'Yan Bindiga Sun Kashe Malamin Musulunci da Mace Mai Ciki a Kwara

'Yan Bindiga Sun Kashe Malamin Musulunci da Mace Mai Ciki a Kwara

  • 'Yan bindiga sun kai hare hare a kauyukan Motokun, Egboro da Fanagun a karamar hukumar Patigi ta jihar Kwara
  • Rahotanni sun ce an kashe mace mai juna biyu da wani malami, tare da yin garkuwa da wasu mutane a yankin
  • Mazauna yankin sun ce hare-haren sun zama ruwan dare saboda haka suna neman karin dauki daga gwamnati

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kwara – Al’umma a karamar hukumar Patigi, jihar Kwara sun shiga tashin hankali bayan da ‘yan bindiga suka kai hari a wasu kauyuka.

Rahotanni sun bayyana cewa a kalla mutane takwas ne aka sace yayin da da dama suka jikkata a sanadiyyar harin.

Taswirar jihar Kwara da aka kai hari
Taswirar jihar Kwara da aka kai hari. Hoto: Legit
Source: Original

Daily Trust ta wallafa cewa shaidun gani da ido sun bayyana cewa maharan sun shigo kauyukan Motokun da Egboro kan babura, dauke da mugayen makamai, suna harbe-harbe ba kakkautawa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai hari a Zamfara, an yi awon gaba da mutane masu yawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun kashe malami da mai ciki

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kai hari ne daga kauyen Motokun zuwa Egboro sannan suka yi gaba da Fanagun a masarautar Tsaragi, inda aka sace Fulani uku da dabbobinsu.

Daily Post ta wallafa cewa mazauna yankin sun ce hare-haren sun dauki tsawon sa’o’i ba tare da wani jami’in tsaro ya kawo dauki ba.

Wani mazaunin yankin, Hon. James Ibrahim, ya bayyana cewa wata mata mai ciki da aka harba ta mutu a asibitin Patigi, yayin da akalla mutane takwas suka fada hannun masu garkuwa.

Ya kara da cewa maharan sun tafi da baburan jama'a sama da 15, tare da jikkata wasu mutane da dama.

Wani malamin addini daga Patigi da ke yawan ziyartar kauyukan domin wa’azi ya shiga cikin wadanda aka kashe, inda maharan suka yi masa kisan gilla.

Sufeton 'yan sandan Najeriya na zaune a ofis
Sufeton 'yan sandan Najeriya na zaune a ofis. Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Shaidar mazauna kauyukan Kwara

Wani shugaban al’umma, Malam Mohammed, ya tabbatar da cewa maharan sun fara ne da Motokun kafin su wuce Egboro, inda suka raba jama’a da muhallansu.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace basarake tare da wasu mata a Plateau

Mutumin ya bayyana cewa bayan harin, mafi yawan mutanen sun gudu zuwa garin Patigi domin neman mafaka.

Ya ce wasu daga cikin wadanda aka sace sun kasance masu kudi da maharan suka san za su iya neman kudin fansa daga gare su.

Matsalar tsaro a yankin Patigi

Wani jagoran 'yan sa-kai, Gina Gana, ya bayyana cewa harin da aka kai ya biyo bayan gwabza fada da sojoji a ranar da ta gabata, inda aka sace dabbobi da dama daga kauyuka daban-daban.

Shugaban karamar hukumar Patigi, Hon. Ahmed Rufai Adam, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce yana cikin wani gagarumin taron tsaro a kan batun a lokacin da aka tuntube shi.

An sace 'dan majalisa a Filato

A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari wani yanki na jihar Filato.

Rahotanni sun nuna cewa maharan sun sace wani dan majalisa a jihar Filato, Hon. Laven Denty a cikin gidansa.

Bayanan da Legit Hausa ta samu sun nuna cewa a makon da ya wuce ma 'yan bindiga sun kai hari unguwar da Hon. Denty ke zaune.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng