'Yan Bindiga Dauke da Makamai Sun Sace 'Dan Majalisa a Filato
- Dan majalisar jihar Filato mai wakiltar Pankshin ta Kudu, Hon. Laven Denty ya shiga hannun masu garkuwa da mutane
- Rahotanni sun bayyana cewa an sace shi ne a gidansa da ke wata unguwa a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa
- Hakan na zuwa ne yayin da jihar Filato ke cigaba da fuskantar matsalar tsaro da garkuwa da mutane a sassa daban daban
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Filato – Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu ‘yan bindiga sun sace ɗan majalisar dokokin jihar Filato mai wakiltar mazabar Pankshin ta Kudu, Hon. Laven Denty.
Jihar Filato dai na cikin jihohin Arewacin Najeriya da ke fama da matalar tsaro tsawon shekaru da suka wuce.

Source: Original
Rahoton tashar AIT ya bayyana cewa an sace dan majalisar ne bayan dauke wani mai hidimar kasa a jihar a kwanakin baya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ina aka sace dan majalisar a Filato?
Daily Post ta wallafa cewa an sace ɗan majalisar ne a gidansa da ke wata unguwa a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa.
Ba a samu wata sanarwa daga hukumomin jihar ko kuma rundunar ‘yan sanda ta Filato ba a kan lamarin, a lokacin da aka wallafa wannan rahoton.
Garkuwa da mutane a garuruwan Filato
Wannan ba shi ne karon farko da masu garkuwa suka kutsa garinsu dan majalisar ba, a makon da ya gabata ma, an kai hari inda aka yi garkuwa da dan NYSC da kuma wani ɗalibin jami’ar Jos.
Rahotanni sun ce masu garkuwa sun shiga gidan wani mai suna Solomon Dansura da misalin ƙarfe 10:00 na dare, inda suka yi awon gaba da baƙinsa guda biyu.
Rahoton gwamnatin Filato kan tsaro
A ‘yan kwanakin da suka gabata, wani kwamiti na musamman da gwamnan jihar Caleb Mutfwang ya kafa domin binciken kashe-kashe a Filato ya gabatar da rahotonsa.
Shugaban kwamitin, Manjo Janar Rogers Ibe Nicholas (mai ritaya), ya bayyana cewa sun gana da kabilu da kungiyoyi daban-daban a jihar kan matsalar.
Daily Trust ta ce abin da ke jawo wadannan hare-hare sun haɗa da rikicin mallakar ƙasa, faɗa kan albarkatu, neman faɗaɗa yankuna, batutuwan addini da siyasa.

Source: Twitter
Ana kai hari Filato daga jihohi
Rahoton ya ce mafi yawan hare-haren na zuwa ne ta iyakokin da ke da kusa da jihohin makwabta.
Daga Nasarawa ana shiga Filato ta Wamba, Lafia da Awe; daga Kaduna ta Lere, Kaura da Sanga; daga Bauchi ta Toro, Tafawa Balewa, Bagoro da Alkaleri; daga Taraba ta Ibi da Karim Lamido.
An ce wadannan hanyoyi ba su da tsaro sosai, kuma hakan ke ba wa ‘yan bindiga damar kai farmaki cikin sauƙi sannan su gudu.
'Yan bindiga sun kai hari banki
A wani rahoton, kun ji cewa an fara bincike bayan wasu 'yan 'yan bindiga sun kai hari wani yanki na jihar Anambra.
Rahotanni sun bayyana cewa 'yan ta'addan sun kai hari ne cikin dare wani banki kuma suka wawure kudi masu yawa.

Kara karanta wannan
Ana sulhu da 'yan ta'adda a Katsina, 'yan bindiga sun sace hakimi da wasu mata 2 a Filato
Yayin da bankin ke kokarin gano adadin kudin da aka sace, an kaddamar da bincike domin kamo wadanda suka kai harin.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

