'Dan Majalisa Gabdi Ya ce Gwamnoni ne Matsalar Kasar nan, Ya ba Talakawa Shawara

'Dan Majalisa Gabdi Ya ce Gwamnoni ne Matsalar Kasar nan, Ya ba Talakawa Shawara

  • 'Dan majalisar Pankshin/Kanke/Kanam a majalisar wakilai ta tarayya, Hon. Yusuf Adamu Gagdi ya kare Shugaban kasa Bola Tinubu
  • Ya bayyana cewa Shugaban Kasa yana bakin kokarinsa wajen rage matsalolin da ke addabar kasa, amma wasu gwamnoni na hana ruwa gudu
  • Hon Gagdi ya bayyana cewa kudin da jihohi ke karba sun karu sau uku tun bayan cire tallafin man fetur, amma ba sa abin da ya dace

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – 'Dan majalisar wakilai mai wakiltar Pankshin/Kanke/Kanam a majalisar wakilai ta tarayya, Hon. Yusuf Adamu Gagdi, ya ce Gwamnatin Tarayya na aikin da ya dace.

Ya bukaci ‘yan Najeriya da su rika tambayar gwamnoni dalilin halin da su ke ciki a maimakon mayar da yawu ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kadai.

Kara karanta wannan

Zargin N3bn: Alkali ya fara fusata, an shekara 10 ana shari'ar tsohon gwamna da EFCC

Hon Gadgi ya dura a kan Gwamnoni
Hoton 'Dan Majalisa, Hon. Yusuf Gagdi a zauren majalisa Hoto: Hoto: @YusufAdamuGagdi
Source: Facebook

Gagdi ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels TV a ranar Talata, 23 ga Satumba, 2025.

'Dan Majalisa ya soki gwamnoni

Daily Trust ta ruwaito cewa Hon. Gagdi ya bayyana cewa gwamnoni ba sa yin aiki da ya dace da kudin da suke karba daga gwamnatin tarayya.

Ya ce suna sharafinsu duk da karin kudin shiga da aka samu daga asusun gwamnatin tarayya bayan cire tallafin man fetur.

Ya ce:

"Ranar da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya hau mulki, ya fadi a fili cewa, an cire tallafin man fetur. Wannan ba kawai magana ba ce, ya tabbatar da hakan a aikace."

Ya kara da cewa jihohin da ke karbar N4bn a kowane wata kafin cire tallafin, yanzu suna karbar tsakanin Naira biliyan 10 zuwa 14.

Sai dai ya yi tambaya, inda ya ce:

Kara karanta wannan

'Dan majalisa ya shawarci Atiku Peter Obi kan takara da Tinubu a 2027

“Me ya sa ‘yan Najeriya da majalisun jihohi ba sa tambayar abin da gwamnoni ke yi da wadannan makudan kudi?”

'Dan majalisa ya kare gwamnatin Tinubu

Hon. Yusuf Gagdi ya yi nuni da cewa gwamnatin tarayya na aiwatar da manufofin da suka shafi jama'a kai tsaye domin saukaka masu.

Hon. Gagdi ya kare Tinubu
Hoton Shugaban Kasar Najeriya, Bola Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ya zayyano cewa ana shirye-shiryen da su ka hada da bayar da rancen karatu ga dalibai, tallafi ga iyalai, da kuma taimakawa kanana da matsakaitan masana’antu.

A cewar 'Dan Majalisar:

“Shin za mu iya cewa gine-ginen da ake yi a jihohi sun dace da adadin kudin da suke karba? Idan kudin da ake bai wa jihohi sun ninku sau uku, amma babu aikin da ya dace da hakan, to akwai babbar matsala.”

Gagdi ya bukaci ‘yan Najeriya su farka daga dogaro da shugabancin tarayya kadai, su kuma fara duba yadda gwamnoni ke tafiyar da albarkatun da suke samu daga gwamnati.

Ya kara da cewa akwai bukatar gaskiya da rikon amana daga shugabannin jihohi domin gyaran tattalin arziki ya kai ga kowa da kowa.

Kara karanta wannan

Otedola ya goyi bayan Dangote a rikicinsa da 'yan kasuwar mai, a shawarci DAPPMAN

Majalisar tarayya ta kara tsawon hutu

A baya, kun samu labarin cewa Majalisar Tarayyar Najeriya ta sanar da dage ranar da aka shirya dawowar sanatoci da ‘yan majalisar wakilai zuwa zauren majalisa.

A bisa jadawalin farko, an shirya cewa za a dawo zaman majalisar ne a ranar Talata, 23 ga watan Satumba, 2025, sai dai a wata sabuwar takarda da aka fitar ta ce an dage.

Sanarwar, wacce aka tura ta ofishin shugaban ma’aikatan shugaban majalisar dattijai, Chinedu Akubueze, ta bukaci sanatoci su lura da wannan sauyi, su dawo ranar 7 ga watan Oktoba, 2025.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng