Ana Rikicin Dangote da 'Yan Kasuwa, Gwamnati za Ta Sayar da Kadarorin NNPCL
- Kungiyoyin ma’aikatan mai sun yi watsi da shirin gwamnati na tsame hannayenta daga kamfanin mai na kasa, NNPCL
- Sun ce matakin zai lalata tattalin arziki a shiga rudani, ya raunana NNPCL kuma ya bar ma’aikata cikin rashin tabbas
- PENGASSAN da NUPENG sun bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya gaggauta dakatar da shirin kuma ya hana gyaran dokar PIA
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Kungiyoyin kwadago biyu mafi karfi a fannin fetur da gas a Najeriya PENGASSAN da NUPENG na shirin saka karfar wando daya da gwamnati.
Kungiyoyin sun fito karara wajen sukar kudirin gwamnatin tarayya na rage hannun jarinta cikin kadarorin hadin gwiwa da kamfanin NNPCL ke kula da su.

Source: Getty Images
Jaridar Punch ta wallafa cewa Shugabannin kungiyoyin biyu, Festus Osifo (PENGASSAN) da Williams Akporeha (NUPENG), sun bayyana matsayinsu ne a wani taron manema labarai a Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyoyin mai sun fusata
Vanguard ta ruwaito cewa kungiyoyin sun ce shirin sayar da 30% zuwa 35% na hannun jarin gwamnati zai iya haifar da gagarumar matsala ga tattalin arzikin kasa.
Sun ce kudirin da gwamnatin tarayya ta dauka zai kuma raunana kamfanin NNPCL, da kuma sanya ma’aikata cikin rashin kwanciyar hankali.
PENGASSAN da NUPENG sun ce;
“Ana shirin sayar da kadarori da suka fi muhimmanci domin samun kudi a cikin gaggawa, amma hakan zai jefa Najeriya cikin matsanancin rashin kudi a nan gaba."
Sun kuma yi gargadin cewa, rage hannun jarin gwamnati zai hana NNPCL biyan albashi da kula da jin dadin ma’aikata, tare da rage gudummawar da take bayarwa ga kasafin kudi.
An shawarci gwamnati kan NNPCL
Kungiyoyin sun bayyana cewa, duk da matsin lambar tattalin arziki da gwamnati ke fuskanta, sayar da kadarorin kasa ba shi ne mafita ba.
Sun nuna damuwarsu kan yadda gwamnati ke shirin gyara dokar PIA wacce aka amince da ita ba fiye da shekaru uku da suka gabata ba.

Source: Facebook
Sun ce:
“Idan gwamnati ta cigaba da wannan shiri, NNPCL za ta zama tamkar ba komai cikin ’yan shekaru."
Sun bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya dakatar da shirin nan take, tare da umartar Ministan Kudi, Shugaban Hukumar NNPCL, da Babban Daraktan kamfanin da su janye daga wannan shiri.
Sun bada shawara da cewa;
“Idan wannan shiri ya tabbata, Najeriya ba za ta iya samun kudin da za ta cike kasafin kudinta ba. Wannan hanya ce ta haddasa rikici, kuma za mu kare hakkinmu da dukkannin karfinmu."
Kungiyoyin sun jaddada cewa za su dauki dukkannin matakan da suka dace don hana sayar da hannun jari, ko da hakan na iya kaiwa ga yajin aiki.
An goyi bayan Dangote a rikicin mai
A wani labarin, mun wallafa cewa hamshakin ɗan kasuwa kuma shugaban kamfanin Geregu Power Plc, Femi Otedola, ya fito fili ya bayyana cikakken goyon bayansa ga Alhaji Aliko Dangote.
Goyon bayansa na zuwa ne a lokacin da ake rikicin da ke tsakanin Matatar Dangote da kungiyar DAPPMAN – wato kungiyar masu rumbunan ajiya da dillalan kayayyakin man fetur.
Otedola ya taya Dangote murna bisa gagarumar nasarar da ya samu na kafa matatar man fetur mafi girma a nahiyar Afrika, kuma ya ce kamata ya yi DAPPMAN ta shiga taitayinta.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


