Kwana Ya Kare: Tsohon Abokin Atiku Abubakar Ya Riga Mu Gidan Gaskiya a Asibiti
- Allah ya yi wa abokin Atiku Abubakar tun na yarinta, Alhaji Muhammad Baba Suleiman Jada rasuwa a asibitin Yola bayan fama da jinya
- Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya tabbatar da rasuwar MB Suleiman Jada a wata sanarwa da ya fitar yau Laraba, 24 ga Satumba, 2025
- Atiku ya alhini tare da ta'aziyyar rasuwar abokinsa, inda ya yi addu'ar Allah Ya gafarta masa kura-kuransa, ya kuma sanya shi a gidan Aljanna
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Yola, Adamawa - Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa kuma jagoran adawar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya rasa daya daga cikin abokansa na yarinta.
Atiku, tsohon dan takarar shugabancin Najeriya ya sanar da rasuwar Alhaji Muhammad Baba Suleiman Jada (MB Suleiman Jada), wanda ya bayyana da abokinsa tun suna kananan yara.

Source: Twitter
Wazirin Adamawa ya tabbatar da rasuwar MB Suleiman Jada ne a wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X yau Laraba, 24 ga watan Satumba, 2025.

Kara karanta wannan
Atiku zai fifita Fulani idan ya samu mulki? Wazirin Adamawa ya kare kansa ga Yarbawa
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku ya yi rashin abokinsa na yarinta
Ya ce marigayin ya rasu a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Modibbo Adama (MAUTECH), da ke Yola, babban birnin jihar Adamawa bayan fama da rashin lafiya.
Atiku ya ce:
"Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Na samu labarin rasuwar Alhaji Muhammad Baba Suleiman Jada (MB Suleiman Jada).
"Marigayin ya kasance abokina tun na yarinta, ya rasu a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Modibbo Adama (MAUTECH), Yola."
Atiku Abubakar ya yi alhinin rasuwar MB Jada
Atiku Abubakar ya yi alhinin rasa abokinsa, inda ya bayyana shi a matsayin mutum mai tausayi, tawali’u, wanda kuma ba da gudummuwa ga al’umma.
Ya ƙara da cewa rasuwar MB Jada babban rashi ne, wanda zai jima bai daina radadi a zukatan iyali, abokai da duk wanda ya san shi ba.
"Za a ci gaba da tuna Alhaji MB Suleiman Jada saboda kyautatawarsa, tawali'unsa da irin gudunmawar da ya bayar ga al’ummarsa. Rashinsa babban rashi ne ga iyali, abokai da duk wanda ya san shi."
- Atiku Abubakar.
Wazirin Adamawa ya yi wa marigayin addu'a
Daga karshe, tsohon mataimakin shugaban kasar ya mika sakon ta'aziyya ga iyalin mamacin tare da addu'ar Allah Ya jikansa, ya gafarta masa kura-kuransa.
Ya kuma roki Allah ya bai wa iyalansa hakurin jure wannan rashi, wanda ya ce zai wahala su iya manta wa da marigayin cikin kankanin lokaci.
"Ina roƙon Allah Madaukakin Sarki Ya gafarta masa kura-kuransa, Ya sanya shi cikin Aljannatul Firdausi, Ya kuma bai wa iyalansa da masoyansa ƙarfi da haƙurin jure wannan rashi mai girma."
Tsohon mataimakin gwamna ya rasu
A wani labarin, kum ji cewa tsohon mataimakin gwamnan jihar Nasarawa, Sanata Solomon Ewuga, ya riga mu gidan gaskiya.
Ewuga ya yi mataimakin gwamna a ƙarƙashin tsohon gwamna Abdullahi Adamu, sannan ya wakilci Nasarawa ta Arewa a majalisar dattawan Najeriya.
Marigayin ya kuma taba rike kujerar karamin ministan babban birnin tarayya Abuja, kuma mutanen Nasarawa na ganin girmansa bisa gudummawar da ya bayar.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
