Gwamnan Kano Ya Yi Garambawul a Gwamnatinsa, Kwamishinoni 2 Za Su Mika Mulki Yau

Gwamnan Kano Ya Yi Garambawul a Gwamnatinsa, Kwamishinoni 2 Za Su Mika Mulki Yau

  • Gwamnan Kano, Abba Yusuf, ya amince da yin garambawul a gwamnatinsa domin daidaita aiki da samar da shugabanci na gari
  • Wannan karamin garambawul din ya shafi kwamishinoni biyu da kuma wani babban sakatare a ma'aikatar shari'a ta jihar
  • Abba Yusuf ya yi kira ga jami'an gwamnati da su ba kwamishinan da aka sauya wa wurin aiki hadin don gudanar da aikinsa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya amince da wani karamin garambawul a majalisar zartarwa ta jihar Kano.

Wannan garambawul din ya shafi wasu kwamishinoni, sannan an tura wasu manyan jami'an gwamnati zuwa inda za su yi aiki.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi karamin garambawul a majalisar zartarwar Kano.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf yana nuna muhimmancin lokaci a wani taro a Kano. Hoto: Sanusi Bature Dawakin-Tofa
Source: Facebook

An yi garambawul a gwamnatin Kano

Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin-Tofa ne ya sanar da hakan a shafinsa na Facebook a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Abba Gida-Gida zai rage bashin Ganduje, za a biya karin N5bn ga 'yan fansho a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar Sanusi Dawakin Tofa ta ce:

"Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da wani karamin sauye-sauye a majalisar zartarwa da kuma tura manyan jami'an gwamnati zuwa wurin da za su yi aiki.
"Wannan matakin, na daga cikin matakan da gwamnatin jihar ke ci gaba da dauka don karfafa shugabanci da samar da ingantattun ayyuka ga al’umma a tsakanin ma'aikatun gwamnati."

Kwamishinonin da garambawul ya shafa

A cewar sanarwar, Gwamna Abba ya ba da umarnin sauya wurin aikin babban lauyan gwamnati kuma kwamishinan shari'a, Barista Haruna Isa Dederi.

Sanarwar ta ce:

"Bisa umarnin gwamnan, Barista Haruna Isa Dederi zai bar mukamin kwamishinan shari'a zuwa kwamishinan ma'aikatar sufuri."

Hakazalika, an dage babban sakataren ma'aikatar shari'a, Barista Mustapha Nurudden Muhammad zuwa ma'aikatar muhalli, inda a can ma zai rike mukamin babban sakatare.

Garambawul din, ya kuma shafi kwamishinan ma'aikatar harkokin jin kai wanda yake aiki a matsayin mukaddashin kwamishinan ma'aikatar sufuri.

Kara karanta wannan

Sakkwato: Shugabannin makarantun sakandare 6 sun tsunduma kansu a matsala

Bayan sauya mukamin Barista Haruna Isa Dederi zuwa kwamishinan sufuri, yanzu an umarci kwamishinan harkokin jin kai, ya tsaya a matsayinsa kawai.

Gwamnan Kano ya ce ya sauyawa kwamishinoni wurin aiki saboda inganta ayyuka da shugabanci nagari
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf zaune a wajen wani taro a Kano. Hoto: @Kyusufabba
Source: Facebook

Dalilin gwamnan Kano na yin garambawul

Sanarwar Sanusi Dawakin Tofa ta ce:

"Gwamnan ya umarci dukkan jami'an da wannan garambawul ya shafa da su mika ragamar tafiyar da ofisoshinsu ga babban jami'i mafi girma a ma'aikatar.
"Ya bukaci a kammala mika mulki nan take, kuma kada hakan ya wuce ranar Talata, 23 ga watan Satumba, 2025, kafin karewar lokacin aiki."

Gwamna Abba ya jaddada aniyar gwamnatinsa na tabbatar da rikon amana, da ingantaccen aiki, da kuma samar da shugabanci mai ma'ana.

Ya bayyana cewa an yi garambawul din ne domin daidaita ayyuka da tabbatar da cewa gwamnati ta cika alkawuran da ta daukarwa mutanen Kano.

Gwamnan ya kuma yi kira ga jami'an gwamnati da su ba da haɗin kai ga sabon kwamishinan da aka sauya wa wuri don gudanar da aikinsa yadda ya kamata.

Kwamishinan Kano ya yi murabus

A wani labarin, mun ruwaito cewa, kwamishinan sufuri na Kano, Ibrahim Namadi, ya miƙa takardar ajiye aiki daga mukaminsa ga gwamnatin jihar.

Kara karanta wannan

Bayan nasarar dalibanta a NECO, gwamnatin kano za ta dauki malamai 2, 600 aiki

Wannan na zuwa bayan an gudanar da bincike kan rawar da ya taka a belin wani dilan ƙwaya, Suleiman Danwawu da NDLEA ta gurfanar da shi a kotu.

Duk da haka ya yi murabus, amma Ibrahim Namadi ya kafe a kan cewa bai aikata laifin komai ba a kan zargin da aka yi masa wajen karbar belin Danwawu.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com