Ewugu: Tsohon Mataimakin Gwamnan da 'Yan Bindiga Suka Sace kafin Ya Rasu
- Tsohon mataimakin gwamnan Nasarawa, Solomon Ewuga, ya rasu bayan fama da jinya mai tsawo
- Ya taɓa rike mukaman ministan Abuja, sannan ya wakilci Nasarawa ta Arewa a majalisar dattawa
- Ewuga ya bar PDP zuwa APC a shekarar 2023, kuma 'yan bindiga sun taba sace shi, suka masa rauni
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Nasarawa – Tsohon mataimakin gwamnan jihar Nasarawa, Solomon Ewuga, ya rasu yana da shekara 70.
Bayan rasuwarsa, an fara magana kan wasu abubuwa da suka faru da shi, ciki har da mutuwar 'yarsa a hadarin jirgin sama.

Source: Twitter
Daily Trust ta wallafa cewa Ewuga ya kasance ɗan siyasa mai tasiri a matakin jiha da kasa, inda ya taɓa rike mukamai masu muhimmanci ciki har da ministan Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A shekarar 2023 ne ya yi kaurin suna a kafafen yada labarai bayan ya sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC, lamarin da ya girgiza siyasar jihar.
Tarihin siyasar Sanata Ewugu
Solomon Ewuga, wanda lauya ne kuma ɗan jarida, ya fara tasiri a siyasar Nasarawa tun shekarar 1999.
A lokacin, ya tsaya takarar kujerar gwamna a jam’iyyar PDP tare da Abdullahi Adamu, bayan Adamu ya lashe zaben fitar da gwani, an zabi Ewuga a matsayin mataimakinsa.
Bayan PDP ta yi nasara a zaben gwamna, an mika sunansa ga shugaba Olusegun Obasanjo a matsayin minista daga Nasarawa.
A watan Yunin 1999 aka nada shi Ministan Abuja, inda ya yi aiki tsawon shekara biyu kafin Obasanjo ya sallame shi.
Ewugu ya shiga jam'iyyar su Buhari
Bayan dawowa daga Abuja, Ewuga ya sake shiga fafutukar neman gwamna a shekarar 2003 da 2007 amma bai yi nasara ba.
Daga bisani ya sauya sheka zuwa ANPP, sannan ya koma CPC inda ya hada kai da Tanko Al-Makura, hakan ya kai ga kayar da tsohon gwamna Aliyu Akwe Doma a zaben 2011.
A wannan lokaci ne Ewuga ya lashe kujerar Sanata a CPC, inda ya wakilci Nasarawa ta Arewa a majalisar dattawa ta 7.
The Sun ta wallafa cewa yayin zaman nasa, ya taka muhimmiyar rawa wajen kare muradun mazabarsa da kuma taimaka wa harkokin majalisa.
'Yan bindiga sun taba sace Ewugu
Bayan yin wa’adi daya a majalisar dattawa, ya sake neman kujerar gwamna amma bai samu nasara ba.
Rayuwar Ewugu ta fuskanci kalubale sosai, ciki har da mutuwar ‘yarsa wacce take matuƙar tasiri gare shi.

Source: Facebook
'Yar tsohon mataimakin gwamnan, wacce take matuƙiyar jirgi ce, ta rasu a hadarin jirgin sama a Kamaru.
Haka kuma, an taba sace shi tare da yin masa rauni mai tsanani wanda ya hana shi zirga zirga na tsawon lokaci.
Ewuga ya kammala karatun digirinsa a fannin kimiyyar siyasa a Jami’ar Ibadan daga 1974 zuwa 1977.
Ewugu ya yi kira ga Jonathan
A wani rahoton, kun ji cewa Solomon Ewugu ya taba yin kira ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan kan siyasa.
A shekarar 2022, Sanata Ewugu ya gargadi Goodluck Jonathan da cewa girmansa zai zube idan ya sake neman takara.
Ewugu ya yi magana ne yayin da yake harin neman gwamnan jihar Nasarawa bayan ya sha fama a baya bai samu ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


