Yajin Aiki: SSANU, NASU Sun Kara wa Gwamnatin Tinubu Lokaci

Yajin Aiki: SSANU, NASU Sun Kara wa Gwamnatin Tinubu Lokaci

  • Kungiyoyin NASU da SSANU sun tsawaita lokacin tafiya yajin aiki bayan an sake zama da wakilan gwamnatin tarayya a kan matsalolinsu
  • Kungiyoyin na bukatar a biya su bashin alawus da sauran hakkoki da suka jima suna jiran biya amma shiru duk da zama da aka yi da su
  • Sun ce idan gwamnati ta kasa cika bukatunsu cikin sabon wa’adin da aka bayar, za su fara yajin aiki a dukkanin jami'o'in kasar nan

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Kungiyar ma’aikatan manyan makarantu da ba malamai ba (NASU) da ta ma’aikatan manyan makarantun, (SSANU), sun fitar da sabuwar matsaya a kan yajin aiki.

Kungiyoyin biyu sun yi kuka da yadda su ka ce gwamnatin tarayya ta yi watsi da dukkanin alkawuran da aka yi masu da sauran bukatunsu.

Kara karanta wannan

An shiga jimami bayan ramin hakar ma'adanai ya rufta da sama da mutane 100 a Zamfara

SSANU, NASU sun sassauto kan tafiya yajin aiki
Hoton wasu daga cikin ma'aikatan kasar nan ana zanga-zanga Hoto: Getty
Source: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa a cikin wata sabuwar wasika da shugabannin NASU da SSANU suka aike wa rassan kungiyoyin a fadin kasar nan, an kara wa'adin yajin aikin da mako biyu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

SSANU, NASU sun dage yajin aiki

Wsikar ta bayyana cewa an yanke wannan shawara ne bayan ganawar da suka yi da Babban Sakataren Ma’aikatar Ilimi, Abel Enitan a ranar Jumma’a, 19 ga Satumba, 2025.

Shugaban SSANU, Muhammed Ibrahim, ya bayyana cewa sun riga sun aikawa da gwamnati takarda tun ranar 18 ga Yuni, 2025, domin jawo hankalin gwamnati kan ukatunsu.

Takardar ta kunshi wasu daga cikin matsalolin albashi da rashin biyan alawus da kungiyoyin ke fuskanta duk da zaman da aka yi da su a baya.

Kungiyoyin NASU da SSANU sun ce bayan isar da wa’adin kwanaki bakwai ga gwamnati, an kafa kwamitin tuntuba domin nazarin korafin da suka gabatar.

SSANU da sauransu sun gana da gwamnati

Kara karanta wannan

Magoya bayan Peter Obi sun tanka bayan ADC ta ba'yan hadaka umarni

Kwamitin ya kunshi manyan jami’ai daga Ma’aikatar Ilimi da ta Kwadago, da kuma hukumar kula da jami’o’i ta kasa, (NUC).

SSANU, NASU sun ce sun zauna da jami'an gwamnati
Hoton Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Sanarwar da kungiyoyin su ka fitar ta ce:

“An tattauna batutuwan da suka shafi bukatunmu, amma har yanzu ba a cimma matsaya ba. Don haka sai muka yanke shawarar kara wa’adin da makonni biyu."

Kungiyoyin sun bayyana cewa wannan karin wa’adi zai bai wa gwamnati damar shawo kan matsalolin kafin su dauki matakin yajin aiki.

Kungioyin sun ce:

“Idan gwamnatin tarayya ta gaza daukar matakin da ya dace kafin cikar wa’adin da aka kara, ba shakka JAC na NASU da SSANU za su tsunduma yajin aikin da doka ta halatta."

Yanzu haka, 'yan kungiyoyin biyu na jiran amsar gwamnati kafin su dauki mataki, inda suke bukatar a biya su dukkannin hakkokinsu da suka hada da bashin alawus da sauransu.

Daliba ta magantu kan shirin yajin aiki

Hadiza Musa, daliba ce a jami'ar BUK da ke Kano, ta bayyana wa Legit cewa a halin da ake ciki da ta ke karatunta na Digiri na biyu, ba sa fatan a yi yajin aiki.

Kara karanta wannan

Kazamin rikicin manoma ya firgita Darazo, ya hana zuwa gona a Bauchi

Ta ce:

"Mu dan Allah su shirya a tsakaninsu, yajin aikin nan ba don shi mu ke ba."

Ta ce daga cikin abin da ke tsorata dalibai a makarantun gwamnatin Najeriya shi ne yajin aiki.

Kungiyar ASUU ta tabo batun yajin aiki

A baya, mun ruwaito cewa Ƙungiyar malaman jami’o’i ta ƙasa (ASUU) ta sake tada jijiyoyin wuya, tana gargadin yiwuwar shiga yajin aikin gama-gari a duk faɗin ƙasar nan.

Ta ce tana kokarin tafiya yajin aikin ne saboda gazawar gwamnatin tarayya wajen cika yarjejeniyoyin da aka dade ana kai ruwa rana akansu da za su taimaki ilimin a kasa.

Shugaban ƙungiyar ASUU na ƙasa, Farfesa Christopher Piwuna, ya bayyana haka ne yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a jami’ar Jos, yana cewa sun gaji.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng