'Yan Bindiga Sun Sace Basarake tare da Wasu Mata a Plateau

'Yan Bindiga Sun Sace Basarake tare da Wasu Mata a Plateau

  • 'Yan bindiga sun sake kai hari a karamar hukumar Kanam ta jihar Plateau cikin tsakar dare lokacin da mutane ke barci
  • Ana zargin tantiran sun yi awon gaba da wani basarake bayan da su ka rika harbi kan mai uwa da wabi
  • Harin na zuwa ne bayan an kai irinsa wanda ya yi sanadiyyar hallaka Dagacin wani kauye a cikin karamar hukumar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Plateau - 'Yan bindiga dauke da makamai sun yi awon gaba da Hakimin Birbyang, Alhaji Zubairu Garba, a jihar Plateau.

Miyagun 'yan bindigan sun sace basaraken ne tare da wasu mata guda biyu a karamar hukumar Kanam ta jihar Plateau.

'Yan bindiga sun kai hari a Plateau
Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang Hoto: Caleb Mutfwang
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta kawo rahoto cewa an yi garkuwa da mutanen ne a daren ranar Lahadi, 21 ga watan Satumban 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun sace Hakimi

Kara karanta wannan

Ana sulhu da 'yan ta'adda a Katsina, 'yan bindiga sun sace hakimi da wasu mata 2 a Filato

'Yan bindigan sun farmaki kauyen ne suna harbi a iska kafin su sace matar Hakimin, wacce daga bisani ta tsere daga hannun masu garkuwa da mutanen.

Wannan lamari ya faru ne mako guda bayan da aka sace tare da kashe, Dagacin Shuwaka da ke cikin gundumar Kyaram a karamar hukumar Kanam ta jihar Plateau.

Shugaban kungiyar ci gaban Kanam (KADA), Shehu Kanam, da sakatarenta, Barista Garba Aliyu, sun tabbatar da aukuwar lamarin.

Sun tabbatar da aukuwar lamarin ne a cikin sanarwa da su ka rabawa manema labarai a birnin Jos, babban birnin jihar Plateau.

Shugabannin sun bayyana cewa masu garkuwa da mutanen, sun kai farmaki a kauyen ne kusan karfe 1:00 na dare, inda su ka yi awon gaba da basaraken zuwa wani wurin da ba a sani ba.

An yi kira ga hukumomi

Ƙungiyar KADA ta yi Allah-wadai da mummunan lamarin, tare da yin kira ga hukumomin tsaro da su kubutar da waɗanda aka sace sannan su dawo da zaman lafiya a yankin.

Hakazalika, kungiyar ta kuma zargi 'yan siyasa na yankin da gazawa wajen ɗaukar matakan da suka dace don shawo kan hare-haren da ke kara ta’azzara a ƙaramar hukumar.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi wa jami'an tsaro kwanton bauna, an samu asarar rayuka

Sun kuma yi kira ga gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang, tare da hukumomin tsaro da su ɗauki matakai don magance barazanar tsaro a yankin.

Rahotanni sun nuna cewa garkuwa da mutane da kuma ta’addancin ‘yan bindiga sun zama ruwan dare a yankin, inda ake yawan sace mutane domin neman kuɗin fansa, yayin da wasu kuma da kwanansu ya kare ake kashe su.

'Yan bindga sun kai hari a Plateau
Taswirar jihar Plateau, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Ba a ji ta bakin 'yan sanda ba

A halin yanzu, ba a samu jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Plateau, DSP Alabo Alfred, ba.

Kakakin 'yan sansan bai amsa tambayar da aka yi masa ba kan lamarin har zuwa lokacin kammala hada wannan rahoton.

'Yan bindiga sun farmaki jami'an tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun kai harin kwanton bauna kan jami'an tsaro a jihar Benue.

'Yan bindigan sun farmakoi jami'an tsaron ne lokacin da su ka fita aikin sintiri a karamar hukumar Katsina-Ala.

Harin ya jawo an nemi jami'ai sama da 10 an rasa yayin da aka gano wasu gawarwaki guda uku.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng