Babbar Magana: An Yi Kutse a Shafin Gwamnatin Najeriya, 'Yan Damfara Sun Wallafa Wata Takarda

Babbar Magana: An Yi Kutse a Shafin Gwamnatin Najeriya, 'Yan Damfara Sun Wallafa Wata Takarda

  • An tabbatar da cewa yan damfara sun yi wa shafin Ma'aikatar Ilimi ta Najeriya kutse domin wallafa takardar tallafin karatun Rasha
  • Hukumar Kula da Harkokin Tallafin Karatu ta Najeriya ta ce sanarwar, wacce aka fitar tun 2022 zuwa 2023 ta bogi ce
  • Sai dai bincike ya nuna cewa tallafin karatun wanda aka yi ikirarin Gwamnatin Rasha ce ke daukar nauyi na karya ne da yaudara

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Ma’aikatar Ilimi ta Najeriya ta bayyana cewa an yi wa shafinta na yanar gizo kutse, tare da wallafa sanarwar shirin tallafin karatu a kasar Rasha mai suna, Alabuga Start Programme.

Daraktar Hukumar Tallafin Karatu ta Tarayya, Ndajiwo Asta, ta ce sanarwar da aka gani a shafin a shekarun 2022 da 2023 ba daga ma’aikatar ta fito ba.

Kara karanta wannan

Matsala ta kunno kai a Najeriya, miliyoyin yara na fuskantar hadarin mutuwa a Arewa

Ministan Ilimi na Najeriya, Dr. Tunji Alausa.
Hoton Ministan Ilimin Najeriya, Dr. Tunji Alausa Hoto: @DrTunjiAlausa
Source: Twitter

An yiwa shafin Ma'aikatar Ilimi kutse

Ta bayyana cewa wasu 'yan damfara ne suka yi wa shafin yanar gizon ma'aikatar ilimi kutse, suka wallafa takardar domin su yaudari matasan Najeriya, cewar rahoton Premium Times.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ndajiwo Asta ta ce:

“Ba mu mu ka wallafa ba, ni kai na wani ya nuna mani takardar a shafin a 2022. Amma tun daga lokacin me ya sa ba a cire shi ba? Wannan zamani ne na AI; kowa na iya kirkirar takarda ya dora a yanar gizo. Wannan shi ne abin da ya faru."
“A kowace shekara muna samun tambaya kan ingancin wannan tallafin karatu da ake gani a shafin, ina tabatar muku da cewa labari ne na bogi. Wannan ya dade yana faruwa tun lokacin da Adamu Adamu ke ministan ilimi.”

Menene sahihincin tallafin karatun Rasha?

Shirin Alabuga Start, wanda aka kaddamar a 2022, yana karkashin gwamnatin Rasha ne, kuma ana gudanar da shi ta hannun Alabuga Special Economic Zone da ke Tatarstan.

Kara karanta wannan

Turken wutar lantarki ya lalace, yankuna da dama sun fada cikin duhu a Kaduna

An yi ikirarin cewa shirin na ba mata ‘yan ƙasashe masu tasowa masu shekaru tsakanin 18-22 damar yin karatu kyauta tsawon shekaru biyu.

Sai dai rahotanni sun nuna cewa wasu daga cikin matan da aka dauka cikin shirin an tilasta masu shiga masana’antar kera makaman yaƙi da ke kimanin kilomita 1,000 daga birnin Moscow.

Binciken da aka gudanar a ƙasashe bakwai na Afirka ya nuna cewa ana daukar matan ne ta hanyar da ba ta dace ba, cike da karya da alkawuran bogi.

A cewar binciken, ana shaida wa matan cewa za su samu albashi mai kyau da horo, amma da zarar sun isa wurin sai su shiga tarkon da ba za su iya tserewa ba.

Me yasa ba a goge takardar ba tun 2022?

Duk da cewa Misis Asta ta bayyana shirin a matsayin na bogi, ba ta nuna cewa akwai bukatar ma’aikatar ilimi ta goge sanarwar bogin da aka wallafa a shafinta ba.

An gano cewa har zuwa yau Litinin da muke hada wannan rahoto, sanarwar tana kan shafin ma’aikatar ilimin Najeriya

Kara karanta wannan

'Manyan dalilan da suka sanya aka girmama ni da digirin Dakta': Rarara

Da aka tambaye ta ko hukumar za ta dauki mataki domin dakatar da amfani da shafin wajen tabbatar da sahihancin shirin, sai ta ce:

“Me kuma ake so mu yi? Mun fada muku ba mu muka saka sa ba. Amma me ya sa kuke dawo da batun? Yanzu a 2025 muke, kuna son jan mu baya zuwa shekaru 3-4 da suka gabata.
"Mu kalli gaba, mu maida hankali kan AI, ba wai komawa kan labaran da suka wuce ba.”
Tunji Alausa.
Hoton takardar sanarwar bogin da aka wallafa a shafin yanar gizon Ma'aikatar da Ministan Ilimin Najeriya Hoto: @DrTunjiAlausa
Source: Twitter

Hukumar NITDA ta bukaci a goge sanarwar

Sai dai hukumar NITDA, wadda ke kula da tsarin fasahar zamani a Najeriya, ta ce wajibi ne ma’aikatar ta goge duk wani bayani game da shirin Alabuga Start daga shafinta.

“Ya kamata su cire shi tun tuni. Abin da ya rage musu kenan. Nauyinsu ne su cire shi,” in ji mai magana da yawun NITDA, Hadeeza Umar.

An gano kwalejojin bogi 22 a Najeriya

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Najeriya ta garkame kwalejiji sama da 20 da bincike ya gano cewa na bogi ne a fadin kasar nan.

Kara karanta wannan

Rashin Imani: Wata mata ta sa cokali a wuta, ta cusa a al'aurar kanwar mijinta

Hukumar kula da kwalejojin koyar da malamai a Najeriya, wato NCCE ce ta sanar da rufe kwalejoji 22 da ke aiki ba bisa ka’ida.

Hakan ya zo ne a wani samame da hukumar ta gudanar kan makarantun bogi da ake amfani da su wajen cutar da al'umma.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262