APC, ADC da PDP Sun 'Ayyana' Wanda Suke Fata Tinubu Ya ba Shugaban INEC

APC, ADC da PDP Sun 'Ayyana' Wanda Suke Fata Tinubu Ya ba Shugaban INEC

  • Jam’iyyar APC ta fadi sifofin wanda ta ke shugaban kasa Bola Tinubu ya ayyana a matsayin shugaban INEC
  • PDP ta bukaci shugaban hukumar da za a nada ya zamo mai gaskiya da zai iya aiki ba tare da son zuciya ba
  • ADC ta yi gargadi da cewa rashin sahihin zabe zai iya barazana ga zaman lafiyar dimokuradiyyar Najeriya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Yayin da babban zaben shekarar 2027 ke kara matsowa, jam’iyyun siyasa da dama sun bayyana bukatunsu kan wanda zai maye gurbin Farfesa Mahmood Yakubu a INEC.

Yakubu da ya fara jagoranci tun 2015 kuma aka sake nada shi a 2020, zai kammala wa’adinsa a Nuwamba, lamarin da ya bude tattaunawa kan wanda zai karɓi ragamar hukumar.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Shugaban APC ya rikita 'yan adawa kan zaben 2027

Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu. Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

Punch ta wallafa cewa jam’iyyu irin su APC, PDP da ADC sun ce ya kamata sabon shugaban hukumar ya zama mai gaskiya, mai adalci, tare da jajircewa wajen kare dimokuradiyya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Irin shugaban INEC da APC ke so

Daraktan yada labarai na jam’iyyar APC, Bala Ibrahim, ya bayyana cewa manufar jam’iyyar ita ce lashe zabubbuka a cikin yanayi na gaskiya da adalci.

Ya ce APC na bukatar sabon shugaban INEC da zai tabbatar da daidaito tsakanin kowane dan takara da jam’iyyu.

A cewarsa:

“Bukatar mu ita ce a ba mu damar shiga zabe a fili, a kan ka’ida, ba tare da wani nuna bambanci ba.
Sabon shugaban INEC ya zama wanda zai gudanar da zabe cikin gaskiya da bin doka.”

PDP ta nemi shugaba mai gaskiya

A nasa bangaren, sakataren yada labarai na PDP, Debo Ologunagba, ya jaddada cewa dole shugaban hukumar ya kasance mai gaskiya da zai iya tsayuwa da kafarsa.

Kara karanta wannan

'Yan Najeriya sun fadi 'wanda' suke so Tinubu ya nada shugaban INEC

Ya ce:

“Abin da muke bukata shi ne shugaba mai gaskiya, wanda ba shi da aibu a halayyarsa, kuma wanda zai kare tsarin dimokuradiyya bisa tanadin kundin tsarin mulki.”

Ologunagba ya kara da cewa dole shugaban kasa da majalisar kasa su tabbatar da an tantance wanda za a nada, don tabbatar da kwararren mutum ne zai jagoranci hukumar.

INEC: ADC ta yi gargadi kan magudi

Jam’iyyar ADC ta yi nuni da cewa hukumar INEC ta jima tana fuskantar kalubale kan rashin amincewar jama’a.

Kakakin jam’iyyar, Bolaji Abdullahi, ya ce dole sabon shugaban hukumar ya shawo kan rashin amincewar jama’a ga INEC kafin zaben 2027.

Kakakin jam'iyyar ADC, Bolaji Abdullahi
Kakakin jam'iyyar ADC, Bolaji Abdullahi. Hoto: ADC Vanguard
Source: Facebook

Bolaji Abdulahi ya yi gargadin cewa idan aka nada shugaban da bai cancanta ba, hakan zai iya haifar da shakku a zukatan jama’a kan sahihancin zabe.

Ya ce hakan ka iya jefa kasar cikin rudani, inda ya yi misali da juyin juya halin Orange Revolution na kasar Ukraine.

Kara karanta wannan

2007: PDP ta bukaci Tinubu ya fara shirin mika mulki, ta kawo dalili

Ra'ayin jama'a kan nada shugaban INEC

A wani rahoton, kun ji cewa, hankalin 'yan Najeriya ya fara karkata kan wanda zai maye gurbin shugaban INEC a Najeriya.

Hakan na zuwa ne yayin da shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu ya kusa ajiye aiki saboda cikar wa'adinsa.

Legit Hausa ta hada rahoto na musamman kan ra'ayoyin jama'ar Najeriya game da wanda suke fata ya dawo sabon shugaban INEC.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng