Majalisa Wakilai Ta Bude Wa Bola Tinubu Kofar Rumtumo Wa Najeriya Bashin Kudi
- Majalisar Wakilan Najeriya ta bayyana cewa ba a fahimci bayanin da ta yi kwanakin baya kan tsare-tsaron karbo bashi a Najeriya ba
- Kakakin Majalisar, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya ce suna goyon bayan tsarin Gwamnatin Bola Tinubu na ciyo bashi
- Ya bayyana cewa bashin da ake karbowa bai wuce ka'ida ba kuma ana amfani da shi wajen bunkasa tattalin arziki da yakar talauci
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ya jaddada goyon Majalisa ga tsare-tsaren karbo rance na Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Tajudeen ya ce Majalisar Wakilai na tare da tsarin Tinubu, yana mai bayyana karbo bashin da wata dabara ta bunkasa tattalin arziki da kawar da talauci.

Source: Twitter
Daily Trust ta rahoto cewa Tajudeen ya fadi hakan ne a wurin taron shekara-shekara na kungiyar African Network of Parliamentary Budget Offices (AN-PBO) karo na 8 wanda ya gudana a Abuja.
Matsayar Majalisar Wakilai kan ciyo bashi
Ya karyata rahotannin da ke cewa Majalisar ta ki amincewa da tsarin ciyo bashin Tinubu, yana mai kiran irin waɗannan rahotannin da “na yaudara da karya.”
"Mutane sun fassara jawabin da Shugaban Masu Rinjaye ya yi a taron Majalisun Afirka ta Yamma (WAPC) ba daidai ba, aka yi ta yada labarin cewa Majalisar Wakilai ba ta goyon bayan ciyo bashin Gwamnatin Tinubu."
"Wannan ba gaskiya ba ne, yaudara ce kawai domin Majalisar Wakilai ta 10 ta sha nanata matsayarta cewa duba da bukatuwar da ake da ita, karbo bashi na da matukar muhimmanci.
"Duba da yadda zamani ya sauya, dole ne Najeriya ta ciyo bashi domin gina manyan ababen more rayuwa, farfaɗo da tattalin arziki, da kuma kare masu rauni.
"Abu mafi muhimmanci shi ne, Shugaban Kasa ya tabbatar mana cewa duk wani rance zai kasance mai manufa tare da bin ingantattun ƙa’idodin duniya."
- Rt Ho. Tajudeen Abbas.
Kakakin Majalisa ya yiwa 'yan Najeriya bayani
Ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa rancen da Shugaba Tinubu ke karbo wa bai wuce ka'ida ba kuma ana amfani da kudin wajen gina ababen da za su taimaki jama'a.
Tajudeen ya ce Ofishin Kasafin Kuɗi da Bincike na Majalisar Dokoki (NABRO) da aka kafa zai samar da bincike mai zaman kansa kan rance, ɗorewar basussuka da kuma manufofin kuɗi, cewar rahoton Channels tv.

Source: Twitter
Kakakin Majalisar Wakilai ya kara da cewa duk da karbo bashi na da muhimmanci, rufe hanyar ɓarna, rashawa da sulalewar kudi ba bisa ka’ida ba ma ya zama dole.
A cewarsa, Najeriya na asarar kusan Dala biliyan 18 a kowace shekara sakamakon laifuffukan kuɗi, wanda ya kai kusan 3.8% na tattalin arzikin ƙasar.
Yan Majalisar Wakilai na shirin tada rigima
A wani rahoton, kun ji cewa wasu fustattun yan Majalisa na shirin tayar da rikici a Majalisar Wakilai da zarar sun dawo hutun shekara a watan Satumba, 2025.
Rahotanni sun nuna cewa tawagar 'yan Majalisar sun gudanar da taruka, kuma auna shirin tunkarar Tajudeem Abbas kan abin da suka kira wariyar da ake nuna masu.
A cewarsu, saboda tsantsar biyayyar da suke yiwa shugabancin majalisa, ana daukar ma'aikata da aiwatar da ayyukan mazabu ba tare da sanya su a ciki ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


