Sojoji Sun Gwabza Fada da 'Yan Bindiga, an Samu Asarar Rayuka da Dama
- Dakarun sojojin Najeriya na ci gaba da kokarin samar da tsaro a yankunan daban-daban na kasar nan
- Jami'an tsaron sun yi artabu da 'yan bindiga bayan da suka kai hari a karamar hukumar Mariga ta jihar Neja
- Kazamin artabun da bangarorin biyu suka yi, ya jawo an samu asarar rayuka tare da jikkata wasu mutane
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Neja - Dakarun sojojin Najeriya da ke aiki tare da ’yan sa-kai sun yi arangama da ’yan bindiga a jihar Neja.
Sojojin sun fafata da 'yan bindigan ne a kauyen Dare Biyu, kusa da Beri, a karamar Hukumar Mariga ta jihar Neja a ranar Litinin.

Source: Twitter
Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Majiyoyi sun bayyana cewa an yi arangamar ne tsakanin ƙarfe 6:00 na yamma zuwa 7:00 na dare.
Sojoji sun kashe 'yan bindiga
Fafatawar ta haifar da hallaka ’yan bindiga da dama, yayin da wani ɗan sa-kai ya rasa ransa, sannan wani ya jikkata sakamakon harbin bindiga.
An bayyana sunayen waɗanda suka mutu a matsayin Yusuf Dan Basi da Bello Shagari, yayin da wanda ya jikkata, Naziru Lawal, ke samun kulawa a asibitin Beri.
Majiyar ta ce da farko 'yan bindigan sun sanya sojoji da ’yan sa-kai a tsakiya, amma sai suka mayar da martani mai zafi, suka yi luguden wuta, suka kwashe waɗanda suka jikkata tare da kare fararen hula a yankin.
Majiyoyin sun kara da cewa ’yan bindigan sun zo ne a kan babura da kuma a kafa, inda suka rika amfani da dabarun kashe baburan don kaucewa gano su.
Rahotannin sun bayyana cewa waɗanda suka kai harin suna da alaka da manyan kungiyoyin ’yan bindiga da ke aiki a Mariga, Kontagora, Magama, Rijau da kuma Mashegu a jihar Neja.
'Yan bindiga na barazana ga fararen hula
Masu nazarin tsaro sun yi gargadi cewa ci gaba da kasancewar ’yan bindiga a kusa da Beri barazana ce kai tsaye ga fararen hula da hanyoyin sufuri.
Sun ba da shawarar a ƙarfafa tsaron hanyar Beri–Mariga–Kontagora, kafa shingayen bincike, amfani da jiragen sintiri, da kuma kaddamar da hare-hare kan kungiyoyin ’yan bindigan.

Source: Original
Karanta wasu labaran kan 'yan bindiga
- Tashin hankali: An harbe wani jagoran jam'iyyar APC har lahira a gaban iyalinsa
- 'A ina 'yan bindiga ke samun makami?' An yi wa Tinubu tambaya mai zafi
- 'Yan bindiga sun kashe ƴan sandan Najeriya 5, sun yi awon gaba da bindigoginsu a Kogi
'Yan bindiga sun sace basarake a Plateau
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai, sun yi awon gaba da wani basarake a jihar Plateau.
'Yan bindigan sun yi garkuwa ne da Hakimin Birbyang, Alhaji Zubairu Garba, a jihar Plateau.
Tsagerun sun sace basaraken ne tare da wasu mata guda biyu a karamar hukumar Kanam ta jihar Plateau bayan sun dira a cikin gidansa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

