Gwamna Fubara Ya Ziyarci Shugaba Tinubu Kwanaki bayan Maida Shi kan Kujera

Gwamna Fubara Ya Ziyarci Shugaba Tinubu Kwanaki bayan Maida Shi kan Kujera

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya samu bakuncin gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara a birnin tarayya Abuja
  • Gwamna Fubara ya ziyarci shugaban kasan ne shi kadai da yammacin ranar Litinin, 22 ga watan Satumban 2025
  • Ziyarar Gwamna Fubara na zuwa ne 'yan kwanaki bayan da Shugaba Tinubu ya janye dokar ta-bacin da ya sanya a jihar Rivers

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya ziyarci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.

Gwamna Fubara ya isa fadar shugaban kasan ne da ke Abuja domin ziyartar Shugaba Bola Tinubu.

Gwamna Fubara ya kai ziyara ga Shugaba Tinubu
Hoton Gwamna Siminalayi Fubara tare da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: @DOlusegun
Source: Facebook

Gwamna Fubara ya ziyarci Tinubu

Tashar Channels tv ta rahoto cewa Gwamna Fubara ya isa fadar shugaban kasan ne shi kadai da misalin karfe 6:20 na yammacin ranar Litinin, 22 ga watan Satumban 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Fubara ya nufi ofishin shugaban kasan ne kai tsaye bayan ya isa fadar Aso Rock da ke Aso Villa, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar da labarin.

Kara karanta wannan

'Yan APC sun ankarar da Shugaba Tinubu kan gwamnonin da zai yi hattara da su

Wannan shi ne karo na farko da Gwamna Fubara ya kai ziyara a fadar Aso Rock Villa tun bayan dawo da shi a matsayin gwamnan jihar Rivers.

An dawo da Gwamna Fubara kan mukaminsa ne bayan an dakatar da shi na watanni shida sakamakon dokar-ta-baci da Shugaba Tinubu ya sanya a jihar.

Dkatar da Gwamna Simi Fubara

Idan ba a manta ba dai, Shugaba Tinubu ya dakatar da Gwamna Fubara, mataimakiyarsa da kuma mambobin majalisar dokokin jihar a ranar 18 ga watan Maris, 2025.

Shugaba Tinubu ya dakatar da su ne sakamakon rikicin siyasa da ya mamaye jihar.

Sai dai a ranar 17 ga watan Satumba, 2025, Shugaba Tinubu ya sanar da janye dokar-ta-bacin.

Ya bayyana cewa matakin ya zama wajibi ne domin dawo da zaman lafiya da daidaito a jihar, wadda ke da matuƙar muhimmanci ga tattalin arzikin kasar nan saboda arzikin man fetur.

A wani jawabi da ya yi ga jama’ar jihar, Gwamna Fubara ya bayyana godiya marar iyaka ga Shugaba Tinubu bisa shiga tsakanin da ya yi a cikin rikicin siyasar Rivers.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya samu gagarumin tagomashi yayin da ake tunkarar zaben 2027

Gwamna Fubara ya ziyarci Mai girma Tinubu
Hoton gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara Hoto: @SimFubaraKSC
Source: Facebook

Meyasa Fubara ya ziyarci Shugaba Tinubu?

Sai dai, ba a bayyana hakikanin dalilin ziyarar da Gwamna Fubara ya kai wa Shugaba Tinubu ba har zuwa lokacin kammala hada wannan rahoton.

Ana hasashen ziyarar ba za ta rasa alaka da dawo da shi kan kujerar gwamna da Shugaba Tinubu ya yi ba.

Karanta wasu labaran kan Gwamna Fubara

Jam'iyyar PDP ta roki Gwamna Fubara

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar PDP reshen jihar Legas ta mika kokon bararta ga Gwamna Siminalayi Fubara.

Jam'iyyar PDP ta bukaci Gwamna Fubara da ka da ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Hakeem Olalemi wanda shi ne mataimakin jam'iyyar PDP na Legas ta Tsakiya, ya shawarci Fubara da kada ya bari tsoron siyasa ya hana shi aiwatar da shugabanci mai nagarta.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng