Bincike: NSIB Ta Fadi abubuwa 2 da Suka Jawo Hadarin Jirgin Kasar Kaduna zuwa Abuja
- Hukumar NSIB ta gano cewa rashin ingantaccen gyara da matsalar na'urar canja hanya ne suka haddasa hatsarin jirgin Abuja–Kaduna
- Bincike ya tabbatar da cewa fasinjoji 21 ne suka jikkata cikin mutane 618 da ke cikin jirgin a lokacin hadarin a watan Agusta, 2025
- NSIB ta bayar da shawarwari kan sauya karafan titin jirgi, saka sababbin na'urorin canja hanyar jirgi da kuma horar da ma’aikatan NRC
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Hukumar binciken hadurra ta Najeriya (NSIB) ta fitar da wasu sababbin bayanai game da jirgin kasar Abuja zuwa Kaduna da ya yi hatsari a Agusta.
NSIB ta bayyana cewa, bincikenta ya nuna mata cewa rashin ingantaccen gyara da kuma lalacewar na'urar canja hanyar jirgi ne suka haddasa hatsarin.

Source: Twitter
Dalilan hatsarin jirgin kasar Abuja-Kaduna
Binciken ya nuna cewa, ba a gudanar da cikakken gyara kan wasu karafan titin jirgi da suka taba lalacewa a tashar Asham ba, kawai an yi masu gyara sama sama ne, lamarin da ya jawo hadarin baya bayan nan, inji jaridar Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hakazalika, an gano cewa na'urar canja hanyar jirgi da ke a tashar Asham ta lalace lokacin da jirgin zai wuce, karo na biyu da hakan ta faru a tashar cikin watanni 13.
Saboda lalacewar na'urar, dole aka dawo ana sarrafa tsarin canja hanyar jirgin da hannu, ta hanyar amfani da abin da ake kira 'point clip' a turance.
Sai dai, daga bisani aka gano cewa ai shi wannan karfen da ke rike kafafuwan titin jirgi don kar su kauce hanya, ya lalace, lamarin da ya jawo hatsarin jirgin Abuja zuwa Kaduna.
Rashin kwarewar ma'aikatan NRC
Rahoton ya kuma nuna cewa ma'aikatan hukumar kula da sufurin jiragen kasa sun samu horo na matakin farko ne kawai, amma ba su da wani horo bayan wannan.
Channels TV ta rahoto cewa, d a wannan ne ake fargabar cewa akwai matsala ga tsaro da kuma yadda ma'aikatan za su iya kula da harkokin sufurin jiragen kasan.
An ce, ko a lokacin da jirgin ya yi hatsari, an gagara samun kayayyakin gyara, ciki har da wasu sassan kafafun jirgi ko karafan hanyar jirgin da ke cikin kayayyakin OEM.
Yayin da aka rahoto cewa fasinjoji 21 ne suka samu raunuka daban daban a hatsarin da ya afku a ranar 26 ga Agusta, 2026, ba a samu asarar rayuka ba.

Source: Twitter
Hadarin jirgi: NSIB ta ba da shawarwari
A matsayin mataki na farko, hukumar NSIB ta fitar da shawarwari da suka hada da sauya dukkan karafan titin jirgin da suka lalace da kuma sanya sababbin na'urorin canja hanyar jirgi a kan hanyar Abuja–Kaduna.
Haka kuma ta nemi a dawo da dukkan kayan aikin sa ido da suka lalace, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.
Hukumar ta jaddada cewa akwai bukatar a rika yi wa ma'aikatar NRC horo akai-akai domin rage faruwar irin wannan mummunan hadari a gaba.
Bayanin 'wanda ya jawo' hadarin jirgin kasa
Tun da fari, mun ruwaito cewa, shugaban hukumar NRC, Kayode Opeifa, ya dora wa kansa dukkanin laifi na hatsarin da ya faru a layin dogon Abuja zuwa Kaduna.
Kayode Opeifa ya kuma nemi afuwar yan Najeriya kan hatsarin da jirgin kasan ya yi a hanyarsa ta zuwa Kaduna, lamarin da ya jikkata fasinjoji shida.
Sai dai ya kara da cewa, duk da tun farko bai kamata lamarin ya faru ba, amma hukumar NRC za ta tabbatar irin wannna hatsarin bai sake faruwa ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


