Tsadar Rayuwa: NLC Ta Taso Gwamna a gaba, Tana So Ya Kara Albashi zuwa N256,960
- Ma’aikatan jihar Ondo sun nemi karin albashi daga N73,000 zuwa N256,950 saboda matsanancin hauhawar farashi
- Kungiyar NLC ta ce jihar Ondo tana da wadataccen kudi saboda man fetur, don haka bai kamata albashi ya gaza N256,950 ba
- 'Yan kwadagon sun shaida wa Gwamna Lucky Aiyedatiwa cewa ma’aikata sune ginshikin tafiyar da gwamnati da tattalin arziki
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Ondo - Ma’aikatan gwamnatin jihar Ondo sun bukaci karin mafi karancin albashi daga N73,000 da ake biya zuwa N256,950.
Bukatar karin albashin na kunshe ne a cikin wata wasika da ma'aikatan suka aika ga gwamnan jihar na Ondo, Lucky Aiyedatiwa.

Source: Facebook
NLC ta nemi karin albashi a Ondo
Kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) reshen jihar da sauran kungiyoyin kwadago ne suka sanya hannu a kan wasikar, inji rahoton Channels TV.

Kara karanta wannan
'Yan kasuwa Musulmi na fuskantar cin zarafi, ana ƙwace dukiyarsu da sunan sarkin Osun
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyoyin kwadagon sun ce bukatar karin albashin ta zama tilas saboda halin matsin rayuwa na da tattalin arziki da ake ciki.
A cewar su, albashin da ake biya yanzu ya gaza biyan bukatun ma'aikata na yau da kullum, musamman bayan cire tallafin man fetur.
Ma'aikatan sun nuna damuwa cewa cire tallafin man fetur ya haifar da hauhawar farashin kaya, sufuri, gidaje da kiwon lafiya.
Albashin da ma'aikata ke so a dawo biya
A cikin wasikar da shugaban NLC na jihar, Ademola Olapade, da sakataren kungiyar, Akin Sunday, suka sanyawa hannu, ma’aikata sun bukaci gwamnatin Aiyedatiwa ta gaggauta kafa kwamitin tattaunawa na karin albashi.
Sun bayyana cewa jihar Ondo tana da isasshen karfin tattalin arziki don biyan sabon albashi, musamman idan aka yi la’akari da cewa gwamnatin Imo ta riga ta amince da mafi karancin albashi na N104,000.
Jaridar The Cable ta rahoto NLC ta kara da cewa:
“Jihar Ondo ba karamar jiha ba ce, ita ce ke taka muhimmiyar rawa wajen samar da kudin shiga ta fannin mai. Bai kamata a bar ma’aikatanta da 'yan fansho suna rayuwa cikin wahala ba.
"A bisa wannan, NLC reshen Ondo da sauran kungiyoyin kwadago, suna gabatar da bukatar karin albashi ga ma'aikatan Ondo zuwa N256,950.
"Muna da tabbacin za a iya biyan wannan albashin na N256,950, wanda zai yi daidai da halin da tattalin arziki yake ciki, kuma zai rage radadin rayuwa ga ma'aikata."

Source: Twitter
Muhimmancin jin dadin ma’aikata a Ondo
Kungiyar ta jaddada cewa ma’aikata sune ginshikin tafiyar da gwamnati da tattalin arziki, yayin da 'yan fansho kuma sune wadanda suka yi hidima da amana a shekarun baya.
“Ya zama wajibi gwamnati ta tabbatar da sun yi rayuwa mai inganci da mutunci bayan ritaya,” inji kungiyar.
A karshe, NLC ta ce ba za ta daina matsa lamba ba har sai an tabbatar da cewa albashin ma’aikatan jihar Ondo ya dace da tsadar rayuwa a Najeriya.
NLC ta tunkari Tinubu kan N70,000
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kungiyar kwadago ta NLC ta bayyana cewa mafi karancin albashin N70,000 da ake biyan ma'aikata a Najeriya ya yi kadan.
Kungiyar NLC ta bukaci a sake duba mafi karancin albashi na kasa domin a kara yawansa, tana mai cewa N70,000 ba ta yi daidai da halin tattalin arziki a yanzu ba.
Hauhawar farashin kayayyaki da karuwar kuɗin abinci, sufuri, haya da wutar lantarki ya lalata darajar wannan albashi na N70,000, a cewar kungiyar NLC.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

