Abin da Ka Shuka: An Yanke Wa Wasu Manyan Sojojin Najeriya 3 Hukuncin Daurin Rai da Rai

Abin da Ka Shuka: An Yanke Wa Wasu Manyan Sojojin Najeriya 3 Hukuncin Daurin Rai da Rai

  • An yanke wa sojoji uku hukuncin daurin rai da rai bayan kama su da satar makiamai da sayar wa yan ta'adda a Najeriya
  • Kotun Soji da ke Maiduguri a jihar Borno ta daure sojojin a gidan yari bayan sun amsa laifuffukan da ake tuhumarsu
  • Shugaban kotun ya ce rundunar aoji ba za ta lamurci irin wadannan dabi'u na sojojin ba domin cin amanar kasa ne

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Maiduguri, jihar Borno - Kotun soji ta musamman da aka kafa ta kama wasu manyan sojoji biyu da wasu kananana biyu da laifin taimaka wa 'yan ta'adda.

Kotun ta yanke wa dakarun sojoji, wadanda aka kama da laifin safara da sayar da makamai da bisa ka'ida ba, hukuncin daurin rai da rai a gidan yari.

Sojojin Najeroya.
Hoton wasu jami'an sojin Najeriya a bakin aiki Hoto: @NigeriaArmy
Source: Getty Images

Jaridar Leadership ta tattaro cewa shugaban kotun soja, Birgediya Janar Mohammed Abdullahi, ne ya karanto hukuncin a harabar kotun da ke sansanin Sojoji a Maiduguri.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gwabza kazamin fada da 'yan bindiga, an samu asarar rayuka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hukuncin da kotu ta yanke wa sojoji 4

Ya ce an yanke wa Rapheal Ameh, Ejiga Musa da LCpl Patrick Ocheje hukuncin daurin rai da rai, yayin da aka yanke wa Cpl Omitoye Rufus hukuncin daurin shekara 15 bayan sun amsa laifuffukan da ake tuhumarsu da su.

Hukunci ya biyo bayan amsa laifuffukan da wadanda ake zargin suka yi, wanda suka haɗa da "sata da kasuwancin makamai ba bisa ka’ida ba, da taimakon yan ta'adda."

Duka wadannan laifuffuka da sojojin auka aikata sun saba wa dokokin sojojin Najeriya, cewar rahoton BBC Hausa.

Yadda sojojin suka rika kasuwancin makamai

Tun farko a zaman kotun, shaidu sun nuna cewa Sajan Rapheal, wanda shi ne mai kula da bindigogi a 7 Division Garrison, ya haɗa baki da LCpl Ogbogo Isaac (wanda ya rasu) wajen satar harsasai daga rumbun ajiyar makamai.

Haka kuma, ya hada baki wasu jami’an yan sanda, Insufekta Francis Ajayi da Francis Manasseh, suka ɓoye makamai a cikin buhunan wake, suka tafi da su jihohin Enugu da Ebonyi.

Kara karanta wannan

Matsala ta girma: An gano gawarwakin yan sanda 8 bayan sun bace a Najeriya

A wadannan jihohi ne suka sayar da makaman ga yan ta'adda kuma an gano cewa Sajan Rapheal ya karɓi kuɗin wannan safarar ta asusun banki tsakanin Yuli, 2022 zuwa Yuni, 2024.

Shi ma Ejiga Musa, wanda shi ne babban mai kula da makamai a 195 Battalion, ya hada kai da LCpl Patrick Ocheje suka sayar da bindigar AK-47 da kuma adadi mai yawa na harsasai.

Rahotanni sun nuna cewa ya karɓi sama da ₦500,000 daga wannan safarar kafin a kama shi lokacin da yake ƙoƙarin sayar da harsasai ga Sufeta Francis Ajayi.

Babban hafsan sojin Najeriya, Christopher Musa.
Hoton Babban Hafsan Sojin Najeriya, Manjo Janar Christopher Musa tare da wasu jami'ai Hoto: @DHQNigeria
Source: Twitter

Illar laifuffukan da sojojin suka aikata

Kotun ta bayyana cewa satar makaman ya sanya sojoji cikin haɗari, ya kawo cikas ga ayyukan tsaro, wanda hakan ya zama daidai da “taimakawa abokan gaba.”

Shugaban kotun soja, Birgediya Janar Abdullahi, ya ce ayyukan “wadannan gurbatattun jami’ai” ba wai kawai karya doka ba ne, cin aman ne ya iarya dokar aikin soja.

Abin fashewa ya tashi a masana'antar sojoji

A wani rahoton, kun ji cewa wani ya tarwatse a masana'antar kera makaman yakin sojojin Najeriya da ke cikin garin Kaduna.

Kara karanta wannan

Me ke faruwa? Mata 3 da suka ci zaben kansila, da mataimakiyar ciyaman sun mutu

Rahotanni sun bayyana cewa mutum biyu sun mutu ciki har da soja guda daya yayin da wasu da dama suka ji munanan raunuka.

Wannan lamari dai ya tada hankulan mutane a kewayen masana'antar, wacce ke unguwar Kurmin Gwari a cikin birnin Kaduna.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262