'Yan Bindiga Sun Yi Wa Jami'an Tsaro Kwanton Bauna a Benue, an Samu Asarar Rayuka

'Yan Bindiga Sun Yi Wa Jami'an Tsaro Kwanton Bauna a Benue, an Samu Asarar Rayuka

  • Daruruwan 'yan bindiga sun yi wa jami'an tsaro kwanton bauna a jihar Benue da ke yankin Arewa ta Tsakiya
  • Majiyoyi sun bayyana cewa an nemi wasu jami'ai an rasa sakamakon harin yayin da aka gano wasu gawarwarki
  • Rundunar 'yan sandan Najeriya ta tabbatar cewa ta cafke wasu daga cikin wadanda ake zargin akwai hannunsu a harin

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Benue - Akalla jami’an tsaro 11 ake fargabar 'yan bindiga sun hallaka a jihar Benue.

Lamarin ya auku ne bayan 'yan bindiga sun yi musu kwanton bauna a kusa da yankin Agu da ke gundumar Mbatula/Mberev, karamar hukumar Katsina-Ala.

'Yan bindiga sun farmaki jami'an tsaro a Benue
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun Hoto: @PoliceNG
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da daddare a ranar Juma’a, 19 ga watan Satumban 2025.

'Yan bindiga sun farmaki jami'an tsaro

Kara karanta wannan

Ana batun sulhu, dakarun sojoji sun dakile harin 'yan bindiga a Katsina

Shugaban karamar hukumar Katsina-Ala, Dr. Shaku Justine, ya tabbatar da aukuwar lamarin tawayar tarho a ranar Lahadi, 21 ga watan Satumban 2025.

Ya bayyana cewa jami’an tsaro 11 da aka fita aikin da su har yanzu ba a gansu ba, yayin da aka gano gawarwaki uku kacal zuwa yanzu.

Shaku Justine ya bayyana cewa an fara gano gawarwaki biyu a daren Juma’a, yayin da tawagar masu ceto ta ci gaba da bincike a dazuzzuka har tsawon Asabar, sannan a safiyar Lahadi aka sake gano guda ɗaya.

Sai dai mazauna yankin sun yi ikirarin cewa jami’an tsaro 16 ne aka rasa yayin artabu da ɗaruruwan ‘yan bindiga.

"Eh, an kai hari kan wasu jami’an tsaro a ranar Juma’a yayin da su ke aikin sintiri. An gano gawarwaki biyu bayan karfe 11:00 na dare."
"Ba mu tabbatar ko dukkan mutum 11 din sun mutu ba, amma an tura tawagar ceto zuwa yankin. Sai sun dawo ne za mu tabbatar da adadin."
"An kona motocin sintiri guda biyu da su ke ciki. Shaidu sun ce maharan sun fi 1000, domin sun zo da yawa."

Kara karanta wannan

'Yan fansho sun fusata, suna shirin fara zanga zanga tsirara a fadin Najeriya

"Har zuwa yanzu (ranar Lahadi da rana), tawagar ceton na cikin daji. An sake gano wata gawa guda ɗaya amma zamu samu cikakken rahoto idan sun dawo."

- Dr. Shaku Justine

'Yan bindiga sun kai hari kan jami'an tsaro a Benue
Taswirar jihar Benue, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Me 'yan sanda suka ce kan lamarin?

Jaridar TheCable ta ce rundunar 'yan sandan Najeriya (NPF) ta ce ta kama mutum shida da ake zargi da hannu a harin.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar, Benjamin Hundeyin, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Lahadi.

Kakakin ‘yan sandan ya ce mutanen aka kama suna tsare kuma suna bada bayanai masu amfani don gudanar da bincike.

'Yan bindiga sun sace hadimin gwamnan Nasarawa

A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a birnin Lafia, babban birnin jihar Nasarawa.

'Yan bindigan sun yi awon gaba da daya daga cikin masu taimakawa gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule.

Tsagerun sun sace Dr. Muhammed Egye Osolafia, wanda aka fi sani da Deedat, wanda yake shi ne mataimaki na musamman kan harkokin jin kai ga Gwamna Abdullahi Sule, a cikin gidansa.

Kara karanta wannan

Karfin hali: 'Yan bindiga sun gabatar da manyan bukatu 3 kan sulhu a Katsina

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng