Daruruwan Maguzawa Sun Shiga Musulunci a Kano sanadiyyar Ganduje

Daruruwan Maguzawa Sun Shiga Musulunci a Kano sanadiyyar Ganduje

  • Tsohon shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Ganduje, ya jagoranci addu’o’i da wani taron karbar wadanda suka musulunta
  • Baya ga haka, Ganduje ya halarci bikin bankwana da tsohon shugaban jami'ar Bayero da tarbar sabon shugaban jami’ar
  • A ziyarce-ziyarcen da ya yi, tsohon gwamna Abdullahi Ganduje ya je ta’aziyya ga iyalan fitattun mutane da suka rasu a Kano

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano – Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa kuma tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya halarci jerin taruka da dama a Kano daga ranar 20 zuwa 22 ga Satumba, 2025.

Daga ziyarar ta’aziyya zuwa bikin jami’a, har zuwa jagorantar addu’o’i, Ganduje ya bayyana cewa wannan al’ada ce da yake ci gaba da yi don ƙarfafa zumunci da kuma ci gaban jihar Kano.

Kara karanta wannan

Tsohon dan bindiga mai shekara 70 da ya ajiye makamai ya yi jawabi a Katsina

Abdullahi Ganduje yayin taron musuluntar da maguzawa a Kano
Abdullahi Ganduje yayin taron musuluntar da maguzawa a Kano. Hoto: @GovUmarGandujee
Source: Twitter

Legit ta tattaro bayan kai wuraren da Ganduje ya ce ne a wani sako da tsohon gwamnan ya wallafa a shafinsa na X.

Maguzawa 280 sun musulunta a Kano

A ranar 22 ga watan Satumban 2025, Ganduje ya bayyana cewa ya jagoranci karatun Alƙur’ani mai girma tare da addu’o’i a gidansa da ke Kano.

A yayin taron, kimanin maguzawa 280 da suka kasance ba Musulmi ba sun bar gargajiya zuwa Musulunci.

Ya ce irin taron yana daga cikin shirye-shiryensa na yau da kullum, inda yake haɗa malamai da al’ummar Kano don yin addu’a da neman zaman lafiya da ci gaban jihar da ƙasar baki ɗaya.

Ganduje ya je ta'aziyya gidan Dankabo

A ranar 20 ga watan Satumban 2025, Ganduje ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan fitattun mutane da suka rasu a Kano.

Ya fara ne da iyalan marigayi Hakimin Kabo, Alhaji Salisu Adamu Dankabo, sannan ya kai ziyara ga iyalan tsohon dan majalisar wakilai na Kumbotso, marigayi Hon. Ali Bala.

Kara karanta wannan

Kafa bataliya da wasu manyan alƙawura 4 da Tinubu ya yi wa Katsina kan ƴan bindiga

Ya bayyana cewa wannan dabi’a ce da yake kiyaye ta, wato halartar al’amuran jama’a na farin ciki da bakin ciki, domin nuna goyon baya da ƙarfafa zumunci da al’ummar jihar.

Ganduje ya halarci taron jami'ar BUK

A ranar 21 ga watan Satumban 2025 , anduje ya halarci wani gagarumin biki a Kano wanda ya shafi Jami’ar Bayero ta Kano (BUK).

Taron ya kasance na bankwana ga tsohon shugaban jami’ar, Farfesa Sagir Adamu, tare da tarbar sabon shugaban jami’ar na 12, Farfesa Haruna Musa.

Abdullahi Ganduje yayin taron jami'ar Bayero. Hoto: @GovUmarGandujee
Abdullahi Ganduje yayin taron jami'ar Bayero. Hoto: @GovUmarGandujee
Source: Twitter

An gudanar da taron ne a wajen taron Amani, inda uwargidan Ganduje, Farfesa Hafsat Ganduje, ta kasance mai masaukin baki da mai shirya taron.

An daura auren 'yar gidan Dantata a Kano

A wani rahoton, kun ji cewa an daura auren 'yar Alhaji Sayyu Idris Dantata a jihar Kano ranar Asabar da ta wuce.

Rahotanni sun bayyana cewa dan tsohon ministan shari'a, Muhammad Bello Adoke ne ya auri 'yar attajirin.

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Alhaji Aliko Dangote da Sanata Ibrahim Dankwambo da wasu manyan baki sun halarci daurin auren.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng