Gwamnatin Gombe Ta Shirya Magance Matsalar Rashin Sanya Yara a Makaranta
- Gwamnatin jihar Gombe ta ci burin sanya yara 400,000 a makarantar firamare a zangon karatu na shekarar 2025/2026
- Shugaban hukumar SUBEB na jihar ya bayyana cewa iyayen da ba sa tura yaransu makaranta za su fuskanci hukunci
- Babaji Babadidi ya bayyana cewa akwai dokar da ta yi tanadin hukunta iyayen da ba sa bari 'ya'yansu su shiga makaranta
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Gombe - Gwamnatin jihar Gombe ta ja kunnen iyayen yara kan batun tura 'ya'yansu zuwa makaranta.
Gwamnatin ta bayyana cewa za ta gurfanar da iyaye da masu kula da yara a gaban kotu idan suka kasa tura ‘ya’yansu makaranta.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta kawo rahoto cewa shugaban hukumar SUBEB ta jihar Gombe, Babaji Babadidi, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin, 22 ga watan Satumban 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Za a hukunta wasu iyayen yara a Gombe

Kara karanta wannan
Fitaccen Jarumin Fim ya sa jam'iyyu a ma'auni, ya gano wacce za ta kayar da Tinubu a 2027
Ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da aikin daukar dalibai na zangon karatun shekarar 2025/2026 a Amada, karamar hukumar Akko ta jihar.
Shugaban na SUBEB ya ce iyayen da suka sabawa dokar za su iya fuskantar hukuncin zaman gidan yari na watanni biyu a karkashin sashe na 19(2) na dokar SUBEB ta 2021.
Babaji Babadidi ya ce wannan mataki wajibi ne domin tabbatar da cewa kowane yaro ya samu ingantaccen ilmin zamani.
"Dole ne iyaye su tabbatar 'ya'yansu ko wadanda ke karkashinsu sun halarci tare da kammala makarantar firamare, karamar sakandare da babbar sakandare."
- Babaji Babadidi
Ya ƙara da cewa duk iyayen da suka karya sashe na 19(2) na dokar sun aikata laifi, kuma idan aka same su da laifi za a ci tara ko kuma a ɗaure su wata ɗaya a gidan kurkuku.
"Idan aka sake samun iyaye da laifi karo na biyu, hukuncin zai kasance tara mai tsanani ko kuma zaman kurkuku na tsawon watanni biyu."
- Babaji Babadidi
Babaji Babadidi ya ce kafin wannan yakin na shigar da yara makaranta, gwamnati ta yi amfani da hanyar rarrashi wajen samar da ilmi kyauta.
"Sai dai idan muka kasa cimma burin shigar da ɗalibai 400,000 makarantar firamare a wannan zangon, za mu koma amfani da doka wajen tilastawa iyaye.”
- Babaji Babadidi

Source: Facebook
Akwai yara marasa zuwa makaranta a Gombe
A nata jawabin, kwamishiniyar ilmi, Farfesa Aishatu Maigari, ta ce jihar na da yara fiye da 700,000 da ba su zuwa makaranta.
A cewarta, yankin Arewa maso Gabas yana da kaso 15% na yara miliyan 18.2 da ba su zuwa makaranta a Najeriya.
"Ba za mu zauna mu zura idanu ba alhalin yaranmu na zaman gida ba tare da zuwa makaranta ba."
"Za mu tabbatar kowanne yaro ya shiga makaranta. Kowanne yaro zai samu ingantaccen ilmi, kuma ya koyi sana’a, wacce za ta sa ba dole sai ya yi aikin gwamnati ba."
- Farfesa Aishatu Maigari
Bill Gates ya yabawa gwamnan Gombe
A wani labarin kuma, kun ji cewa babban attajiri a duniya, Bill Gates, ya fito ya yabawa gwamnatin jihar Gombe.
Bill Gates ya yabawa Gwamna Inuwa Yahaya kan manyan gyare-gyaren da ya aiwatar a bangaren lafiya.
Hamshakin attajirin Bill Gates ya ce yana alfahari da yadda gwamnatin jihar ke magance matsaloli domin samun sakamako mai kyau.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

