Maguzawa 200 sun karbi kalmar Shahada a hannun Ganduje a fadar gwamnatin Kano
Gwamnan jahar Kano, kuma Khadimul Islam, Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya musuluntar da akalla maguzawa maza da mata 200 da suka kai masa ziyara a fadar gwamnatin jahar Kano.
Hadimin Gwamna Ganduje a kan kafafen sadarwar zamani, Salihu Tanko Yakasai ne ya bayyana haka a shafinsa na Facebook inda yace maguzawan sun fito ne daga yankunan karamar hukumar Sumaila ta jahar Kano.
KU KARANTA: Harin yan bindiga: Ministan sufuri Amaechi ya tsallake rijiya da baya a jahar Kaduna

Asali: Facebook
“Malamai daban daban daga bangare daban daban ne suka jagoranci baiwa maguzawa kalmar shahada, a taron da ya gudana a babban dakin taro na fadar gwamnatin jahar Kano a ranar Lahadi.” Inji shi.
Idan za’a tuna a kwanakin baya ne gwamnan jahar Kano, Abdullahi Ganduje bayyana nasarar da jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ta samu a zaben maye gurbin da aka kammala a jihar a matsayin alama da ke nuna cewa an yi wa tsohon gwamna Rabi'u Musa Kwankwaso ritaya daga siyasa.

Asali: Facebook
Sanarwar da babban sakataren yada labarai na gwamnan, Abba Anwar ya fitar a ranar Juma'a ya ce gwamnan ya yi wannan jawabin ne yayin da ya ke maraba da Kakakin majalisar jihar, Abdulaziz Gafasa da wasu manyan masu rike da mukamai a majalisar da suka raka sabbin 'yan majalisun jihar hudu zuwa gidan gwamnati.
A cewar Ganduje, nasarar da ya samu a kotun koli ta sake tabbatarwa cewa Rabiu Kwankwaso ya yi ritaya daga siyasa.

Asali: Facebook
"A shekarun baya kokacin da shi (Kwankwaso) ke shirin takarar kujerar shugaban kasa, ya yi ta cika bakin cewa zai yi wa Shugaba Buhari ritaya daga siyasa. Ya ce nima zai min ritaya. Amma idan ka duba yanzu, wanene aka tilastawa yin ritaya?," in ji Ganduje.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitnghausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng