CWR: 'Yar Najeriya Ta Girgiza Intanet, Ta Shirya Lalata da Maza 100 don Kafa Tarihi a Duniya

CWR: 'Yar Najeriya Ta Girgiza Intanet, Ta Shirya Lalata da Maza 100 don Kafa Tarihi a Duniya

  • Yar Najeriya, Mandy Kiss ta fara shirin shiga kundin bajintar Guinness World Record (GWR) na macen da ta fi lalata maza
  • Fatacciyar mai amfani da kafar sada zumunta ta bayyana cewa za ta yi amfani da maza 100 cikin sa'o'i 24 a jihar Legas
  • Sai dai babu tabbacin ko kundin bajintar duniya zai yarda da wannan lamari da Mandy Kiss za ta zo da shi ko akasin haka

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Fitacciyar mai amfani da kafar sada zumunta a Najeriya, Ayomiposi Oluwadahunsi wacce aka fi sani da Mandy Kiss, ta shirya kafa tarihin lalata da maza.

Mandy Kiss ta bayyana shirinta na kafa tarihin mace da ta fi yin jima'i da maza masu yawa a cikin awanni 24 ma'ana kwana daya domin shiga kundin bajinta na Guinness World Record (GWR).

Kara karanta wannan

Rashawa: Amurka za ta rika daukar mataki mai tsauri kan manyan Najeriya

Kandy Kiss na shirin shiga kundin bajinta.
Hoton fitacciyar mai amfani da kafafen sada zumunta, Mandy Kiss Hoto: Real Mandy Kiss
Source: Instagram

Ta sanar da hakan ne a wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Instagram a ranar Litinin da ta gabata, 22 ga watan Satumba, 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yar Najeriya ta shirya amfani da maza 100

Mandy ta wallafa wata takarda mai dauke da tambarin GWR, tana mai cewa za ta gwada yin wannan bajinta ta kwanciya da maza 100 a ranar 30 ga watan Oktoba, 2025.

Takardar ta bayyana cewa burinta shi ne ta kwanta da “mazaje 100” cikin sa’o’i 24 a wannan rana domin shiga kundin bajinta na duniya.

Ana sa ran wannan lamari zai gudana ne a Ikorodu, Legas, duk da cewa ba a bayyana takamaiman wurin da za a gudanar da shi ba.

“Maza 100 a cikin sa'o'i 24. Zan iya kuma zan yi,” in ji Mandy a rubutun da ta fitar a shafinta.

Kundin bajintar duniya zai aminta da hakan?

Sai dai har yanzu ba a tabbatar ko kundin bajinta na Guinness World Records ya amince da wannan lamarin ba, kuma ba bu tabbacin ko za ta amince da shi idan Mandy Kiss ta yi.

Kara karanta wannan

Sabuwar cuta mai cin naman jiki ta bulla a Adamawa, gwamnati ta fara bincike

Bayanai sun nuna cewa ba wannan ne karo na farko da aka yi yunƙurin kafa irin wannan tarihi ba, in ji rahoton Tribune.

Mandy Kiss.
Hotunan Mandy Kiss da ke kokarin gwada shiga kundin bajinta na duniya Hoto: Real Mandy Kiss
Source: Instagram

A shekarar 2004, wata jarumar fina-finan batsa daga Amurka mai suna Lisa Sparx ta yi ikirarin cewa ta yi amfani da maza 919 cikin awanni 22 a Warsaw da ke kasar Poland.

Daga baya ta fayyace cewa lamarin ya haɗa da kusan mutane 150 ne kawai cikin sa’o’i 7.5

Sai dai duk da yadda aka yada labarin a lokacin, mahukuntan kundin bajinta na Guinness World Records ba su amince ko ayyana abin da ta yi a hukumance ba.

'Dan TikTok ya kare bidiyoyin da yake saki

A wani labarin, kun ji cewa G-Fresh Al’ameen ya bayyana cewa shi bai ga komai na rashin kyautawa ba game da irin bidiyon da yake yi wanda mutane ke korafi.

Ya ce shi kansa, bidiyon soki-burutsu da yake yi yana ba shi nishadi ba ma al'ummar Najeriya ba saboda bai son zama haka banza.

G-Fresh ya kuma yi karin haske kan karuwar da yake samu ta fannin kudin shiga bayan ya auri matarsa daga jihar Adamawa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262