Gwamnatin Tinubu Ta Fadawa 'Yan Najeriya Dalilin Cigaba da Cin Bashi daga Waje
- Shugaban FIRS, Zacch Adedeji, ya ce karin kudin shiga ba zai hana gwamnati ci gaba da neman rance ba
- A watan Satumba 2025 gwamnatin Najeriya ta ce ta tara kudin shiga har N3.64trn, karin kaso 411 cikin 100
- Zacch Adedeji ya bayyana cewa rance wani bangare ne na tsarin kasafin kudin gwamnati, ba alamar gazawa ba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa duk da karuwar kudin shiga a watannin baya-bayan nan, ba za ta daina neman rance ba saboda manufar tattalin arzikin kasa.
Wannan sanarwar ta fito daga bakin Shugaban Hukumar Tara Haraji ta Kasa (FIRS), Zacch Adedeji.

Source: Twitter
Punch ta wallafa cewa Adedeji ya ce karuwar kudin shiga bai kawar da bukatar rance ba, domin tsarin kasafin kudi ya kunshi kudin shiga, kashe-kashe da kuma rance a kowane lokaci.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce rance na da muhimmanci wajen tabbatar da dorewar ci gaban kasa da kaucewa karin tsada a gaba.
Rance ba matsala ba ne inji FIRS
Shugaban FIRS, Zacch Adedeji ya bayyana cewa rance wani ginshiki ne a cikin kasafin kudin kowace kasa.
Ya yi karin bayani da misali cewa idan kasafin shekara ya kai N100,000, gwamnati na iya tara N90,000 daga haraji sannan ta nemi N10,000 a matsayin rance domin cike gibi.
Ya kara da cewa babu wata kasa a duniya da ke rayuwa ba tare da neman rance ba, domin rance wani bangare ne na tsarin tattalin arziki.
A cewarsa, bankuna ma na cin gajiyar rancen gwamnati ta hanyar samun riba da biyan haraji daga kudin shigar su.
Kudin shigar Najeriya ya karu sosai
Adedeji ya bayyana cewa karin kudin shiga ya samo asali ne daga bangaren da ba na man fetur ba, wanda ya tashi daga N151bn shekaru biyu da suka wuce zuwa N1.06trn a yanzu.

Kara karanta wannan
Fitaccen Jarumin Fim ya sa jam'iyyu a ma'auni, ya gano wacce za ta kayar da Tinubu a 2027
Hakazalika, kudin shiga daga man bangaren fetur ya kai N644bn yayin da harajin VAT ya haura N723bn, fiye da ninki uku idan aka kwatanta da baya.
Wannan karin, a cewarsa, na nuni da cewa gwamnati ta samu nasarori a kokarinta na rage dogaro da man fetur a matsayin ginshikin kudin shiga.

Source: Twitter
Martani ga masu sukar ciwo bashi
Shugaban FIRS ya soki masu adawa da tsarin rancen gwamnati, inda ya ce yawanci suna dogaro da bayanan da suka samu daga kafafen sada zumunta ba tare da nazari mai zurfi ba.
Sannan ya bayyana su da masu karamin sani, wadanda ba sa yin muhimman tambayoyi kan tattalin arziki.
Ya kara da cewa ba domin biyan albashi ake karbo rance ba, sai dai wajen aiwatar da manyan ayyuka da za su amfani al’umma har tsawon shekaru masu zuwa.
Dogara ya kare Tinubu kan tattalin arziki
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara ya yi magana kan rushewar tattalin Najeriya.
Dogara ya yi ikirarin cewa tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya ruguza tattali kafin mika wa Bola Tinubu murna.
Ya bayyana cewa a yanzu haka tattalin kasar ya fara farfadowa sakamakon wasu matakai da gwamnatin Tinubu ke dauka.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

