Sardauna: An Samu Karin Goyon Baya a Kudirin Kirkiro Jiha 1 a Arewacin Najeriya
- Manyan mutane sun fara goyon bayan bukatar kirkiro jihar Sardauna daga cikin jihar Taraba a Arewacin Najeriya
- Tsohon Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Hon. Babangida Nguroje ya ce samar da jihar zai kara bude damarmakin bunkasa tattalin arziki
- Nguroje ya kuma goyi bayan bukatar samar wa sarakuna matsuguni a doka da ware wa mata kujeru a Majalisar Dokokin Tarayya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Taraba - Tsohon Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Babangida Nguroje, ya goyi bayan bukatar kirkiro sabuwar jiha mai suna, 'jihar Sardauna' daga cikin Taraba.
Tsohon Dan Majalisar ya kuma goyi bayan bai wa sarakuna matsayi a doka, ware wa mata kujeru na musamman a Majalisar Tarayya da kuma kafa karamar hukumar Nguroje.

Source: Facebook
Tribune Nigeria ta rahoto cewa Hon. Babangida Nguroje ya fadi haka ne a taron sauraron ra’ayoyi na jama’a kan gyaran kundin tsarin mulkin 1999 da Majalisar Wakilai ta shirya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kirkiro jihar Sardauna bai karya doka ba
Ya bayyana cewa neman ƙirƙiraro jihar Sardauna daga cikin jihar Taraba ta yanzu babbar buƙata ce wacce ta ta’allaka da tarihi, doka, al’adu da tattalin arziki.
Ya ce suna da hujjar neman ƙirƙirar wannan jiha, domin hakan ya yi daidai da tanade-tanaden Sashe na 8 (1) da (2) na kundin tsarin mulki na 1999, wanda ya ba al’umma dama su nemi kafa sababbin jihohi da ƙananan hukumomi.
Yayin da yake roƙon Kwamitin Majalisar Wakilai da ya duba wannan bukata, Hon. Babangida ya ce:
“Ya kamata Majalisar Wakilai da ma Majalisar Dattawa su fifita ra’ayoyin jama’a tare da samar da kundin tsarin mulki wanda za a iya cewa ya fito ne daga muradun mutane.
“Sardauna tana Kudu maso Gabashin Taraba a kan dutsen Mambilla, inda take da manyan hanyoyin arziki saboda kyawawan yanayinta.
“Yanki ne na noma da kiwo, tare da yanayi mai sanyi da ke jawo masu yawon buɗe ido, kuma tana da ruwan da zai samar da lantarki mai karfin megawatts 3,050."
Tsohon dan Majalisa ya goyi bayan kudirin
Ya ƙara jaddada cewa masarautu a Najeriya na taka muhimmiyar rawa wajen tsaron al’umma, adana al’adu da kiyaye dabi’un jama’a, cewar rahoton Guardian.
Tsohon dan Majalisar ya ci gaba da cewa:
“Ra’ayina shi ne a bai wa sarakunan gargajiya wani matsayi na doka don su ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen kyautata wa al’umma.
“Haka nan ina ganin ware kujeru na musamman ga mata a majalisar dokoki zai zama gagarumin ci gaba wajen faɗaɗa dimokuradiyya da musayar ra’ayoyi.
"Sannan kuma zai ƙara wa sauran mata da ‘yan mata kwarin gwiwa su shiga siyasa da shugabanci.”
- - Hon. Babangida Nguroje.

Source: Facebook
Abubuwan da za a duba kafin kafa jihohi
A wani rahoton, kun ji cewa Majalisa za ta duba dukkan muhimman abubuwa da suka wajaba kafin ta amince da bukatun ƙirƙiro jihohi a Najeriya.
Majalisar Dattawa ce ta bayyana hakan ta bakin mai magana da yawunta kuma Shugaban Kwamitin Yada Labarai, Sanata Yemi Adaramodu.
Ya ce duk da yan Najeriya na ci gaba da kiraye-kirayen kirkiro jihohi, za a gudanar da lamarin cikin gaskiya, ba tare da nuna son zuciya ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


