Gwamna Fubara Ya Fadi Abin da Tinubu Ya Gaya Masa bayan Sun Sa Labule
- Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya sanya labule da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a Aso Rock
- Ganawar Gwamna Fubara da Mai girma Bola Tinubu na zuwa ne bayan janye dokar ta-bacin da aka sanya a jihar Rivers
- Gwamna Fubara ya bayyana yadda ganawar ta kasance da kuma shawarwarin da Shugaba Tinubu ya ba shi
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Rivers - Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya yi magana kan ziyarar da ya kai ga Shugaba Bola Tinubu.
Gwamna Fubara ya kuma bayyana cewa ya sasanta da magabacinsa, Nyesom Wike.

Source: Facebook
Gwamna Fubara ya gana da Bola Tinubu
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa Gwamna Fubara ya bayyana hakan ne bayan wata ganawar sirri da Shugaba Bola Tinubu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Fubara dai ya gana da shugaban kasan ne a fadarsa da ke Aso Rock Villa.
Jaridar Daily Trust ta ce da yake amsa tambayoyin manema labarai bayan ganawar, Gwamna Fubara ya bayyana dalilinsa na sanya labule da Shugaba Tinubu.
Dalilin Fubara na ziyartar Shugaba Tinubu
Gwamna Fubara ya bayyana cewa ya je fadar shugaban kasan ne domin sanar da Mai girma Tinubu cewa ya koma bakin aiki bayan dage dakatarwar da aka yi masa ta watanni shida.
Ya bayyana ziyarar a matsayin “tattaunawa tsakanin uba da ɗa,” inda ya ce ya kuma nemi shawarwarin shugaban kasan don gujewa maimaituwar rikicin siyasa a jihar.
"Kun sani cewa an ɗage dakatarwar da misalin ƙarfe 12:00 na daren 17 ga wata kuma na koma aiki a ranar 19 ga wata."
"Abin da ya dace shi ne na ga shugaban kasa na shaida masa cewa na dawo, kuma na fara gudanar da aikina a matsayin gwamnan jihar Rivers."
"Ba komai bane, tattaunawa ce ta uba da ɗa, na gode masa, sannan na nemi shawararsa domin kada mu sake tsintar kanmu cikin wani rikici."
- Gwamna Siminalayi Fubara

Source: Twitter
Me Tinubu ya gayawa Gwamna Fubara?
Da aka tambaye shi kan abin da shugaban kasa ya gaya masa, Gwamna Fubara ya bayyana cewa:
“Ya ba ni shawarwari kan abin da ya kamata na yi da kuma yadda zan tafi a kan hanya madaidaiciya.”
A lokacin da aka tambaye shi ko gaskiya ne an samu zaman lafiya a jihar Rivers, Fubara ya amsa da cewa:
"Ni a bangane na, mun yi sulhu. Fubara na aiki tare da maigidansa."
Ziyarar Fubara ta biyo bayan ganawar da Shugaba Tinubu ya yi da wasu manyan jami’an gwamnati da shugabanni, ciki har da shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya kuma Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq.
Gwamna Fubara ya godewa Shugaba Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya mika sakon godiyarsa ga shugaban kaaa, Bola Ahmed Tinubu da ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike.
Gwamna Fubara ya nuna godiyarsa ga mutanen biyu ne bisa rawar da suka taka wajen dawo da zaman lafiya a jihar Rivers.
Hakazalika, Gwamna Fubara ya godewa al’ummar jihar Rivers baki ɗaya saboda jajircewarsu da goyon bayan da suka nuna masa a lokacin da aka dakatar da shi daga kan mukaminsa.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

