Abinci Ya Kare: Gwamna Ya Kori Wasu Manyan Jami'an Gwamnati 2 daga Aiki
- Gwamnatin Bauchi karkashin jagorancin Gwamna Bala Mohammed ta gano wasu manyan jami'ai biyu da ke amfani da takardun bogi
- Hukumar Kula da Ma'aikatan Gwamnati a Bauchi ta kori jami'an daga aiki a wani bangare na tsaftace harkokin aikin gwamnati
- Bayan haka, hukumar ta kara wa wasu ma'aikata girma ciki har da daraktoci da mataimakansu, da wasu lauyoyin gwamnati
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Bauchi - Gwamnatin Jihar Bauchi karkashin Gwamna Bala Mohammed ta kori wasu manyan ma’aikata biyu saboda amfani da jabun takardu.
Wadanda abin ya shafa sun hada da Yusuf Adamu Ningi, jami’in gudanarwa, da kuma Suleiman Ahmed (Ahuta), wadanda aka tura su zuwa Fadar Gwamnatin Bauchi.

Source: Facebook
Hukumar Kula da Ma'aikatan Gwamnatin Bauchi ce ta sanar da korar wadannan manyan jami'ai a wata sanarwa da mai magana da yawunta, Saleh Umar ya fitar yau Laraba, in ji Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa an dauki wannan mataki ne a taron da hukumar ta gudanar jiya Talata a Bauchi.
Dalilin korar manyan jami'ai 2 a Bauchi
Sanarwar ta ce bincike ya tabbatar da cewa jami’an sun aikata laifin amfani da jabun takardu, wanda ya saba da dokokin aikin gwamnati na jihar (Rule 0327 ii, iii da vi).
Saleh Umar ya ce hukuncin korar ya fara aiki ne daga ranar 23 ga Satumba, 2025, cewar rahoton Daily Post.
A wani bangare na taron, hukumar kula da ma'aikatan Bauchi ta amince da kara wa wasu daraktoci uku girma zuwa mukamin manyan daraktoci.
Sannan kuma ta tabbatar da daga matsayin mataimakan daraktoci hudu zuwa matsayin daraktoci.
An kara wa wasu ma'aikata girma
Wadanda suka samu karin girma sun hada da daraktoci na gudanarwa da albarkatun dan Adam, daraktan bincike da lissafi, da kuma daraktocin tsare-tsare, shari’a da harkokin kasa da kididdiga.

Kara karanta wannan
Sanata Barau ya bi sahun Gwamna Abba, ya tura dalibai 1000 karatu a jami'ar Katsina
Haka kuma, hukumar ta amince da daukaka matsayin wasu lauyoyi guda takwas da babban jami’in kula da filaye zuwa matsayin mataimakin darakta, da sauransu.
Shugaban hukumar ma'aikatan Bauchi, Dr. Ibrahim Alhaji Muhammad, ya yi kira ga ma’aikatan gwamnati da su rika bin doka da ka’idojin aiki yadda ya kamata.
Ya jaddada cewa hakan zai kawar da ayyukan da suka sabawa doka, ya kara masu mutunci, kuma ya inganta aikin gwamnati tare da kawar da cin hanci da rashawa ba.

Source: Twitter
Gwamnatin Bauchi ta taya ma'aikata murna
Yayin da ya taya wadanda aka karawa girma murna, Dr. Ibrahim ya nanata kudirin hukumar na ba sani ba sabo kan duk wanda ya kuskura ya aikata barna.
Ya ce hukumar za ta ci gaba da kokarin tabbatar da ladabi, bin doka, da gaskiya a dukkan bangarorin aikin gwamnati na jihar Bauchi.
Bauchi: Gwamnatin ta gano ma'aikatan bogi
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Bauchi ta tabbatar da cewa ta gano ma’aikatan bogi sama da 100 a bangaren lafiya.
Shugaban hukumar kula da asibitocin jihar, Malam Sambo Alkali, ya ce an gano wadannan ma'aikata na bogi ne a binciken da aka gudanar a bincike wasu cibiyoyin lafiya guda biyar.
Malam Sambo Alkali ya kuma tabbatar da cewa duka wadanda aka gano za su fuskanci hukunci daidai da abin da suka aikata.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

