'Yan Bindiga Sun Kai Hari a Zamfara, an Yi Awon Gaba da Mutane Masu Yawa
- An shiga jimami a jihar Zamfara bayan wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun farmaki mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba
- Tsagerun 'yan bindigan sun kai farmakin ta'addancin ne a wani kauye da ke karamar hukumar Bungudu
- Harin na 'yan bindigan ya jawo an raunata wasu mutum uku tare da yin awon gaba da mutane masu yawa zuwa cikin daji
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Zamfara - Ƴan bindiga dauke da makamai sun kai farmaki a karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara.
'Yan bindigan sun kai harin ne a kauyen Bayan Dutsi da ke yankin Tofa, a karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara.

Source: Facebook
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan bindiga sun yi ta'asa a Zamfara
A yayin harin, 'yan bindigan sun raunata mutane uku tare da sace wasu da ba a tantance adadinsu ba.
Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10:15 na dare a ranar Litinin, 22 ga Satumban 2025.
'Yan bindigan sun kutsa kauyen ne suna harbe-harbe kan mai uwa da wabi, lamarin da ya jawo raunuka ga wasu mazauna yankin tare da yin garkuwa da wasu.
"Bayan samun rahoton gaggawa, dakarun haɗin gwiwa na Operation Fansa da jami'an rundunar Askarawan Zamfara sun garzaya zuwa yankin."
"An garzaya da waɗanda suka jikkata zuwa asibiti domin kula da lafiyarsu."
- Wata majiya
Jami'an tsaro sun tsaurara matakan kariya
Haka kuma, majiyoyin sun bayyana cewa jami’an tsaro sun kara ninka kokarin da suke yi domin ceto mutanen da aka sace da kuma dawo da zaman lafiya a yankin da lamarin ya shafa.
Hare-haren 'yan bindiga sun zama ruwan dare a jihar Zamfara, inda tsagerun suke cin karensu babu babbaka.
Mutane da dama sun rasa rayukansu yayin da wasu suka rasa matsugunansu sakamakon hare-haren na 'yan bindiga.
Ko a cikin 'yan kwanakin nan, sai da 'yan bindiga suka yi awon gaba da mutum 18 da suka hada da mata da yara a wani hari da suka kai a Zamfara.

Source: Original
Karanta wasu karin labaran kan 'yan bindiga
- Tashin hankali: An harbe wani jagoran jam'iyyar APC har lahira a gaban iyalinsa
- Tsohon dan bindiga mai shekara 70 da ya ajiye makamai ya yi jawabi a Katsina
- 'Yan bindiga sun kashe ƴan sandan Najeriya 5, sun yi awon gaba da bindigoginsu a Kogi
- Dubu ta cika: 'Yan sanda sun cafke kasurgumin jagoran 'yan bindiga a Zamfara
Sojoji sun fafata da 'yan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun yi arangama mai zafi da 'yan bindiga a jihar Neja.
Sojojin tare da hadin gwiwar 'yan sa-kai sun fafata da 'yan bindigan ne a wani kauye da ke karamar hukumar Mariga.
Dakarun sojojin sun nuna bajinta yayin artabun, inda suka hallaka 'yan bindiga masu tarin yawa tare da kubutar da fararen hula.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

