Malamin Musulunci Ya Gamu da Hatsarin Mota a Maiduguri, an Gano Halin da Yake ciki

Malamin Musulunci Ya Gamu da Hatsarin Mota a Maiduguri, an Gano Halin da Yake ciki

  • Rahotanni sun tabbatar da cewa matashin malami, Isma’il Maiduguri daga jihar Borno, ya tsira daga mummunan hatsarin mota a hanyar Maiduguri
  • Isma’il ya bayyana cewa shi da abokinsa Abubakar Dumame sun tsira lafiya bayan hatsarin da ya afku a Ngamdu da ke jihar
  • Malamin ya gode wa Allah bisa wannan tsira da ya yi, inda ya bayyana farin cikinsa da cewa dukansu suna cikin koshin lafiya ba tare da raunuka ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Maiduguri, Borno - Rahoton da muka samu yanzu sun tabbatar da cewa daya daga cikin matasan malamai a Arewa ya gamu da hatsarin mota.

Malam Isma'il Maiduguri wanda dan asalin jihar Borno ne ya gamu da hatsarin a kan hanyar Maiduguri da ke jihar.

Malam Isma'il Maiduguri ya yi hatsarin mota
Alaranma Isma'il Maiduguri da hotunan hatsarin mota da ya yi. Hoto: Isma'il Maiduguri.
Source: Facebook

Shehi ya tsallake rijiya ta baya a Maiduguri

Kara karanta wannan

'Manyan dalilan da suka sanya aka girmama ni da digirin Dakta': Rarara

Matashin malamin shi da kansa ya tabbatar da haka a yau Lahadi 21 ga watan Satumbar shekarar 2025 a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Isma'il Maiduguri ya yi godiya ta musamman ga Ubangiji mahalicci bayan tsira daga hatsarin da ya afku a Ngamdu da ke jihar.

Ya bayyana farin cikinsa inda ya ce da shi da abokinsa, Abubakar Dumame suna raye babu abin da ya same su kuma suna cikin koshin lafiya.

Hatsarin mota: Alaranma ya yi godiya ga Ubagiji

A cikin rubutun da ya yi, Aramma Isma'il Maiduguri ya yi godiya ga Ubangiji bisa tseratar da su da ya yi yayin hatsarin.

Ya ce:

"Alhamdulillah Alhamdulillah Alhamdulillah!!!.
"Yanzu muka tsira daga hatsarin mota da ya afku a Ngamdu yayin da muke fitowa daga birnin Maiduguri a yau.
"Alhamdulillah, da ni da kuma Abubakar Dumame dukanmu muna raye kuma cikin koshin lafiya, mun gode Allah."
Alaranma Isma'il Maiduguri ya godewa Allah bayan hatsarin mota
Matashin malamin addini, Alaranma Isma'il Maiduguri. Hoto: Isma'il Maiduguri.
Source: Facebook

Isma'il Maiduguri: Martanin mutane kan hatsarin mota

Mutane da dama sun yi jimamin hatsarin da ya afku da matashin malamin inda suka yi ta masa fatan alheri da addu'o'i domin samun lafiya.

Kara karanta wannan

Obasanjo ya yi wa shugabanni nasiha mai ratsa zuciya kan mutuwar dimokuradiyya

Wasu ko godiya suke yi wa Ubangiji saboda tseratar da rayuwarsa da ya yi da abokin tafiyarsa ba tare da sun samu rauni ko rasa rai ba.

Muhammad Hussaini Shawa:

"Allah kiyaye gaba."

Abdurrahman Yunus

"Subhanallah.
"Allah ya kiyaye na gaba, Allah ya maida mafi alkhairi."

Suleiman Yusif Sulaiman:

"Alhamdulillah Masha Allah, Allah ya qara kare mana malam da kuma abokan arziki."

Abu-Ammar Yareema

"Ameen ya Hayyu ya Qayyum, Akaramakalla, Allah ya qara kare mana kai da tawagarka."

Isma'il Maiduguri ya yi tone-tone ga malamai

Mun ba ku labarin cewa Alaranma Ismail Maiduguri ya zargi wasu daga cikin malaman musulunci da kiristanci da biyewa ‘yan siyasa lokacin zabe.

Malamin Al-Kur’anin ya ce yawan cikan sahu a masallatai da coci ake amfani da su a wajen sayen bakin malamai musamman idan lokacin siyasa ya yi.

Gwani Ismail Maiduguri ya ce tun da an karbi kudin ‘yan siyasa, dole yanzu ba za a iya kokawa da irin mulkinsu ba komai zaluncin da suke yi bayan hawa karagar mulki.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.