Abu Ya Dawo Sabo: An Shirya Share Hawayen Rarara kan Digirin Girmamawa Na Bogi

Abu Ya Dawo Sabo: An Shirya Share Hawayen Rarara kan Digirin Girmamawa Na Bogi

  • Ana ci gaba da muhawara kan batun digirin girmamawa na bogi da aka ba shahararren mawaki, Dauda kahutu Rarara
  • Sadaukin Bauchi, Abdurahman Sade, ya bayyana cewa mawakin ya cancanci karramawa daga kowace jami'a a duniya
  • Ya bayyana cewa zai yi kokarin ganin cewa Rarara ya samu karramawar da ta dace da shi domin ya cancanci hakan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Sadaukin Bauchi, Abdurahman Sade, ya bayyana shahararren mawaki, Dauda Kahutu Rarara, a matsayin gwarzo.

Abdurahman Sade ya bayyana Rarara a matsayin wanda ya cancanci digirin girmamawa daga kowace jami’a a duniya.

Sadaukin Bauchi zai yi kokari a karrama Rarara
Hoton mawaki, Dauda Kahutu Rarara Hoto: Rabiu Garba Gaya
Source: Facebook

Abdurahman Sade ya bayyana haka ne yayin wata tattaunawa da jaridar Daily Trust a ranar Litinin, 22 ga watan Satumban 2025.

Rarara zai samu karramawar da ta dace

Sadaukin na Bauchi ya yi tsokaci kan rikicin da ya biyo bayan batun digirin girmamawa da ake zargin jami'ar European-American ta ba Rarara, wanda daga bisani ta musanta.

Kara karanta wannan

Otedola ya goyi bayan Dangote a rikicinsa da 'yan kasuwar mai, a shawarci DAPPMAN

Abdurahman Sade wanda ya ce shi ne ya jawo hankalin jami’ar kan wannan matsala a baya, ya yi alkawarin ci gaba da kokari har sai Rarara ya samu sahihiyar karramawa daga jami’ar.

"A manta da wancan na bogi. Ni da kaina zan ci gaba da kokari har sai ya samu na gaskiya. Ni masoyin Rarara ne."
"Jawo Rarara aka yi cikin lamarin nan. Yana cikin aiki sosai har bai samu damar bincike ba. Gaskiya, wannan tayin na digiri ya zo ne ta hannun wani abokinsa, wanda mun tabbatar ba shi da niyyar yaudararsa."
"Watakila mutanen da suka kusanci abokin nasa kan karramawar ba su bayyana gaskiya ba. A zahiri karramawa ce ga abokinsa, amma abokin ya ce Rarara ya fi cancanta."
"Ya cancanta. Rarara ya cancanci karramawa ba daga wannan jami’ar kaɗai ba, ina ganin daga kowace jami’a a duniya. Gaskiya, gwarzo ne. Ya cimma abubuwa da dama.”

- Abdurahman Sade

Wace shawara aka ba Rarara?

Da aka tambaye shi darasin da za a koya daga wannan lamari, mai rikon sarautar ya bayyana cewa:

“Darasin da nake so ya koya shi ne ya yi taka-tsantsan da abubuwan intanet. Duk wanda ya kusance shi kan batun karramawa, ya tabbatar da sahihancinsa. Akwai cibiyoyin bogi masu yawa a duniya."

Kara karanta wannan

Kafa bataliya da wasu manyan alƙawura 4 da Tinubu ya yi wa Katsina kan ƴan bindiga

Sadaukin Bauchi zai yi kokari a karrama Rarara
Hoton Sadaukin Bauchi, Abdurahman Sade Hoto: Abdul Sade
Source: Facebook

Ba jami'ar bogi ba ce

Hakazalika Abdulrahman Sade ya musanta rahotannin da ke cewa jami'ar ta bogi ce.

“Ni na yi karatu a wannan jami’ar. Ta yaya za a ce ta bogi ce? Matsalar ba daga jami’ar ta fito ba. Matsalar daga mutanen da ke bayan lamarin ne. Na jawo hankalinsu kai tsaye."
"Na aika rahoto gare su, kuma na jawo hankalin jami’ar kan lamarin, suka tabbatar mini cewa wannan karramawar ta bogi ce, cewa wasu ne kawai suka yi amfani da sunan jami’ar."
"A wannan karon, ana yin kokari don tabbatar da cewa ya samu sahihin digirin girmamawa, domin kamar yadda na faɗa tun farko, ya cancanta. Jami’ar ta riga ta amince za ta ba shi."

- Abdurahman Sade

Rarara ya magantu kan karrama shi

A wani labarin kuma, kun ji cewa shahararren mawaki, Dauda Kahutu Rarara, ya yi magana kan karramawar da aka yi masa.

Rarara ya nuna matakur godiyarsa ga jami'ar tare da mutanen da suka samu halartar bikin karrawamar da aka yi masa.

Hakazalika, ya bayyana cewa bai biya ko sisin kwabo ba kagin jami'ar ta ba shi digirin girmamama na Dakta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng