Dalilai 4 da Suka Sa Kano Ta Doke Sauran Jihohi a Yawan Daliban da Suka Ci NECO 2025

Dalilai 4 da Suka Sa Kano Ta Doke Sauran Jihohi a Yawan Daliban da Suka Ci NECO 2025

Kano - A ranar Laraba da ta gabata, 17 ga watan Satumba, 2025, Hukumar Shirya Jarabawar Kammala Sakandire ta Najeriya (NECO) ta fitar da sakamakon jarabawar bana.

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Sakamakon ya nuna cewa dalibai 818,492, kimanin kashi 60.26% na wadanda suka zana NECO sun ci darussa akalla biyar ciki har da Turanci da Lissafi.

Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Hoton Gwamna Abba Kabir Yusuf a gidan gwamnatinsa da kw Kano Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Hukumar NECO ta fitar da sakamakon 2025

Daily Trust ta tattaro cewa shugaban NECO na kasa, Farfesa Dantani Ibrahim Wushishi ne ya bayyana hakan a hedkwatar hukumar da ke Minna, jihar Neja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa jimillar ɗalibai 1,367,210 ne suka yi rajista domin zana jarabawar, maza 685,514 da mata 681,696 a fadin Najeriya.

Farfesa Dantani ya kara da cewa daga cikin waɗanda suka yi rajista, ɗalibai 1,358,339 ne suka zauna jarabawar, maza 680,292 da mata 678,047.

Kara karanta wannan

Hukumar NAHCON ta rage kudin aikin Hajji na 2026 a Najeriya

Yadda Kano ta yi fice a jarabawar NECO

Sai dai wani abu da ya ja hankali game da sakamakon NECO na 2025 shi ne yadda daliban Kano suka fi na sauran jihohin Najeriya cin jarabawar ta bana.

Dalibai 68,159 yan asalin jihar Kano, kwatankwacin 5.020% na wadanda suka zauna jarabawar, sun ci darussa biyar ciki har da Turanci da Lissafi.

Wannan ya sa Kano ta shiga gaban jihohi a yawan wadanda suka ci jarabawar, jihar Legas ke biye mata a matsayi na biyu da ɗalibai 67,007 (kashi 4.930%), yayin da Oyo ta zo ta uku da ɗalibai 48,742.

Masana na alaƙanta wannan nasara da dalilai da dama, ciki har da matakan da gwamnatin jihar Kano karkashin Gwamna Abba Kabir Yusuf ke ɗauka, domin bunƙasa harkokin ilimi.

Wane dalilan da suka sa Kano ta yi zarra?

A wannan rahoton, mun tattaro maku dalilan da ake ganin su ne suka sanya daliban Kano suka samu wannan nasara a NECO 2025.

Kara karanta wannan

Murna za ta koma ciki: Sabon rahoto ya cire Kano daga ta 1 a sakamakon NECO

1. Ware wa fannin ilimi kaso mai tsoka

Tun a kasafin kudinsa na farko bayan ya karbi mulki a 2023, Gwamna Abba ya nuna cewa gwamnatinsa za ta bai wa fannin ilimi fifiko a jihar Kano.

Gwamnatin Kano ta ware Naira biliyan 95 ga harkokin ilimi daga cikin Naira biliyan 350 na kasafin kudin 2023, wato kusan kashi 27 cikin 100.

Haka kuma, a kasafin kuɗin 2024, gwamnati ta ƙara wa wannan fanni kaso mafi tsoka, inda ware wa ilimi Naira biliyan 198, watau kashi 31 cikin 100, cewar rahoton Bussiness Day.

Wannan kaso ya zarce matsakaicin kasafin da Hukumar Kula da Harkokin Ilimi ta Majalisar Dinkin Duniya watau UNESCO ta ba da shawara, tsakanin kashi 15 zuwa 20 cikin 100.

2. Ayyana dokar ta-baci kan ilimi a Kano

A ranar 8 ga Yuni, 2024, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ayyana dokar ta-baci kan ilimi, tare da sanar da ɗaukar malamai 5,000 don ƙarfafa tsarin karatu a jihar Kano.

