Sanata Barau ya bi Sahun Gwamna Abba, ya Tura Dalibai 1000 Karatu a Jami'ar Katsina
- Jami’ar Tarayya Dutsin-Ma ta yi bikin karbar ɗalibai 1,000 da suka ci gajiyar tallafin karatu ta gidauniyar Mataimakin Shugaban Majalisa, Sanata Barau Jibrin
- An gudanar da bikin a ranar Litinin, inda manyan baki ciki har da daraktoci da shugabanni daga Kano da yankin Arewa maso Yamma su ka halarta
- Ƙungiyar ɗaliban Jihar Kano ta ce ta tabbatar da gudunmawar da Sanatan ya ke bayarwa a wajen bunkasa ilimin matasa da samar masu da ci gaba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Jami’ar Tarayya Dutsin-Ma (FUDMA) da ke Jihar Katsina ta gudanar da bikin karbar ɗalibai 1,000 da suka samu tallafin karatu.
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan kasar nan, Sanata Barau Jibrin ne ya dauki nauyin karatun daliban da za su fara digiri na farko.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa bikin, wanda aka yi a ranar Litinin a harabar jami’ar, ya samu halartar manyan baki da dama.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daga ciki akwai Shugaban Hukumar Cigaban Arewa maso Yamma (NWDC), Farfesa Abdullahi Shehu Maaji da Shugaban Ma’aikata na ofishin Sanata Barau, Farfesa Muhammad Ibn Abdallah.
Sanata Barau ya dauki nauyin karatun dalibai
The Nation ta ruwaito cewa sanarawar da mai ba Barau shawara kan harkokin yaɗa labarai, Ismail Mudashir, ya fitar a Abuja ta ce wannan ya nuna jajircewar Sanatan wajen ci gaban jama'a.
Ya kara da cewa Sanata Barau Jibrin ya himmatu a wajen bunƙasa ilimi a tsakanin matasa, ba kawai a Kano ba har ma a sauran sassan ƙasar nan.

Source: Twitter
Ta gidauniyar Barau Ibrahim Jibrin (BIJF), dubunnan ɗalibai sun samu tallafin karatu domin cigaban ilimi a Najeriya da ƙasashen waje.
A halin yanzu, akalla ɗalibai 70 na ci gaba da karatun digiri na biyu da na uku a manyan jami’o’i a ƙasashen waje.
An jinjinawa Sanata Barau Jibrin
A jawabin Sanatan ta bakin Shugaban Ma’aikatansa, Muhammad Ibn Abdullah, ya nuna jin daɗinsa tare da gode wa hukumar Jami’ar Tarayya Dutsin-Ma.
Ya bayyana cewa jami'ar a ƙarƙashin Shugabanta, Farfesa Aminu Ado, ta ba su haɗin kai wajen aiwatar da wannan shiri na daukar nauyin karatun dalibai.
Haka kuma, ƙungiyar ɗaliban Jihar Kano (NAKSS) reshen FUDMA, ta karrama Sanata Barau da lambar yabo saboda irin gudummawar da yake bayarwa wajen bunkasa ilimi da cigaban matasa.
Daliban na ganin cewa irin wannan taimako ya tabbatar da sha’awar Sanata Barau wajen ganin matasa sun samu ingantaccen ilimi domin su taka rawa wajen gina ƙasar nan.
Sanata Barau ya yi koyi da Kwankwasiyya
A wani labarin, mun wallafa cewa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya kaddamar da sabon shirin tallafin karatu ga dalibai 300 don karo digiri na biyu.
Wannan na zuwa ne bayan nasarar shirin da ya kai dalibai 70 zuwa kasar Indiya domin digirin digirgir, wanda aka fara tun ranar 29 ga Disamba, 2024, a filin jirgin saman Malam Aminu Kano.
A cewar Ismail Mudashir, mai ba Sanatan shawara kan harkokin yada labarai, ya wannan tallafin karatu na cikin gida zai gudana a karkashin gidauniyar Sanata Barau.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


