Ana Sulhu da 'Yan Ta'adda a Katsina, 'Yan Bindiga Sun Sace Hakimi da Wasu Mata 2 a Filato

Ana Sulhu da 'Yan Ta'adda a Katsina, 'Yan Bindiga Sun Sace Hakimi da Wasu Mata 2 a Filato

  • Wasu 'yan bindiga sun sace hakimin Birbyang, Alhaji Zubairu Usman Garba da wasu mata biyu a Kanam, Jihar Filato
  • Rahotanni sun bayyana cewa 'yan bindigan dauke da miyagun makamai sun shiga garin suna harbi babu kakkautawa da daddare
  • Al’umma da kungiyar ci gaban Kanam sun ce yanzu lamarin tsaron a yankin ya damalmale, inda su ka bukaci gwamnati da jami’an tsaro su dauki mataki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Plateau – Wasu masu garkuwa da mutane sun bi dare inda su ka kai farmaki karamar hukumar Kanam da ke jihar Filato.

'Yan bindigan sun sace hakimin gundumar Birbyang, Alhaji Zubairu Usman Garba, tare da mata biyu a ranar Lahadi da daddare.

An sace mutum uku a Filato
Hoton Gwamnan jihar Filato, Caleb Muftwang Hoto: Caleb Muftwang
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa rahotanni sun bayyana cewa maharan sun shiga kauyen ne suna harbi babu kakkautawa, sannan suka yi awon gaba da mutanen da suka sace.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace basarake tare da wasu mata a Plateau

'Yan bindiga sun sace hakimi a Filato

Independent Newspaper ta ruwaito cewa daga cikin wadanda aka sace har da matar hakimin, wadda daga baya ta samu damar tserewa daga hannun masu garkuwa da mutane.

Wannan lamari ya faru ne mako guda bayan sace da kashe shugaban unguwar Shuwaka da ke cikin gundumar Kyaram, a cikin karamar hukumar ta Kanam.

Lamarin ya fara daga wa jama'a hankali, inda Sakataren Kungiyar Ci gaban Kanam (KADA), Shehu Kanam ya ce suna cikin tashin hankali.

Da ya ke tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a garin Jos, ya ce maharan sun shigo kauyen da ƙarfe 1.00 na dare.

Jama'a sun shiga damuwa kan harin Filato

Shehu Kanam ya bayyana damuwarsa kan yawaitar hare-hare da garkuwa da mutane a yankin babu dare babu rana.

Ya yi kira ga jami’an tsaro su tashi tsaye domin ceto mutanen da aka sace tare da dawo da zaman lafiya a yankin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi awon gaba da hadimin gwamnan Nasarawa

Jama'a sun shiga damuwa kan hari a Filato
Taswirar jihar Filato, inda jama'a ke zaman dardar Hoto: Legit.ng
Source: Original

A wata sanarwa da shi da Shugaban kungiyar, Barrister Garba Aliyu suka rattaba hannu a kai, sun zargi ’yan siyasa daga yankin da rashin daukar matakan magance hare-haren.

Sun kuma roki Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, da sauran hukumomin tsaro da su maida hankali wajen shawo kan barazanar tsaro da ke barazana ga rayukan al’ummar yankin.

Rahotanni a baya bayan nan sun ce an samu karuwar hare-haren ’yan bindiga a yankin, inda wasu ke biyan kudin fansa, yayin da wasu ke rasa rayukansu.

An gano gidan kera makamai a Filato

A baya, mun wallafa cewa sojoji daga rundunar Najeriya sun kai samame a masana’antar haramtattun makamai a unguwar Heipang, karamar hukumar Barkin Ladi, jihar Filato.

Wannan samame ya biyo bayan bayanan leƙen asiri da suka nuna yadda wata ƙungiya ke kera bindigogi a wannan wuri domin sayar wa ga bata-garin mahara a cikin al'umma.

A yayin samamen, an cafke wani mai ƙera makamai, yayin da wasu daga cikin mutanen da suke aikin suka tsere kafin hukumar ta iso, amma duk da haka, an kama makamai da dama.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng