Matsala Ta Girma: An Gano Gawarwakin Yan Sanda 8 bayan Sun Bace a Najeriya
- Jami'an tsaron da suka rasa rayukansu a harin jihar Benuwai sun karu bayan gano karin gawarwakin 'yan sanda takwas
- A ranar Juma'a da ta gabata ne dakarun tsaro suka yi arangama da wasu yan bindiga a iyakar kananan hukumomin Katsina-Ala da Ukum
- Shugaban karamar hukumar Katsina-Ala, Dr. Justine Shaku ya ce abin da ya faru ya yi muni kuma babu dadi, amma suna kan bincike
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Benue - An gano karin gawarwakin ‘yan sanda takwas da aka kashe a mummunan harin da aka kai wa jami’an tsaro a jihar Benuwai.
Harin ya auku ne a yankin Agu Centre, kan iyakar kananan hukumomi Katsina-Ala da Ukum a jihar Benuwai da ke Arewa ta Tsakiya.

Source: Twitter
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa mummunan lamarin ya faru ne a ranar Juma’a lokacin da rundunar jami’an tsaro ta yi arangama da ‘yan bindiga.
Jami'an tsaro sun yi arangama da yan bindiga
Bayan musayar wuta mai tsanani, an tabbatar da mutuwar jama'an tsaro uku yayin da wasu guda takwas suka bata.
Tawagar jami'an tsaron da ta fafata da yan bindigar ta kunshi jami’an Operation Zenda, tare da haɗin gwiwar Benue State Civil Protection Guard (BSCPG) da kuma Special Intervention Squad (SIS).
A baya dai, an ruwaito cewa jami’ai uku, ‘yan sanda biyu da jami'in BSCPG daya sun mutu a artabun, yayin da ‘yan sanda takwas suka bace.
An gano karin gawarwakin yan sanda 8
Sai dai a yau Litinin, shugaban ƙaramar hukumar Katsina-Ala, Dr. Justine Shaku, ya tabbatar wa manema labarai cewa an gano gawarwakin yan sanda takwas da suka ɓace.
"Wannan ya kai adadin jami’an da aka kashe zuwa 11 (’yan sanda 10 da ɗaya daga BSCPG),” in ji Shaku.
Ya ƙara da cewa kwamishinan ‘yan sandan jihar Benuwai, CP Ifeanyi Emenari, na nan kuma shi ne zai jagoranci duk wasu ayyuka da suka shafi tsaro.
Wane mataki hukumomi suka dauka?
“Har yanzu yanayin da lamarin ya faru yana da sarkakiya kuma ba daɗi, amma muna kan lamarin,” in ji shi.

Source: Facebook
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Udeme Edet, ya tabbatar da cewa an gano gawarwakin dakaru takwas da suka bata.
Haka zalika, a wata hira da aka yi da shi ta wayar tarho, kwamandan BSCPG, Kyaftin Ayuma Ajobi (Mai ritaya), ya ce ya rasa ɗaya daga cikin jami’ansa da kuma babura guda biyu a harin.
Yan bindiga sun farmaki caji ofis a Kwara
A wani labarin, kun ji cewa 'yan bindiga sun kai hari ofishin yan sanda a jihar Kwara, kuma sun kashe jami'i daya da ke bakin aiki.
Majiyoyi sun ce 'yan ta'addar sun yi kaca-kaca da ofishin ‘yan sandan, amma ba su samu makamai ba saboda jami'ai sun fita aiki da bindigoginsu.
Jami’an tsaro na haɗin gwiwa, da suka haɗa da sojoji, ‘yan sanda, 'yan banga da mafarauta sun hanzarta kai dauki, inda suka kori maharan tare da dawo da zaman lafiya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