Kara karanta wannan

Fitaccen Jarumin Fim ya sa jam'iyyu a ma'auni, ya gano wacce za ta kayar da Tinubu a 2027

Wannan na cikin matakan da Gwamna Abba ya dauka wadanda ake ganin sun kawo sauyi a fannin ilimi tun daga tushe a jihar Kano.

Abba Kabir ya ayyana dokar ta-baci a fannin ilimi a wani taro da aka gudanar da dakin taron Open Theatre da ke gidan gwamnatin Kano ranar Asabar, 8 ga Yuni, 2024.

Da yake jawabi a wurin, gwamnan ya ce ayyana dokar zai ba da damar ɗaukar matakai masu ƙarfi domin magance manyan ƙalubalen da ke damun harkar ilimi a fadin jihar.

A kalamansa da jaridar Punch ta tattaro, Gwamna Abba ya ce:

“Ayyana dokar ta-baci zai bai wa gwamnatinmu damar ɗaukar matakai masu ƙarfi wajen magance manyan ƙalubalen da suka addabi fannin ilimi a faɗin jihar Kano."

3. Samar da kayan aiki da daukar malamai

Gwamnatin Kano ta bayyana cewa nasarar da dalibai suka samu a jarabawar NECO ta bana na da alaka da yanayi mai kyau da Gwamna Abba ya samar a bangaren koyo da koyawar.

Daga cikin abubuwan da gwamnatin ta lissafo da ta ce sun taimaka wajen samun wannan nasara akwai raba kayan makaranta kyauta wanda ya rage wa iyaye nauyi.

Kara karanta wannan

Bayan nasarar dalibanta a NECO, gwamnatin kano za ta dauki malamai 2, 600 aiki

Gwamna Abba.
Hoton Gwamna Abba tare da wasu daliabai mata a jihar Kano Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Source: Facebook

Gyara daruruwan ajujuwan da suka lalace tare da samar da kujeru da tebura don inganta yanayin karatu da daukar malamai kimamin 10,000 daga hawan Abba zuwa yanzu.

Haka zalika gwamnatin Kano ta kuma rika shirya wa malaman taron kara wa juna da horas da su akai-akai don inganta harkar koyarwa.

Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya wallafa a shafin Facebook bayan an saki sakamakon NECO.

4. Tallafin karatu ga daliban Kano

Daya daga cikin abubuwan da ake ganin sun zaburar da daliban Kano har suka ci nasara a NECO shi ne tallafin karatun gaba da sakandire ga Gwamnatin Kano ke bayarwa.

Masana na ganin dalibai da dama za su yi kokarin ganin sun samu sakamako mai kyau a sakandire domin gwamnati ta dauki nauyin karatunsu a jami'a.

Wani malami a tsangayar ilimi ta Jami'ar Bayero da ke Kano (BUK), Dr. Bilyaminu Bello Inuwa ya ya shaida wa BBC Hausa cewa tallafin karatun da gwamnati ke bayarwa na karawa dalibai kwarin gwiwa.

Kara karanta wannan

NECO ta saki sakamakon jarabawa, an gano makarantu 38 a jihohi 13 sun yi magudi

A cewarsa, 'ya'yan talakawa da ba su samun damar ci gaba da karatu bayan kammala sakandire, za su dage su ci jarabawar saboda su shiga tsarin tallafin karatu.

"Tsarin daukar nauyin karatun gaba da sakandire zai karawa dalibai kwarin gwiwar cin jarabawa domin su samu damar ci gaba da karatu.
"Yaran da rashin karfin iyayensu ke hana su ci gaba da karatu, za su kara kokari su ci jarabawar fita daga sakandire saboda su samu tallafin gwamnati," in ji shi.
Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Hoton Gwamna Abba Kabir a fadar gwamnatin Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Gwamnatin Kano ta tura dalibai karatu

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnatin Kano ta sanar da cewa ta amince da daukar nauyin dalibai yan asalin Kano 240 zuwa karatun digiri na biyu.

Gwamnatin karkashin Gwamna Abba Kabir ta dauki nauyin karatun wadannan falibai a jami'o'i masu zaman kansu da su ke a jihohi daban-daban na kasar nan.

Daga cikin jami'o'in da aka tura daliban su yi karatu akwai Skyline, Al-Hikima, jami'ar Crescent da ke Abeokuta da sauran makamantansu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262