Gwamnatin Kano Ta Hango Matsala bayan Bullar Zazzabi Mai Sa Zubar Jini a Najeriya
- Hukumar Kula da Cututtuta ta Kano (KNCDC) ta gargadi mutane da su dauki matakan gujewa kamuwa da zazzabi mai sa zubar da jini
- Wannan gargadi na zuwa ne bayan hukumar NCDC ta kasa ta tabbatar da cewa akwai wasu mutane biyu da ake zargin sun kamu a Abuja
- KNCDC ta bukaci mazauna Kano su yi taka tsan-tsan tare da bin matakan tsafta domin kaucewa kamuwa da wannan zazzabi mai tsanani
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Gwamnatin Kano karkashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta gargadi mutanen jihar da su yi taka tsan-tsan da zazzafan zazzabi mai sa zubar da jini.
Gwamnatin Abba ta yi wannan gargadi ne biyo bayan rahoton da Hukumar Kula da Cututtuka ta Ƙasa (NCDC) ta fitar cewa akwai wasu mutane biyu da ake zargin sun kamu da zazzabin mai tsanani a Abuja.

Source: Facebook
Hukumar Kula da Cututtuka ta Jihar Kano (KNCDC) ta gargadi Kanawa da su kula don kaucewa kamuwa da zazzabin, a wata sanarwa da ta wallafa shafin Facebook.
Ana zargin zazzabin ya shigo Najeriya
Tun farko dai hukumar NCDC ta fitar da rahoto da ke nuna cewa an killace wasu mutane biyu da ake zargin su na ɗauke da cutar zazzaɓi mai tsanani da ke iya haddasa zubar da jini a Abuja.
Hakan ya sa Gwamnatin Kano ta hannun hukumar KNCDC ta yi gargadi, tana mai cewa yana da muhimmanci domin kare lafiyar jama’a.
A cewarta, duba da yadda Kano ke da yawan tara jama’a, kasuwanci da kuma yawan tafiye-tafiye zuwa sassan Najeriya, ya zama tilas ta yi wannan gargadi.
KNCDC ta bayyana cewa binciken farko ya tabbatar da cewa ba cutar Ebola ba ce ta kama mutanen da ake zargi a babban birnin tarayya Abuja.
Gwamnatin Kano ta gargadi jama'arta
Sai dai an ce har yanzu ana gudanar da ƙarin gwaje-gwaje domin gano ko cutar Lassa ko ta Dengue ce ta haddasa alamomin da aka gani.
“Zazzaɓin mai tsanani da ke sa mutum zubar da jini, wanda ake kira Viral Hemorrhagic Fevers, na daga cikin manyan cututtuka masu haɗari.
"Alamominsa na iya haɗawa da zazzabi, amai, gudawa, ko kuma zubar jini daga jiki,” in ji hukumar KNCDC.
Hukumar ta ƙara da cewa irin waɗannan cututtuka na iya yaɗuwa daga dabbobi zuwa mutane, ko kuma daga mutum zuwa mutum ta hanyar hulɗar jini ko zufa.
Matakan da KNCDC ta nemi mutane su bi
Bisa wannan dalilai, hukumar KNCDC ta shawarci jama’ar Kano da su bi matakai uku don kare lafiyarsu, wamda suka hada da;
- Wanke hannuwa akai-akai da sabulu ko sinadarin tsafta da aka amince da shi.
- Jama'a su kauce wa hulɗa da mu'amala da mutanen da suka kamu da kowane irin zazzabi ko zubar jini ba tare da sanin musabbabin hakan ba
- Sannan su kauce wa hulɗa da namun daji domin kariya daga kamuwa da cututtuka.

Kara karanta wannan
Abin kunya: An kama masu karkatar da kudin tallafin 'taki' da ake rabawa talakawa a Katsina

Source: Facebook
Haka kuma, hukumar ta bukaci jama’a da su tabbatar ana dafa nama sosai kafin ci, tare da garzayawa asibiti da wuri idan aka fuskanci duk wata alamar cutar.
Gwamnatin Kano ta canza sunan ma'aikata
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatun Kano ta sauya sunan Ma'aikatar Mata, Yara da Nakasassu zuwa Ma'aikatar Mata, Yara da Masu Bukata ta musamman.
An yi wannnan canjin suna ne domin cire kalmar da ake ganin ta kaskantar da masu bukata ta musamman a jihar Kano
Kwamishinar Harkokin Mata Hajiya Amina ta yaba Gwamma Abba Kabir, tana mai nuna irin yadda yake son tallafawa gajiyayyu da masi bukata ta a musamman.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

