Abu Ya Girma: An kai Karar Akpabio Majalisar Dinkin Duniya kan Natasha

Abu Ya Girma: An kai Karar Akpabio Majalisar Dinkin Duniya kan Natasha

  • Fiye da ƙungiyoyi 350 na mata sun kai ƙara ga majalisar dinkin duniya kan dakatar da Sanata Natasha Akpoti
  • Matan sun zargi majalisar dattawa da nuna wariyar jinsi da kuma kin bin umarnin kotu kan dawo da ita bakin aiki
  • Kungiyoyin sun nemi a tabbatar da tsaro da ’yancin Natasha Akpoti tare da samar da tsarin kai ƙara cikin majalisar

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Wasu ƙungiyoyin kare ’yancin mata a Najeriya sun kai ƙara ga Majalisar Dinkin Duniya kan dakatar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.

Sanata Natasha Akpoti da ake dambarwa da ita tana wakiltar Kogi ta Tsakiya ne a majalisar dattawa.

Akpabio da Natasha a majalisar dattawa
Akpabio da Natasha a majalisar dattawa. Hoto: Nigerian Senate
Source: Facebook

The Cable ta rahoto cewa kungiyoyin da ke aiki a ƙarƙashin inuwar Womanifesto kuma masu wakiltar sama da ƙungiyoyi 350 ne suka kai karar.

Kara karanta wannan

Sakkwato: Shugabannin makarantun sakandare 6 sun tsunduma kansu a matsala

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun yi zargin cewa an dauki matakin ne bisa nuna bambancin jinsi da ramuwa ga rahoton da sanatar ta gabatar.

Asalin rikicin Sanata Natasha da Akpabio

A ranar 20 ga Fabrairu, 2025 Akpoti-Uduaghan ta zargi shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, da neman lalata da ita, wanda shi kuma ya musanta.

Bayan kwana kaɗan, kwamitin ladabtarwa na majalisar dattawa ya ba da shawarar a dakatar da ita na tsawon wata shida bisa zargin karya ƙa’idojin majalisa.

Rahotanni sun nuna cewa wannan hukunci ya hana ta samun albashi, tsaro da kuma damar shiga zauren majalisar.

A ranar 4 ga Yuli, 2025 babbar kotun tarayya a Abuja ta bayyana dakatarwar a matsayin wuce gona da iri, inda ta umarci a dawo da ita bakin aiki.

Sai dai majalisar dattawa ta ce ba za ta aiwatar da hukuncin ba, tana mai jaddada cewa hukuncin bai ƙunshi umarnin dawo da ita kai tsaye ba, tare da cewa shari’ar na ci gaba a kotu.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: An kama gidan da ake kera bindigogi a Filato, an gano makamai

An kai kara majalisar dinkin duniya

Jagorar Womanifesto kuma shugabar cibiyar Women Advocate Research and Documentation Centre, Abiola Akiyode-Afolabi ta yi magana kan karar da suka kai.

Akiyode-Afolabi ta ce idan za a iya dakatar da Sanata mace saboda rahoton cin zarafi, to me zai hana a yi wa talakawan mata haka?

Kungiyoyin sun yi kira ga majalisar dinkin duniya da ta matsa wa gwamnatin Najeriya da majalisar dattawa wajen bin hukuncin kotu da kuma kare lafiyar Akpoti.

Zauren majalisar dinkin duniya da ke Amurka
Wakilan kasashe a zauren majalisar dinkin duniya. Hoto: United Nations
Source: Facebook

Bukatar sauye-sauye a majalisar dattawa

A cikin ƙarar, kungiyoyin sun kuma buƙaci a kafa tsarin kai ƙara mai zaman kansa a cikin majalisar domin ba wa ’yan majalisa damar samun adalci.

The Sun ta wallafa cewa sun kuma yi kira da a gudanar da bincike mai zaman kansa kan zargin cin zarafi da Akpoti ta gabatar.

Ƙungiyoyin da suka rattaba hannu kan ƙarar sun haɗa da Amnesty International, FIDA, Baobab, WIMBIZ, STER da sauransu.

Kara karanta wannan

Bayan barazanar Isra'ila, Saudi ta kulla yarjejeniyar tsaro da Pakistan mai nukiliya

NLC za ta yi zanga zanga kan Natasha

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar kwadago ta yi barazanar fara zanga zanga kan hana Sanata Natasha Akpoti komawa ofis.

Hakan na zuwa ne bayan majalisar dattawa ta ce har yanzu babu hurumin dawo da Natasaha bakin aiki bayan shafe wata 6 da dakatar da ita.

Rahotanni sun nuna cewa majalisar dattawa ta fadi haka ne bayan Natasha ta ce za ta koma bakin aiki bayan kammala dakarwar wata shida.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng