mulki ya ce a sakin layi na 3:
“A yayin da shugaban kasa zai yi amfani da ikonsa na nada mutum a matsayin shugaban ko memba na Hukumar Zabe ta Kasa mai zaman kanta (INEC), ko Majalisar Shari’a ta Kasa,
"Ko kuma Hukumar Kidayar Jama’a ta Kasa, shugaban kasa zai tuntubi majalisar kolin kasa.”
Sai dai duk da haka, jaridar Punch ta wallafa cewa dole wanda shugaban kasar zai nada ya zamo ya kai shekara 50 da haihuwa ko sama da haka kuma mai nagarta.
2. Tuntubar majalisar kolin kasa
Business Day ta wallafa cewa kundin tsarin mulkin ya yi tanadi da cewa shugaban kasar zai yi shawara da majalisar kolin kasa kafin nada shugaban INEC.
Mambobin majalisar kolin kasa sun ƙunshi shugaban kasa wanda shi ne shugaban majalisar; mataimakin shugaban kasa, wanda shi ne mataimakin shugabanta.
Haka zilika akwai dukkan tsofaffin shugabannin kasa, dukkan tsofaffin alkalan kasa, shugaban majalisar dattawa da shugaban majalisar wakilai.

Source: Twitter
Baya ga haka akwai dukkan gwamnonin jihohin Najeriya da kuma babban lauyan gwamnatin tarayya.
3. Za a tantance shugaban INEC a majalisa
Bayan shugaban ƙasa ya zaɓi wanda yake so ya naɗa, bayan tuntubar majalisar ƙasa, sai a gabatar da sunan wanda aka zaba ga majalisar dattawa domin tantancewa.
Ba za a tabbatar da shi ba sai idan ya tsallake tantancewa a majalisa. Tantancewar na iya zama mai tsauri domin tabbatar da nagartar wanda shugaban kasa ya zaba.

Source: Facebook
Da zarar an tantance wanda aka tura sunan shi majalisa, shugaban kasa zai sanar da nada shi ba tare da bin wasu matakai ba kamar jin ra'ayin yan kasa.
Shugaban hukumar zai yi wa'adi daya mai shekara biyar a bisa kundin tsarin mulki, daga nan kuma shugaban kasa na da ikon sake nada shi ko ya zabi wani.
An yi gargadi kan nada shugaban INEC
A wani rahoton, kun ji cewa kusa a jam'iyyar NNPP, Buba Galadima ya yi gargadi kan shugaban INEC da za a nada a Najeriya.
Buba Galadima ya yi ikirarin cewa shugaban kasa na shirin nada wani tsohon alkali a matsayin wanda zai maye gurbin Farfesa Mahmud Yakubu.
Ya kara da cewa idan har Bola Tinubu ya nada mutumin da ake hasashe, za a iya yakin basasa a Najeriya saboda abubuwan da za su biyo baya.
Asali: Legit.ng


